Arsenal na son Alvarez, Mece ce makomar Alexander-Arnold?

Asalin hoton, Getty Images
Ɗanwasan baya na Ingila Trent Alexander-Arnold ba a shaida masa ya bar Real Madrid ba, duk da rahotanni daga Spain da ke cewa sabon koci Alvaro Arbeloa ya buƙaci ɗanwasan mai shekara 27 ya nemi wata ƙungiya. (Mail)
Arsenal na diba yiyuwar ɗauko ɗanwasan gaba na Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez. (ESPN)
Bayern Munich za ta fuskanci hamayya daga Liverpool kan ɗanwasan gaba na Ivory Coast da RB Leipzig Yan Diomande, mai shekara 19. (Bild - in German)
AC Milan na son ɗanwasan baya na Liverpool da Ingila Joe Gomez, mai shekara 28. (Calciomercato - in Italian)
West Ham ta yi watsi da tayin fam miliyan 32.9 daga Flamengo kan ɗanwasan tsakiyarta na Brazil Lucas Paqueta. (Athletic - subscription required)
Ɗanwasan tsakiya na Crystal Palace da Ingila Adam Wharton, mai shekara 21 da ɗanwasan tsakiya na Brighton da Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 22, na kan gaba da Manchester United ke farauta maimakon ɗanwasan Nottingham Forest Elliot Anderson, mai shekara 23, wanda ake tunanin zai koma Manchester City. (The I - subscription required)
Liverpool na diba yiyuwar dawo da ɗanwasan Girka Kostas Tsimikas, mai shekara 29, wanda ta ba Roma aro. (Talksport)
Chelsea ta tuntuɓi Juventus kan aron ɗanwasan tsakiya na Brazil Douglas Luiz, wanda ke taka leda Nottingham Forest. (Fabrizio Romano)
Barcelona na shirin toshe wa masu buƙatar ɗanwasan tsakiyarta Fermin Lopez inda take shirin ba shi sabuwar kwantaragi. (Sport - in Spanish)











