Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Rufewa

    Masu bin shafin namu, nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonin.

    Sai kum agobe idan Allah ya kai mu.

    Amma kafin nan Abdullahi Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Trump ya yi barazanar ƙaƙaba wa Kanada harajin kashi 100 saboda China

    Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar sanya ƙarin harajin kashi 100 kan Kanada idan ta kuskura ta ƙulla yarjejeniyar kasuwanci da China.

    Ya yi gargaɗin cewar China za ta haɗiye Kanada, ta hanyar amfani da ƙasar wajen sayar da kayyakin da ta yi niyyar shigarwa Amurka.

    Dangantaka tsakanin Amurka da Kanada ta yi tsami tun bayan da Mista Trump ya koma mulki a karo na biyu, amma rashin jituwar ta tsananta a baya-bayan nan.

    Mista Trump ya janye gayyatar da ya yi wa Mista Carney na shiga ''Kwamitin zaman lafiyar Gaza'' bayan da firaministan na Kanada ya soki wasu manufofin gwamnatin Trump.

  3. 'Ƴan ɗariƙa na fuskantar matsin lambar sauya aƙida a Afghanistan'

    Shugaban Taliban

    Asalin hoton, AFP

    Wasu Musulmai tsiraru mabiya wata ɗariƙa a Afghanistan sun ce suna fuskantar matsin lamba daga jami'an Taliban kan sauya aƙidarsu.

    Musulman mabiyar ɗariƙar Ismaili - da Aga Khan ya assasa - sun ce jami'an Taliban na yi musu tayin ba su kariya da yi musu ihsani mai yawa idan suka koma tafarkin Sunni.

    Sun kuma ce Taliban na amfani da ƙarfi wajen tilasta musu komawa tafarkin na Sunni.

    A ranar Talata wasu ƴanbindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe wasu mutum biyu mabiyar ɗariƙar da ke gadin shaguna, tare da ji musu munanan raunuka a Faizabad da ke kudancin lardin Badakhshan, inda mafiyar mabiya ɗarikar ta Ismaili ke zaune.

    Haka kuma jami'an na Taliban sun yi barazanar rufe wuraren ibada na mabiya ɗariƙar.

  4. Ƴan majalisar dokokin jihar Kano 22 sun fice daga NNPP

    Kakakin majalisar Kano da Gwamna

    Asalin hoton, Abba Kabir Yusuf/Facebook

    Ƴanmajalisar dokokin jihar Kano 22 daga cikin mambobin majalisar 40 sun bi sahun gwamnan jihar wajen ficewa daga jam'iyyar NNPP.

    A ranar Juma'a ne Gwamna Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP a hukumance.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran majalisar, Kamaluddeen Sani Shawai ya fitar ya ce ƴanmajaliar sun fice ne domin nuna goyon bayansu ga gwamnan.

    Cikin ƴanmajalisar da suka bayyana ficewarsu daga NNPP har da kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Jibril Ismail Falgore da mataimakinsa, Hon. Muhammad Bello Butu Butu, da shugaban masu rinjaye, Hon. Lawan Hussaini Dala da mataimakinsa na Kibiya da mai tawatarwa Hon. Zawachiki na Kumbotso.

    Kawo yanzu dai gwamnan da ƴanmajalisar ba su bayyana jam'iyyar da zai shiga ba, amma dai ana hasashen ba zai wuce APC ba.

  5. Yan bindiga sun kashe mutum 6 a Jihar Neja - Ƴansanda

    ...

    Asalin hoton, NPF

    Ƴan sanda sun ce mutane 6 ne suka mutu ranar Juma'a a wani sabon hari da aka kai kusa da ƙauyen Wawa da ke jihar Neja da ke yankin a arewa ta tsakiyar Najeriya.

    A cewar rundunar ƴan sandan, ƴan bindigar sun yi wa wani uba da ɗansa kwanton ɓauna a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ziyarar ma’aikatan gona a wani ƙauye mai suna Damala.

    Ɗan yayi nasarar tserewa inda ya nemi agaji. Ƴan uwa da ƴa sa-kai da suka je neman mahaifin yaron su ma ƴan fashin sun kai musu hari.

