Wasiyyar da Buhari ya ba ni kan talakawan Najeriya - Peter Obi
Tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam'iyyar LP, Peter Obi ya ce marigayi tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ba shi wasiyya a lokacin da suka gana yayin da yake yaƙin neman ƙuri'ar jama'a a gabanin zaɓen 2023.
Peter Obi ya bayyana wa ƴan jarida batun wasiyyar da Buhari ya ba shi ne a yayin ziyarar ta'aziyya da ya kai Daura domin jajanta wa iyalan marigayin.
"Lokacin da nake takarar shugabancin Najeriya, na gana da shi (Buhari) kuma zan iya tuna roƙon da ya yi min, inda ya kama sunana ya ce "Peter, don Allah ka kula da talakan Najeriya". In ji Peter Obi.
"Kuma ina iya tuna cewa na amsa masa da, ai wannan muhimmi ne, ginshiƙi ne a gare ni na zuba makudan kuɗi a muhimman fannonin ci gaban jama'a. Abubuwa kamar Ilimi da lafiya sannan na tsamo mutane daga talauci."
"Na yi imanin matuƙar ba a tsamo mutanen daga halin talauci ba, to ba za mu iya magance matsaloli kamar na rashin tsaro da muke fama da su ba," kamar yadda tsohon ɗantakarar shugabancin Najeriya a LP, ya ƙara haske.
Dangane kuma da tambayar da aka yi wa tsohon ɗantakarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar LP, kan halayyar Buhari da ya kamata ƴan Najeriya su koya, sai ya ce:
"Sauƙin kai da rashin ɗaukar rayuwa da zafi. Kuma ina addu'ar Allah ya ji ƙansa da rahama kuma Allah ya yi wa zuri'arsa albarka a koyaushe." In ji Peter Obi.
Me Peter Obi yake so?

Asalin hoton, Peter Obi/X
Ɗan takarar shugabancin Najeriya a 2023 a jam'iyyar Labour, Peter Obi ya tabbatar da cewa zai yi takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar ADC, inda ya yi watsi da yiwuwar zama mataimakin Atiku Abubakar.
Obi ya bayyana hakan ne a gidan talbijin na Channels a farkon watan Yuli.
"Zan tsaya takarar shugaban ƙasar jamhuriyar Najeriya, kuma na yi imani ina da cancantar yin hakan." In ji Obi.
"..Babu wanda ya taɓa tattauna batun (kasancewa mataimakin Atiku Abubakar). Mutane suna tsammanin abubuwa da yawa. Babu mutumin da ya taɓa magana da ni akan wannan cewa ko zan zama kaza ko kaza".












