Sasanta mahaifina da gwamna Uba Sani ba aikina ba ne – Bello El-Rufai

Bello, wanda ɗa ne ga Nasir El-Rufa'i makusancin gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ne kafin zama ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta arewa
Bayanan hoto, Bello El-Rufa'i makusancin gwamnan Kaduna ne kafin zama ɗan majalisa mai wakiltar Kaduna ta arewa
    • Marubuci, Madina Maishanu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A daidai lokacin da alamu ke nuna cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani da tsohon gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa'i na ƙara rincaɓewa, ɗa ga El-Rufa'i ya bayyana ra'ayinsa game da lamarin.

Bello El-Rufai, wanda ɗan majalisa ne mai wakiltar mazabar Kaduna ta Arewa ya bayyana a cikin shirin Mahangar Zamani na BBC cewa ba ya jin daɗin abubuwan da ke faruwa tsakanin tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i da gwamnan jihar mai ci, Uba Sani, duba da matsayin dukkansu biyu a rayuwarsa.

Rashin fahimta tsakanin tsohon gwamnan da magajinsa ƙasa da shekara ɗaya bayan kafa sabuwar gwamnati a jihar ta Kaduna.

Tun farko gwamna Uba Sani ya koka game da ɗimbin bashin da ya yi zargin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Ruda'i ya bari, inda ya ce gwamnatin jihar ba za ta iya biyan ko da albashin ma'aikata ba da ƴan kuɗaɗen da take samu.

Sannan daga baya Majalisar Dokokin jihar ta ƙaddamar da bincike kan tsohuwar gwamnatin jihar bisa zargin rashin bin ƙa'ida wajen ciyo bashi da kuma zurarewar kuɗi naira biliyan 423 ba tare da wani ciakken bayani ba.

Sai dai gwamnan ya musanta duk waɗannan zarge-zarge inda ya shigar da ƙara a kotu yana ƙalubalantar majalisar.

Bello El-Rufa'i ya ce: "Ba daɗi mana, ko mutum maƙiyina ne ba na so na ga yana fada da wani makiyina, ina son zaman lafiya."

Bello ya kuma alakanta lamarin da yadda rayuwa kan iya sauyawa a kowane lokaci, "aure na rabuwa, abokai su daina abokantaka, kawai ya kamata dai a bar zumunci duk kuwa da kowane irin rikici aka shiga."

Me ya haɗa su?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bello dai ya ce bai san abin da ya hada mahaifin nasa da tsohon ubangidansa ba, inda ya shaida cewa ba ya tsammanin kowannensu na rigima da juna don bai taba jin kowannensu ya fito ya zagi dayan a wurinshi ba.

A cewarsa bai ma san ko fadan da ake zargin suna yi da gaske ne kamar yadda mutane ke yayatawa ba.

"A cikinsu ba wanda ya ce min komai kan rikicin, ni dai kawai na gane cewa yanzu ba da ba ne."

Bello ya kuma nuna kamar mutane ne ke zuzuta rikicin fiye da abin yake a kasa da burin ya zama wani babban rikici.

"Mutane suna so abin ya zama kamar Dramendra da Amitabh Bachchan [na fim din Indiyawa] na fada, har kira na wasu ke yi don jin karin bayani kan abin da ya faru."

Mutane da dama sun dade suna son su ji daga bakin Bello kasancewar, kusancinsa da gwamnan jihar.

A shekarun baya ya taba zama mataimakinsa kuma shi ya ba shi shawarar fitowa takarar dan majalisa kamar yadda ya shaida wa BBC.

Sai dai sabanin yadda Bello ya ce ba wanda ya fito a cikinsu ya yi magana maras dadi kan dayan a wurinsa, a cikin makon nan, Mallam Nasir El-Rufai ya mayar wa Uba Sani kakkausan martani a shafukan sada zumunta kan wasu kalaman gwamnan da ba su yi masa dadi ba.

Mutanen biyu waɗanda a baya aminan juna ne a fagen siyasa, abubuwa sun sauya tun bayan sauyin gwamnati da kuma takun-saka da ta kunno kai bayan da Uba Sani ya hau kan kujerar gwamna.

Daga lokacin ne aka fara bijiro da batun binciken gwamnatin El-Rufa'i kan yadda gwamnatinsa ta kashe kuɗi a zamaninta, lamarin da ya nuna alamun rikici ke nan a tsakaninsu.

Lamarin ya ba mutane da dama mamaki kasancewar masu lura da al’amuran siyasa na ganin cewa El-Rufai ne ya yi ruwa da tsaki wajen samun nasarar Uba Sani a takarar gwamna.

Bello dai ya ce a ganinsa wannan ba wani abu ba ne saboda bincike ba laifi ba ne amma idan ana yi tsakani da Allah ba tare da wata manufa ba.

"Bincike ba wani ba ne ba, amma idan kana bincike don zalunci ko don tozarta wani ko don wani ya maka laifi toh Allah sai ya hukunta ka. Allah zai yafe maka komai amma ban da shiga hakkin wani."

Za a iya sassanta su?

...

Da aka tambayi Bello ko ya na ganin zai iya sasanta su, cewa ya yi karara "wallahi ba aikina ba ne, aikina shi ne mayar da hankali kan taimaka wa mutanen mazabar Kaduna ta Arewa."

Ya nuna cewa yana son zaman lafiya kuma da ya so hakan a tsakaninsu.

"Ina son zaman lafiya da rike amana, idan mutum ya taba min abu ko za mu yi rigima da shi amma ba a waje ba, amma wannan ni ke nan."

Bello ya nuna a karshe cewa, akwai yiwuwar dawo da zaman lafiya tsakanin su biyun, ya kara jaddada matsayin dukanninsu biyu da kuma yadda yake yi musu addu'ar zaman lafiya a tsakaninsu.

"A wurina ba wanda ya kai Mallam Nasiru a siyasance, aikin shi kawai yake sawa a gaba kuma ba wanda nake so na zama kamar shi, kuma ubana ne, uba uba ne."

"Sannan game da shi gwamna Uba Sani duk wadanda ke jira na fadi wani abu game da shi, na ba ni mamaki."

A jihohi da dama a Najeriya dai ana ci gaba da samun lamari mai kama da irin wannan inda ake samun tsamin dangantaka tsakanin tsoffin gwamnoni da wadanda suka mara wa baya don su gaje su.