    Daga bisani jami’an tsaro sun gano gawarwaki shida. Mutumin da aka fara kai wa hari da kuma wani mutum ɗaya kuma sun yi ɓatan dabo.

    An kai waɗanda lamarin ya shafa babban asibitin garin Wawa. Jami’ai sun ce ana gudanar da bincike, amma lamarin ya ƙara zurfafa fargabar da ake yi kan tabarbarewar tsaro a yankunan da ke kewaye da hanyar Neja zuwa Kwara.

    Garin Wawa dai yana kusa da gandun dajin Kainji kuma ya haɗa jihohin Neja da Kwara, da Jamhuriyar Benin, wanda ke bai wa ƴan bindiga damar kai hare-hare kan sansanonin sojoji su kuma ƙetara zuwa wasu ƙasashe.

  6. Bobi Wine ya zargi Jami'an tsaro da kai samame a gidansa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jagoran ƴan adawar Uganda Bobi Wine, ya zargi jami’an tsaro da kai wani mummunan hari cikin dare a gidansa da ke Kampala babban birnin ƙasar, inda aka ci zarafin matarsa ​​Barbara, wanda ya kai ga kwantar da ita a asibiti.

    A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, Wine ya ce ɗaruruwan sojoji sun kai farmaki gidansa da ke Magere da yammacin ranar Juma'a.

    Ya yi zargin cewa sojojin sun zo ne da tsani, inda suka fasa kofofi da tagogi tare da gudanar da bincike mai zurfi a gidan tare da neman sanin inda yake.

    ''Sun ƙwace wayoyi da kwamfuta da na'urorin intanet da na kyamarar CCTV, da duk wani abun da za su iya ɗauka," in ji shi.

    Wine ya ce an tsare matarsa ​​Barbara Kyagulanyi da bindiga inda aka umarce ta da ta bayyana inda yake.

    Daga baya an kai matarsa ​​asibiti, inda aka kwantar da ita sakamakon raunuka da kuma tsananin kaɗuwa da ta yi.

    Hukumomin gwamnatin Uganda dai ba su ce komai kan wannan zargi ba.

    Lamarin dai ya zo ne a daidai lokacin da rikicin siyasa ya ƙara ƙamari a ƙasar bayan zaɓen da aka gudanar a ranar 15 ga watan Janairu, wanda aka ayyana shugaba Yoweri Museveni a matsayin wanda ya lashe zaɓen, ya tsawaita wa'adinsa na kusan shekaru arba'in a karagar mulki da wasu shekaru biyar.

  7. Sojoji sun sha alwashin kuɓutar da masu ibada da aka sace a Kaduna

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar sojin Najeriya ta musanta iƙirarin cewa ta yi tafiyar hawainiya wurin kai ɗauki lokacin da aka kai hari a yankin Kurmin Wali da ke jihar Kaduna, inda aka sace masu ibada sama da 100 a ranar Lahadin da ta gabata.

    Wasu daga cikin al’ummar da ke ƙaramar hukumar Kajuru, sun yi zargin cewa sojojin sun yi ƙasa a gwiwa, inda suka yi zargin cewa jami’an tsaro ba su yi gaggawar kuɓutar da masu ibadar da aka sace ba.

    Sai dai shalkwatar tsaron ƙasar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su cikin gaggawa.

    A cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Michael Onoja ya fitar, ya bai wa al'ummar tabbacin ceto waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya.

    “Saɓanin iƙirari cewa an yi ƙasa a gwiwa wurin kuɓutar da waɗanda aka sace,Rundunar sojin ƙasa, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, suna ci gaba da aiwatar da ayyukan leƙen asiri a yankin dazukan da ƴan bindigar ke ciki,'' in ji sanarwar.

    Rundunar ta kuma jaddada aniyar ta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, inda ta sha alwashin sake haɗa waɗanda harin na Kurmin Wali ya rutsa da su da iyalansu.

