Me Nasir El-Rufa'i ke nema a siyasance?

Malam Nasir El Rufa'i

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Lokacin karatu: Minti 5

Tambayar kenan da an Najeriya ke yi cewa me Malam Nasir ElRufa'i ke nema a siyasance, tun bayan wata tattaunawa irinta ta farko da kafar yada labarai a Najeriya da tsohon gwamnan jihar Kadunan ya yi tun bayan saukarsa daga mulki a 2023.

Tattaunawar da za a shafe tsawon lokaci ana fedewa da kuma fassara abubuwan da ta kunsa, masu nauyin gaske, inda a ciki El Rufa'i ke cewa shi ba zai taa komawa jam'iyyar hamayya ta PDP ba amma kuma shi har yanzu ɗan APC ne.

Dama dai tun bayan rashin nasarar tsallake tantancewar majalisar dattijai domin nadawa a matsayin minista a gwamnatin shugaba Bola Tinubu, al’umma da sauran masu nazari kan siyasa ke neman sanin abin da ke kunshe a cikin zuciyar dan siyasar, wanda lokaci zuwa lokaci kan tayar da kura a fagen siyasar ta Najeriya, kamar yadda ya yi a tattaunawar tasa ta baya-bayan nan.

To sai dai har yanzu za a iya cewa ’yan Najeriya na cike da rashin tabbas dangane da haƙiƙanin abin da tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ke son cimmawa a siyasance.

Gabanin sauka daga mukamin gwamna, Nasir El-Rufa'i ya ce idan ya gama wa’adin mulkinsa na shekara takwas zai koma gefe ne domin gudanar da harkokinsa na karatu da sauran abubuwa, yana mai cewa ba zai shiga harkokin gwamnati a jiha da matakin ƙasa ba kuma ba zai karɓi muƙami ba.

Ko a lokacin kamfe na shugabancin ƙasar a 2023, sai da ɗantakarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya nemi El-Rufa'i da ya kawar da alƙawarinsa na ƙin shiga gwamnati.

To sai dai duk da jajircewar da ya yi wajen kafa wannan gwamnati mai ci, tafiyar ba ta je ko ina ba, sai ga shi an gan su a rana.

A karshe kuma cikin tattaunawarsa da kafar talabijin ta Arise, sai ga shi El-Rufa’in ya kammala fallasa duk wani sauran sirrin da ya rage tsakaninsa da wadanda ake wa kallon abokan siyasarsa na kut da kut.

Wani abu da ya sa jama'a ke neman sanin ko wane abu El-Rufa'in ke nema a siyasance.

'Da wuya El-Rufa'i ya nemi takara'

El Rufa'i

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Bayanan hoto, El Rufa'i tare da Bola Tinubu lokacin da Tinubu ya nemi goyon bayan El Rufa'i a 2023.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da a yanzu ya bayyana cewa bai shirya barin fagen siyasa ba, wani tsohon ma'aikaci ga Nasir El-Rufa'i wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa ba ya tsammanin tsohon gwamnan jihar ta Kaduna zai sake yin wata takara.

"Zancen gaskiya malam Nasiru mutum ne mai basira da kuma buri sannan kuma mutum ne da ke son juya al'amura. Saboda haka idan ka san wane ne Malam Nasiru to ka san zai wuya ya tsaya takara.

"Abin da na fi tunanin yake so shi ne a kafa gwamnatin da zai dama a cikinta da kuma samun ƙarfin faɗa-a-ji. Duk abin da kuka ga yana yi a yanzu ba na ji za ta kai shi ga takara illa dai ya mara wa wani ɗan siyasa baya yadda idan aka samu nasarar zai samu ƙumbar susa." In ji tsohon ma'aikacin El-Rufa'i." In ji majiyar ta BBC.

Ya ƙara da yin bayani kan dalilan da suka sa El-Rufa'i ba samu muƙami ba a gwamnatin Tinubu.

