Me ya sa El Rufa'i ke jan zare da jam'iyyar APC?

El Rufa'i

Asalin hoton, Onanuga/El Rufa'i/X

Lokacin karatu: Minti 4

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i, a karon farko ya caccaki jam'iyyar APC a bainar jama'a inda ya bayyana jam'iyyar APC mai mulki da wadda ta "sauka daga aƙidun dimkoraɗiyya da aka kafa ta a kai".

El Rufa'i dai ya bayyana hakan yayin gabatar da jawabi a wani taron da aka shirya kan hanyoyin ciyar da dimokraɗiyya gaba a Najeriya, da aka gudanar a Abuja.

Wannan ne kuma ya janyo zazzafar martani daga jam'iyyar APC mai mulki da ma ɓangaren fadar shugaban ƙasa.

Za dai a iya cewa wannan ne karon farko da tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya fara fitowa fili ya soki salon kamun ludayin jam'iyyar APC, tun bayan da majalisar dokokin ƙasar ta gaza tantance shi a matsayin minista a Najeriya.

Kalaman Nasiru El Rufa'i

Malam Nasiru El Rufa'i

Asalin hoton, El Rufa'i/Onanuga/X

Da farko dai Malam Nasir El Rufa'i ya bayyana halin da ake ciki dangane da shugabanci da hamayya a Najeriya da "abin da ke neman ɗaukin gaggawa".

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana damuwarsa dangane da abin da ya ƙara kira da "rashin bin ƙa'idojin dimokraɗiyya da ingantattun tsare-tsaren jam'iyyar APC.

"Jam'iyyar APC ta sauka daga tsarin da aka gina ta. A tsawon shekaru biyu ba a yi taron sassan jam'iyyar ba kamar taron masu ruwa da tsaki da majalisar zartarwa. Ba a yi ko ɗaya ba. Sai ka kasa fahimtar cewa ko dai jam'iyyar ta zama ta mutum ɗaya ne;.." In ji El Rufa'i.

Ya kuma buƙaci jam'iyyun hamayya su haɗa hannu da ƙarfe wajen tunkarar jam'iyya mai muli a kakar zaɓe mai zuwa.

Bugu da ƙari, El Rufa'i ya zargi jam'iyyar APC da kitsa maƙarƙashiya ga zaman lafiyar sauran jam'iyyun hamayya a ƙasar.

"Akwai sojin haya a PDP da aka ɗauka domin rusa jam'iyyar. Ita ma jam'iyyar Labour Party tana fuskantar irin matsalolin. Peter Obi da kansa ya faɗa min cewa "ban san me ke faruwa da jam'iyyar da na tsaya takara a cikinta ba."

Martanin fadar shugaban ƙasa

Tuni dai fadar gwamnatin Najeriya ta mayar wa da tsohon gwamnan jihar ta Kaduna martani.

Babban mai taimaka wa shugaban ƙasa kan sadarwar tsare-tsaren gwamnati, Daniel Bwala, a shafinsa na X, ya bayyana takaicinsa Inda ya ce kalaman na El Rufa'i ka iya zama wasu daban ba waɗannan ba idan da ace ya cikin gwamnatin shugaba Tinubu.

"Yayana idan da ace kana cikin gwamnatin, shin irin wannan matsayar za ka ɗauka?

"Tarihi ne ke maimata kansa. Gwamnati ce da ka yi aiki a ɗaya daga cikin sassanta, da kake son yanzu ka rusa. Haba Mallam, a ji tsoron Allah mana."

Shi ma darektan yaɗa labaran jam'iyyar ta APC, Bala Ibrahim ya ce ya kamata El Rufa'i ya miƙa kokensa ga shugabancin jam'iyyar ta APC a maimakon fitowa fili ya nemi ya zubar mata da ƙima.

Ba zan fita daga APC ba - El Rufa'i

Tsohon gwamnan na Kaduna, Malam Nasir El Rufa'i ya ce ba shi da niyyar fita daga jam'iyyarsa ta APC.

Ya faɗi hakan ne a wani martani da ya yi na ƙarfafa labarin da jaridar The Nation ta yi.

Da ma dai El Rufa'i ya shaida wa ƴanjarida cewa ba zai bar jam'iyyar ta APC ba a yayin wata tattaunawa da suka yi da shi bayan taron na ranar Litinin.

"Ba na shirin barin jam'iyyar," in ji shi, inda ya ƙara da cewa yana sa ran jam'iyyar ta APC za ta ƙara ƙwazo.

Da dama ƴan Najeriya dai sun fara hasashen ficewar El Rufa'i daga jam'iyyar bisa la'akari da yadda ya kwance mata zane a kasuwa.

Ihu bayan hari - Sharhi

Malam El Haroon Muhammad, mai sharhi kan harkokin yau da kullum sannan masanin hulɗar jakadancin ƙasashen duniya ya ce kalaman Malam Nasiru El Rufa'i "ihu ne bayan hari".

"El Rufa'in nan fa shi ne ya yi uwa ya yi makarɓiya wajen kawo wannan gwamnati inda a lokacin ya ɓata da ƴan kinsa har ma yake cewa babu dattijo.

Ita da ma siyasa ai haka ta gada. Sun ci moriyarsa sun yada kwauren. Yanzu ya kamata ƴan arewa su gane mai ƙaunarsu saboda Allah da mai ƙaunarsu saboda irin gudunmowar da za su bayar wadda daga nan an gama amfani da su." In ji Malam El Haroon Muhammad.

Babu dattijo a Arewa - El Rufa'i - 2023

Malam Nasiru El Rufa'i

Asalin hoton, El Rufa'i/X

Caccakar da Nasiru El Rufa'i ya yi wa jam'iyyar APC a bainar jama'a a karon farko ta sa ƴan Najeriya da dama musamman masu fashin baƙi ganin tsohon gwamnan na yin da-na-sanin irin rawar da ya taka a 2023 wajen taimakawa ɗora gwamnatin Tinubu a kan mulki.

A wata hira da BBC Hausa a watan Fabrairun 2023, Malam El Rufa'i ya ce za su yi iya yinsu wajen ganin sun lalata dukkannin ƙulle-ƙullen da wasu dattawan Arewacin ƙasar ke yi na ganin takarar Bola Tinubu ba ta yi tasiri ba.

"Batun wani dattawa, ba wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekara 63, don haka su waye dattawan Arewa, mu gwamnonin Arewa mu ne dattawan Arewa kuma mune shugabannin Arewa."

"Don haka mun ja layi sannan mun lashi takobin idan Allah ya yarda za mu kunyata su." In ji El Rufa'i.