  8. Amurka za ta rage tallafin tsaro da ta ke bai wa ƙawayenta

    The Pentagon

    Asalin hoton, Reuters

    Amurka za ta "taƙaita" irin taimako ta fannin tsaro da ta ke bai wa ƙasashen da ta ke ƙawance da su bisa ga sabon dabarun tsaron ƙasa na ma'aikatar Pentagon ta fitar.

    A wani gagarumin sauyi ga muhimman batutuwan da suka shafi tsaro, a yanzu ma'aikatar tsaron Amurka ta dauki tsaron Amurka da yankin yammacin duniya - ba ƙasar China ba - a matsayin abin da aka fi bai wa fifiko.

    A baya dai ma'aikatar tsaron Amurka ta bayyana barazanar da ake fuskanta daga ƙasar China a matsayin babban abin da aka fi mayar da hankali a kai.

    Wannan sabuwaer manufar na zuwa ne bayan kiraye-kirayen baya-bayan nan daga Shugaba Donald Trump, da suka hada da ƙara "raba nauyi" tsakanin abokan ƙawance wajen tunkarar barazanar da ake fuskanta daga Rasha da Koriya ta Arewa.

    Sabuwar dabarar tsaron ta yi kira ga ƙawayen Amurka da su tashi tsaye, ta na mai cewa abokan hulɗa sun kasance masu sakaci wurin barin Washington ta ci gaba da tallafawa ɓangaren tsaron ƙasashensu.

  9. Ƴansanda sun kama amarya kan zargin kashe angonta da guba a Jigawa

    Ƴansanda

    Asalin hoton, Police

    Rundunar ƴansandan Jigawa da ke arewacin Najeriya ta tabbatar da kama wata amarya bisa zargin kashe angonta makoni bayan aurensu.

    Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴanandan jihar SP Lawal Shi'isu Adama ya fitar ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Guaza da ke yankin ƙaramar hukumar Jahun, bayan da aka zargi matar da amfani a shinkafar ɓera (guba) wajen kashe mijin nata.

    Bayanan farko da ƴansanda suka samu sun nuna cewa angon ya ci abincinsa na rana a gida daga nan ya fara jinya, lamarin da ya a aka gaggauta kai shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

    ''Bayan da aka kama wadda ake zargin ta tabbatar wa ƴansanda cewa ita ce ta sa masa gubar a abincinsa, bayan da ta aiki wani ɗan'uwanta ya sayo mata shi a kasuwa'', in ji sanarwar.

    Amaryar ta ce iyayenta ne suka yi mata auren dole ne da mutumin da ta ce ba ta so, abin da ta ce ya sa ta ɗauki matakin kashe shi.

    Tuni dai kwamishinan ƴansandan jihar ya bayar da umarnin faɗaɗa bincike kafin gabatar da ita a gaban kotu.

    Ba wannan ne karon farko da ake samun matsalar kisa tsakanin ma'aurata ba a Najeriya, wanda galibi yakan faru sanadiyyar auren dole ko saɓani ko.

  10. Shettima ya koma Najeriya bayan halartar taron tattalin arziki na duniya

    Mataimakin shugaban Najeriya

    Asalin hoton, Stanley Nkwocha/X

    Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya Kashim Shettima ya koma Abuja bayan balaguron da ya yi inda ya shafe mako guda yana gudanar da harkokin diflomasiyya da tattalin arziki a ƙasashen Guinea-Conakry da Switzerland.

    Wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai Stanley Nkwocha ya fitar ta ce mataimakin shugaban ƙasar ya isa filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe ranar Asabar.

    Ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin rantsar da shugaban ƙasar Guinea, Mamadi Doumbouya, ya kuma jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron tattalin arziki na duniya (WEF) karo na 56 a Davos.

    Da farko dai Shettima ya ziyarci birnin Conakry, inda ya halarci bikin rantsar da shugaba Doumbouya, inda ya jaddada rawar da Najeriya ke takawa a cikin ƙungiyar ECOWAS da kuma buɗe sabbin hanyoyin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a fannin noma da masana'antu.

