Hanyoyi bakwai da za a yaƙi talauci a Najeriya - Sarki Sanusi

Sarki Muhammadu sanusi II

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Najeriya ta daɗe tana fuskantar matsalolin talauci da hauhawar farashin kaya, da rashin tabbas a harkokin tattalin arziki, kodayake a baya-bayan nan an ɗan amu sauƙi.

Duk da kasancewarta ƙasa mai dimbin arziki, akwai miliyoyin 'yan ƙasar da ke rayuwa a cikin tsananin talauci, inda rashin aikin yi da rashin wadatacciyar wutar lantarki da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara dagula rayuwar al'umma.

A wani taron neman mafitar makomar tattalin arziƙin Najeriya zuwa shekarar 2030, wanda 'News Central' ta shirya, Sarkin Kano na 16 kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana wasu shawarwari kan yadda za a iya rage talauci a ƙasar.

Sarki Sanusi ya jaddada cewa babban mataki shi ne tabbatar da daidaito a ɓangaren tattalin arziki saboda cimma duk wata manufa ta ci gaban ƙasa.

Sarkin ya bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi domin kaucewa talauci a ƙasar kuma sun haɗa da:

Ilimantar da yara mata

Sarki Muhammadu Sanusi II

Asalin hoton, Getty Images

Sarki Sanusi ya jaddada muhimmancin ilimi musamman ga yara mata wajen yaƙar talauci.

Ya bayyana cewa ilimantar da mata na ƙara basirar iyali da rage talauci.

Muhammadu Sanusi II ya ce idan aka ilimantar da 'ya mace, an ilmantar da al'umma.

"Mata masu ilimi suna da damar samun aiki da gudanar da kasuwanci, da inganta rayuwar gida." in ji shi.

Tabbatar da daidaton tattalin arziƙi

Sarki Sanusi ya jaddada cewa babban mataki shi ne tabbatar da daidaito a ɓangaren tattalin arziki saboda cimma duk wata manufa ta ci gaban ƙasa.

''Babban mataki a yanzu shi ne rage hauhawar farashin k

Rashin daidaito da rashin tsari mai kyau a ɓangaren gwamnati da kasuwanci suna hana mutane zuba jari da gudanar da harkokin kasuwanci.

Ya ce idan babu daidaito a tattalin arziƙi ƙasar ko a fannin haraji ko na tsarin gwamnati, ba za a samu canji ba," in ji shi.

Ƙayyade farashin dala

Wani mutum na ƙirga takardun naira da kuma takardun dala a gefe

Asalin hoton, Getty Images

Sarki Sanusi ya yi nuni da cewa rashin tabbas a farashin dala na ɗaya daga cikin manyan matsalolin tattalin arzikin ƙasar domin yana shafar komai daga harkar kasuwanci, zuwa ilimi da rayuwar yau da kullum.

Ya ce Babban Bankin Najeriya (CBN) ya riga ya fara wannan matakai don tabbatar da wannan daidaito, amma har yanzu akwai aiki a gaba.

"Idan har aka ƙayyade farashin dala, hakan zai rage tashin farashin kaya, darajar naira za ta ƙaru kuma hakan zai ƙarfafa zuba jari daga cikin gida da waje." kamar yadda sarkin na Kano ya yi bayani.

Inganta kashe kuɗin gwamnati

Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa Najeriya ta samu ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin gwamnati, musamman wajen ƙara samun kuɗaɗen shiga da rage giɓin kasafin kuɗi.

Amma ya yi nuni da cewa ya kamata a duba ingancin kashe kuɗi, musamman wajen manyan ayyuka kamar hanyoyi da wutar lantarki da sauran ayyukan gwamnati.

Ƙara samar da wutar lantarki

Sarkin Kanon na 16 ya kuma ce bai kamata a mayar da hankali kawai wajen bayar da wutar lantarki a farashi mai rahusa ba, ya kamata a tabbatar da samun wutar lantarki mai inganci.

Ya ci gaba da cewa idan har masu ƙananan kasuwanci suka samu tsayayyiyar wutar lantarki ta awa 24, hakan zai sa su bunƙasa arziƙinsu sannan za su ƙaru a faɗin ƙasa

Jajircewa da haƙuri don samun ci gaba

Sarki Sanusi ya nuna cewa samun ci gaba na buƙatar haƙuri da jajircewa.

Ya bayyana cewa a lokacin da yake gwamnan CBN, manufarsa kan hauhawar farashin kaya ita ce tsakanin kashi 6 zuwa 9, amma yanzu hauhawar farashin kaya ta kai kashi 20.

Wannan yana nuna cewa akwai buƙatar sake duba tsarin kuɗi da manufofi don rage talauci in ji shi.

Tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi

A cewar Sarki Sanusi, tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi shi ne tushen ci gaban tattalin arziki da hanyar rage talauci a Najeriya.

Ya kuma jaddada cewa ilimi na buɗe ƙofofin samun aiki da ƙirƙirar sana'a da inganta rayuwar iyali da al'umma baki ɗaya.

Sarkin ya ce lura da yadda ake kashe kuɗin gwamnati shi ma hanya ce ta kauce wa talauci a ƙasar.