Hotunan yadda sarki Muhammadu Sanusi II ya karɓi takardar kama aiki

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
A ranar Juma'a ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa sarki Muhammad Sanusi II takardar kama aiki.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
An mayar da Muhammad Sanusi II kan karaga ne bayan soke dokar masarautun jihar Kano ta 2029.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
Dakar masarautar Kano ta 2024 ta bayyana cewa tsarin masarautar Kano zai koma yadda yake kafin samar da dokara masarautun Kano ta 2019.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
Haka nan dokar masarautar Kanon ta 2024 ta soke duk wasu naɗe-naɗe ko muƙamai na sarauta da aka yi ƙarƙashin dokar 2019.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
Wannan ya sanya sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da sarakuna Bichi da Gaya da ƙaraye da Rano suka rasa rawunnansu.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
Hakimai da dama na masarautar Kano sun halarci bikin bai wa saraki Muhammdu Sanusi takardar kama aiki, duk da cewa wasu masu riƙe da sarautun gargajiya a jihar ta Kano sun ƙalubalanci sabuwar dokar a kotu.

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ce an soke dokar masarautun Kano ta 2019 domin dawo da martabar masarautar Kano.