    A cewar mataimakin shugaban ƙasar, wannan tafiya ta nuna yadda gwamnatin Najeriya ta ƙara ƙaimi wurin tabbatar da haɗin kan yankin yammacin Afirka da kuma ƙudurin da ta ɗauka na sake farfado da tattalin arzikin ƙasa ƙarƙashin shugaba Tinubu.

  11. Zaftarewar ƙasa ta kashe mutum 7 a Indonesia

    ...

    Aƙalla mutane bakwai ne suka mutu yayin da wasu sama da 80 suka ɓace bayan zaftarewar ƙasa da ta afku a lardin Java ta Yamma a ƙasar Indonesia.

    Zaftarewar ƙasar ta afku ne a yankin West Bandung da ke kudu maso gabashin babban birnin Jakarta sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka kwashe kwanaki ana yi.

    Fiye da gidaje talatin ne suka ruguje bayan da "ƙasa ta binne wuraren zama, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka tare da shafar mazauna yankin", in ji wata sanarwa da hukumar daƙile bala'o'i ta Indonesia ta fitar.

    An kuma ba da sanarwar ambaliya, zaftarewar ƙasa da matsanancin yanayi a yankin mafi baki ɗaya.

    Zaftarewar ƙasa ta afku a ƙauyen Pasirlangu da misalin karfe 02:30 na safiyar ranar Asabar.

    An kwashe mutane da dama lami lafiya daga yankin da abin ya shafa, a cewar Abdul Muhari, shugaban sadarwa na hukumar bincike ta ƙasa.

  12. Ukraine ta koka kan hare-haren da Rasha ke kai wa yayin da ake tattaunawar zaman lafiya

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ukraine ta yi alla-wadai da wani sabon harin da Rasha ta kai cikin dare wanda ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu 23, yayin da ake shirin komawa tattaunawa da Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

    Ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha ya ce "mummunan" harin - wanda shugaban Rasha Vladimir Putin ya ba da umarnin kai wa "ba wai kawai ya shafi mutanenmu ba ne, har ma da tattaunawar sulhu da ake yi''.

    Tawagogin Rasha da Ukraine da Amurka sun yi taro a Abu Dhabi a karon farko tun bayan da Kremlin ta ƙaddamar da mamaya kan maƙwabciyarta a shekarar 2022.

    A rana ta biyu na tattaunawar a Abu Dhabi, Sybiha ya ce harin da aka kai a cikin dare ya nuna cewa "bai kamata Putin ya kasance a kwamitin zaman lafiya ba, sai da a gaban kotu ta musamman".

    A makon da ya gabata, shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Putin ya karɓi goron gayyata na shiga ‘Kwamitin zaman lafiya’ - ƙungiyar da za ta mai da hankali kan kawo ƙarshen rikice-rikice a duniya. Putin dai bai tabbatar da hakan ba.

  13. Ana ci gaba da zanga-zangar adawa da hukumar ICE a Minnesota

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Daruruwan ƴan kasuwa a jihar Minnesota sun rufe shagunansu ranar Juma'a kuma dubban masu zanga-zangar sun fito cikin tsananin sanyi don nuna adawa da ayyukan samame da hukumar shige-da fice ta Amurka (ICE) ke ci gaba da gudanarwa a jihar.

    Zanga-zangar ta ƙara zafi ne bayan masu shiryata sun ƙarfafa wa mazauna yankin gwiwa da su daina aiki ko makaranta domin su fito nuna adawa da hukumar ta ICE.

    Hukumar ICE dai ta shafe sama da makonni shida ta na gudanar da samame a jihar Minnesota a ƙarƙashin umarnin gwamnatin Donald Trump.

    Hukumar ta bayyana aikin a matsayin wani mataki na kare lafiyar jama'a da nufin korar masu aikata laifuka da suka shigo ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

    Masu sukar wannan mataki sun yi iƙirarin cewa abin na sahfar ƴan cirani da ba su da wani laifi kuma ana hadawa da wasu ƴan Amurka ma yayin samamen.

    An tura dubban jami'an tsaro na tarayya zuwa Minnesota a matsayin wani ɓangare na aikin da aka yi wa laƙabi da "Operation Metro Surge".

