Mece ce makomar manyan jam'iyyun adawa a Najeriya?

....

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Peter Obi/Nasir El-Rufai/Facebook

    • Marubuci, Chukwunaeme Obiejesi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Reporter
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

A yanzu Najeriya ta zamo tamkar ƙasar da ke amfani da tsarin jam'iyya ɗaya, a yayin da manyan jam'iyyun adawar ƙasar biyu ke fama da rikicin cikin gida wanda ke kawo rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyun.

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa Olalekan Ige, ya shaida wa BBC cewa, bisa la'akari da yadda abubuwa ke tafiya dukkan manyan jam'iyyun adawa biyu, wato PDP da Labour Party, wadanda suka samu kuri'u fiye da miliyan 13 a zaben shugaban kasa na 2023, ba za su iya fitar da kwakkwaran dan takarar da zai yi gogayya da jam'iyya mai mulki ta APC a zaben 2027 ba.

Tun bayan zaben 2023, jam'iyyun adawar ke fama da matsala daga wannan zuwa waccan, abin da ke sanya wasu fitattu a jam'iyyar na sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

A cikin zaɓukan cike gurbi na gwamnoni guda huɗu da aka gudanar bayan babban zaben Najeriya na 2023, APC ta lashe uku, ciki har da na jihar Edo inda ta ƙwace mulki daga hannun PDP.

Batun shugabanci a jam'iyyar Labour na ƙara tsananta

 Lamidi Apapa, Nenadi Usman, da kuma Julius Abure

Asalin hoton, Lamidi Apapa/Nenadi Usman/Facebook/Labour Party

Bayanan hoto, Dukkan wadannan mutum ukun na ikirarin shugabanci a jam'iyyar Labour

A baya-bayan nan ne kotun ƙoli ta yanke hukuncin da aka yi tunanin zai kawo ƙarshen rikicin shugabancin da jam'iyyar ke fama da shi, to amma sai ya zamanto kamar hukuncin ya ƙara ta'azzara rikicin.

A maimakon mutum biyu da ke ikirarin cewa su ne shugabannin jam'iyyar, a yanzu mutum uku ne ma suke ikirarin shugabancin wato da Julius Abure da Nenadi Usman da kuma Lamidi Apapa.

Kotun ƙolin ta yanke hukuncin cewa babu wata kotu da take da ƴancin tsoma baki a rikicin shugabancin jam'iyya, kasancewar "lamari ne na cikin gida."

A ranar Laraba 9 ga watan Afrilu ne, tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar ta Labour na ƙasa ya ayyana kansa a matsayin shi ne shugaban jam'iyyar na ƙasa ya na mai cewa tun da kotu ta cire Abure," Shi Lamidi Apapa, wanɗa shi ne mataimakin shugaban jam'iyyar a yanzu kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya bashi damar jan ragamar ta."

Wannan kuma ta zo dai-dai da ranar da Nenadi Usman, wadda ita ce shugabar riƙo ta jam'iyyar da wasu manyan jiga-jigai na jam'iyyar suka gudanar da wani taro a Abuja domin yanke hukunci a kan yadda za su ciyar da jam'iyyarsu gaba bayan hukuncin kotun ƙoli da ya cire Julius Abure.

A shekarar 2024 ne, aka zabi Nenadi Usman a matsayin shugabar rikon ƙwarya ta jam'iyyar, a yayin wani taro masu kwmaitin zartar ya gudanar a jihar Abia.

To sai kuma bangaren Abure ya ce bai amince da matakin da taron ya ɗauka ba.

Ita ma jam'iyyar PDP rikicinta na cikin gida na kara ƙamari

 Atiku Abubakar da Nyesom Wike

Asalin hoton, Atiku Abubakar/Nyesom Wike/Facebook

Bayanan hoto, Atiku Abubakar da Nyesom Wike

Rikici makamancin wannan ne ke faruwa a jam'iyyar PDP, inda ita kuma ake tababa a kan muƙamin sakataren jam'iyya na kasa wanɗa kotun koli ta ce batun shugabancin jam'iyya lamari ne na cikin gida a don haka jam'iyya ya kamata ta warware shi.

Ita ma PDP ta rabu guda biyu inda bangare guda ke biyayya ga shugabancin jam'iyyar ɗayan kuma ke biyayya ga bangaren tsohon gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike.

Duk da kasancewar Wike mamba ne a jam'iyyar, ya kuma kasance ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja wanda shugaba Tinubu na jam'iyyar APC ya nada shi.

Hakan ne ya sa mutane ke ganin cewa jam'iyyar ta PDP ta zamo wani bangare na APC.

Olalekan Ige, ya ce rashin kyakkyawan tsarin jam'iyyun adawa a Najeriya, shi ke janyo ba a samun ingantacciyar gwamnati.

Shin zai yiwu a sake samun wata haɗakar jam'iyya?

Nasir El-Rufai

Asalin hoton, Nasir El-Rufai/Facebook

Bayanan hoto, Nasir El-Rufai

A baya-bayannan, Nasir El-Rufa'i, daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya fita daga jam'iyyar tare da komawa jam'iyyar SDP.

Tun bayan komawarsa jam'iyyar, ya ke kokarin hada kan jam'iyyun adawa a kan su zo su hade domin kayar da jam'iyyar APC a zaben shugaban kasa na 2027.

Lekan Ige, ya ce samun nasarar yiwuwar hadewar jam'iyyun ya danganta ne a kan su jiga-jigan 'yan siyasa da za su kasance a majar.

Ya ce ya kamata jam'iyyun adawa su kasnace suna da manufofi masu kyau da tsari ta haka ne kawai za su rika yin nasara a dukkan abubuwan da suka sanya gaba, kuma dole ne jam'iyyun adawa su rinka ajiye bambance-bambancen da kuma son rai a tsakaninsu idan har suna son ci gaba da kuma tsayawa da kafarsu a lokacin zabe.