"Kasancewarsa mai basira da buri da kuma son nuna iyawa ne ya sa wasu da ke ganin idan ya shiga gwamnatin to zai iya yi musu illa. Wannan dalilin tare da dalilai na tsaro da aka ace sun taimaka, su ne suka hana shi samun muƙami a gwamnatin Tinubu." In ji tsohon ma'aikacin El-Rufa'i,

'El-Rufa'i na son haɗa kan ƴan adawa'

Atiku da El Rufa'i

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Bayanan hoto, Atiku da El Rufa'i lokacin da suka je gaisuwar rasuwar Edwin Clark a Abuja.

Farfesa Tukur Abdulƙadir, masanin kimiyyar siyasa kuma malami a jami'ar jihar Kaduna, ya ce ba wani sabon abu ba ne game da Malam Nasir El-Rufa'i, inda tun bayan gaza samun muƙami a wannan gwamnati ya fara sa zare da gwamnatin APC.

"Shi dai yanzu El-Rufa'i na ƙoƙarin haɗa kan ƴan hamayya bisa la'akari da irin ziyarce-ziyarce da ganawa da ƴan siyasa kuma idan aka yi la'akari da irin kalaman da yake yi a baya-bayan nan lallai alamu na nuna cewa adawa zai yi mai ƙarfi wajen tunkarar gwamnatin APC."

Amma kuma sai nan gaba kamar shekara mai zuwa ne za a iya gano haƙiƙanin take-takensa da tasirinsa kasancewar lokacin ne siyasar za ta kankama sannan al'amuranta su ƙara zafafa." In ji Farfesa Tukur.

Wane tasiri El-Rufa'i zai yi a hamayya?

El Rufa'i da Kwankwaso

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Farfesa Tukur Abdulƙadir ya ce tasirin da El-Rufa'i zai yi ya dogara ne kacokan wajen ƙarfi da tasirin da waɗanda zai haɗa kai da su wato masu hamayya domin tunkarar jam'iyya mai mulki.

"Akwai yiwuwar yin hamayya mai ƙarfi a nan gaba daga ƴan adawa to amma kuma wani abu shi ne ita kuma gwamnatin da jam'iyyar APC ba za su tsaya su zura musu ido ba.

"Wani abu da yake da sanyaya gwiwa dangane da tasirin haɗe kan abokan hamayya, shi ne kasancewar da wuya a samu wani jagora guda ɗaya tilo karɓaɓɓe wanda jama'a ke girmamawa kamar tsohon shugaba Muhammadu Buhari."

"Shi ne mutum mai jama'a da kwarjini da abokan hamayya suka saka a gaba kuma suka yi nasara. Amma yanzu da wuya a sake samun irin wannan a nan gaba saboda a yanzu dai babu mai wannan ƙimar irin ta Buhari. Saboda haka akwai jan aiki a gabansu bisa la'akari da irin yanayin siyasar da ake yi da kuma irin ƴan siyasar da ake da su a yanzu" In ji Farfesa Tukur Abdulƙadir.

El-Rufa'i bai bar jam'iyyar APC ba

El Rufa'i

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Duk da cewa har yanzu Malam Nasir El-Rufa'i ɗan jam'iyyar APC ne kuma ya ce yana magana ne domin a gyara, to amma ana yawan ganin sa da manyan ƴan hamayyar jam'iyyar da suka haɗa da Atiku Abubakar na jam'iyyar hamayya ta PDP da Peter Obi na LP da Rabi'u Kwankwaso na NNPP.

A makon da ya gabata ne El-Rufa'i ya yi wa Atiku Abubakar na PDP rakiya zuwa wurin gaisuwar rasuwar dattijo Edwin Clark, inda har El-Rufa'i ya yi kira ga al'ummar yankin kudu maso kudu da su haɗa kai da na arewacin ƙasar domin ceto Najeriya.

A baya-bayan nan kuma an ga tsohon gwamnan na karɓar baƙuncin ɗaiɗaikun masu hamayya da suka haɗa da Hajiya Naja'atu Muhammad wadda ta shahara wajen sukar gwamnatin Bola TInubu.

Duk da dai El-Rufa’in a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise ya ce ziyarar da yake yi ba shi ne ke nufin ya koma jam’iyyar mutanen da ya hadu da su ba, hasali ma, ya kawar da duk wata yiwuwar komawarsa babbar jam’iyyar hamayya ta PDP.