  14. Kotu ta fara zaman yanke hukunci a shari'ar jagoran adawa a Afrika ta kudu

    Julius Malema

    Asalin hoton, Getty Images

    Dubban magoya bayan ɗan siyasar Afirka ta Kudu Julius Malema ne suka hallara a gaban wata kotu a ranar Juma'a a daidai lokacin da kotun ta fara zaman sauraron bayanai gabanin yanke hukunci a shri'ar da ke masa bisa zargin mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba.

    Julius Malema, wanda ya shahara saboda irin nau'in siyasarsa, yana iya rasa kujerarsa a majalisar dokokin ƙasar idan har kotu ta yanke masa hukuncin ɗauri na fiye da watanni goma sha biyu.

    A watan Oktoban da ya gabata ne dai aka same shi da laifin harba bindiga bisa ka'ida ba yayin bikin cika shekaru biyar na EFF a shekarar 2018.

    Hukunci mafi tsauri da kotu za ta iya yanke masa shi ne zaman gidan yari na tsawon shekara 15.

  15. Malami ya zargi DSS da yi wa shari’arsa zagon ƙasa

    Abubakar Malami

    Asalin hoton, Abubakar Malami

    Tsohon ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da wasu ayyuka da ya ce suna da nufin tauye masa haƙƙinsa na samun adalci a shari'ar da ake yi masa.

    A wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mohammed Bello Doka ya sanya wa hannu, Malami ya ce ana ci gaba da hana shi ganawa da lauyoyinsa lamarin da ke kawo masa cikas wurin kare kansa daga zarge-zargen da ake yi masa

    Ya bayyana abin da hukumar ta DSS ke yi a matsayin wani mataki na yi wa doka zagon ƙasa.

    Sanarwar ta ce "Waɗannan jerin abubuwan da ke faruwa suna nuni ne da wani tsari na kama mutum kafin ma a gudanar da bincike, inda ake neman tattara shaida bayan tsarewa, matakin da ya saɓa wa doka da kuma ƴancin da tsarin mulki ya ba shi," in ji sanarwar.

    Sanarwar ta ci gaba da cewa, kama shi da aka yi ya zo ne a daidai lokacin da ya ke buƙatar ya kare kansa a shari’arsa da hukumar EFCC gaban babbar kotun tarayya.

    Malami ya ƙara jaddada aniyarsa na kare kansa a gaban kotu.

  16. NNPP ta mayar wa Abba Kabir martani kan ficewa daga jam’iyyar

    ...

    Asalin hoton, facebook/Abba Kabir Yusuf

    Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta yi kakkausar suka kan matakin da gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na ficewa daga jam'iyyar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri’ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.

    A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Ladipo Johnson ya fitar, jam’iyyar ta ce matakin da Gwamna Yusuf ya ɗauka tamkar cin amanar al’ummar jihar Kano ne, wanɗanda a cewarta, sun kaɗa masa ƙuri’a ne sakamakon daɗewar da ya yi yana tare da tafiyar siyasar Kwankwasiyya.

    ''Muna matuƙar takaicin yadda Gwamna Abba, mutumin da al’ummar Jihar Kano suka damka wa al’ummar Jihar kan karfin biyayya da sadaukarwar da ya yi na tsawon shekaru da dama da ya yi wa tafiyar Kwankwasiyya, a yanzu ya zaɓii ya ci amanar da aka miƙa masa.'' in ji sanarwar

    Ta kuma ƙara da cewa ''Wannan mataki na iya mayar da jihar hannun waɗanda suka daɗe suna adawa da ci gabanta da muradun al’ummarta.''

    Jam’iyyar NNPP ta buƙaci magoya bayanta a Kano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, su kuma yi taka-tsan-tsan kan duk wani abu da zai iya haifar da tarzoma a siyasance ko kuma ta da zaune tsaye.

  17. Rasha ta kai hari kan Ukraine yayin da tattaunawa kan kawo ƙarshen yaƙin ke gudana

    ...

