Manchester United na son Finn Jeltsch, Aston Villa ta taya Mateta

Hoton Finn Jeltsch

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United na nazarin yiwuwar tuntubar Stuttgart domin sayen matashin dan bayan Jamus, Finn Jeltsch, mai shekara 20.

Aston Villa ta gabatar da tayi domin sayen dan wasan gaba na Crystal Palace kuma dan kasar Faransa, Jean-Philippe Mateta, mai shekara 29, sai dai tayin ya yi kasa da farashin da Palace ke nema.

Haka kuma Villa na gab da cimma yarjejeniya ta yuro miliyan 70, kimanin fam miliyan 59.8, domin daukar dan wasan gaba na Chelsea da Senegal, Nicolas Jackson, mai shekara 25.

Manchester City na shirin gabatar da tayi a hukumance ga Chelsea domin sayen dan wasan tsakiya na Argentina, Enzo Fernandez, mai shekara 25, kafin rufe kasuwar musayar 'yan wasa.

Tottenham na iya kwace dan wasan gefe na Marseille da Aljeriya, Amine Gouiri, mai shekara 26, wanda Napoli ma ke zawarcinsa.

Newcastle za ta gabatar da tayi na karshe da ya kai yuro miliyan 60, kwatankwacin fam miliyan 51, domin sayen dan wasan gaba na Lille da Belgium, Matias Fernandez-Pardo, mai shekara 21.

Leeds United da Crystal Palace sun nuna sha'awar daukar dan bayan Everton da Jamhuriyar Ireland, Jake O'Brien, mai shekara 25.

Nottingham Forest na tattaunawa da kungiyar Corinthians ta Brazil kan yiwuwar daukar dan wasan tsakiya mai shekara 20, Andre.

Hull City ta cimma yarjejeniya da Union Berlin domin sayen dan wasan gaba na Jamus, Ilyas Ansah, mai shekara 21. Ana sa ran cinikin zai haura fam miliyan 20, kimanin fam miliyan