    Asalin hoton, Emergency Service of Ukraine

    Rasha ta ƙaddamar da hare-haren jirage marasa matuƙa da makamai masu linzami kan Ukraine cikin dare, inda ta kashe mutum ɗaya tare da raunata wasu 23 duk da cewa ta shiga tattaunawa da Amurka da nufin kawo ƙarshen yaƙin.

    Magajin garin Kyiv babban birnin ƙasar Ukraine ya ce mutum ɗaya ya mutu, huɗu kuma sun jikkata sakamakon wani ƙazamin harin da Rasha ta kai, yayin da magajin garin Kharkiv ya ba da rahoton cewa mutane 19 ne suka jikkata a wani hari da aka kai a birnin.

    Tawagogin Rasha da Ukraine da Amurka sun yi taro a Abu Dhabi a tattaunawar farko ta ɓangarorin uku tun bayan da Kremlin ta ƙaddamar da mamaye makwabciyarta a shekarar 2022.

    Wata majiya ta shaida wa BBC cewa an samu ci gaba a tattaunawar amma har yanzu ba a warware muhimmin batu da ya shafi mallakar yankuna ba.

    Rasha ta mamaye kusan kashi 20% na yankunan Ukraine, gami da sassan yankin gabashin Donbas.

    Kremlin na son ta cib gaba da riƙe wadannan yankuna har ma da ƙarin wasu, amma Ukraine ta dage kan cewa hakan ba zai yiwu ba.

  18. Manoman Zimbabwe sun nemi taimakon Trump wurin karɓar diyya daga gwamnatin ƙasarsu

    ...

    Asalin hoton, AFP

    Tsofaffin manoma fararen fata na Zimbabwe suna neman gwamnatin Amurka ta taimaka musu domin samun diyya daga gwamnatin ƙasar kan gonakin da aka ƙwace a ƙarƙashin mulkin tsohon shugaban ƙasar Robert Mugabe.

    Wata ƙaramar ƙungiyar manoma ta tabbatar da cewa ta rubutawa wani kamfani da ke da alaƙa da Shugaba Trump wasiƙa domin ya matsawa Washington lamba don neman a gaggauta biyansu diyyar fiye da dala biliyan uku da suke bin gwamnatin Zimbabwe.

    Wakilin ƙungiyar manoma Bud Whitaker ya shaida wa BBC cewa da yawa daga cikin mambobin yanzu sun tsufa kuma suna neman masu sayen hannayen jari da suka samu daga gwamnati a matsayin diyya.

    Gwamnatin Zimbabwe ta ƙwace gonakin fararen fata sama da dubu huɗu, daga shekara ta 2000 a matsayin wani ɓangare na manufofin gyara abubuwan da suka faru a zamanin mulkin mallaka.

  19. Shugaban Ivory Coast ya ƙaddamar da sabuwar majalisar ministoci

    Alassane Ouattara

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya sanar da sabuwar majalisar ministocin ƙasar inda babu wasu manyan sauye-sauye baya ga ficewa daga gwamnatin ministan noma Kobenan Kouassi Adjoumani, wanda ke da alaƙa ta ƙut-da-ƙut da shugaba Ouattara.

    Téné Birahima Ouattara, ɗan'uwan Shugaba Alassane Ouattara, wanda a baya shi ne ministan tsaro, ya zama mataimakin firaminista gami da matsayinsa na baya.

    Robert Beugré Mambé, mai shekaru 72, wanda aka sake naɗawa a matsayin Firaministan Ivory Coast a farkon wannan makon, ya jaddada cewa sabuwar majalisar za ta ba da fifiko kan muradun jama'a da hadin kan ƙasa da kuma ci gaban tattalin arziki.

    Sabuwar majalisar ministocin ƙasar za ta iya dogaro da goyon bayan sabuwar majalisar dokokin ƙasar, ƙarƙashin jagorancin Patrick Achi, tsohon firaminista.

    Jam'iyya mai mulki, Rally of Houphouëtists for Democracy and Peace (RHDP), ita ke riƙe da sama da kashi 75% na kujerun majalisar dokokin.

  20. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara kan labaran da mu ke wallafawa.