Me ke faruwa a jam'iyyar NNPP a jihar Kano?

..

Asalin hoton, Kwankwasiyya/Facebook

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ɓarakar da ke cikin jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta fara ɗaukar hankali a siyasar Najeriya, bayan wasu ƙusoshin jam'iyyar, sun yi hannun-riga da tsarin Kwankwasiyya, lamarin da masana suka ce ba abun mamaki ba ne.

Ɗanmajalisar wakilai mai wakiltar Dala, wanda ƙusa ne a jam'iyyar, kuma na gaba-gaba a tsarin Kwankwasiyya, Ali Sani Madakin Gini ya fito a wani faifan bidiyo yana cewa ya fita daga tsagin Kwankwasiyya, inda ya ce, "Daga yau, na daina harkar Kwankwasiyya."

Ali Madaki ya ƙara da cewa, "Kwankwasiyya ƙarya ce, Kwankwasiyya yaudara ce."

Da yake yi wa BBC ƙarin bayani, ya ce, "Na fahimci cewa an gina tafiyar Kwankwasiyya ce kawai domin ci gaban Kwankwaso".

Haka shi ma takwaransa da ke wakiltar ƙananan hukumomin Kibiya da Rano da Bunkure, Hon. Kabiru Alhassan Rurum ya sanar da ficewarsa daga tsarin.

Shi ma Hon. Rurum ya bayyana wa BBC cewa ya fice daga tafiyar ne sakamakon ''rashin adalci'' daga ɓangaren jagoran tafiyar, Rabi'u Kwankwaso.

Sai dai duka ƴan majalisar biyu sun bayyana cewa har yanzu suna nan a jam'iyyarsu ta NNPP, amma ba sa cikin tsarin Kwankwasiyya, wanda ke ƙarƙashin jagorancin Sanata Rabi'u Kwankwaso.

'Abba tsaya da ƙafarka': Daga ina rikicin ya fara?

..

Asalin hoton, Fadar gwamnatin

Duk da cewa an daɗe ana ka-ce-na-ce a tsakanin ƴan jam'iyyar, bayan zaɓen fid-da-gwani na zaɓen ƙananan hukumomi a jihar ne ake tunanin gutsuri tsoma ya fara zafi, inda wasu ke ganin ba a musu adalci ba wajen tsayar da ƴantakara.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A lokacin ne aka fara yaɗa maganar "Abba tsaya da ƙafarka" bayan wasu sun yi zargin cewa ba shi ba ne ya tsayar da ƴantakarar na ƙananan hukumomi.

Bayan fitowar ƙungiyar ce NNPP a Kano ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Kano da wani kwamishina, bisa zarginsu da alaƙa da ƙungiyar, duk da cewa sun musanta lamarin.

A wata ɓarakar daban, a wani rubutu da Ali Madaki ya yi a shafinsa na Facebook, ya sanya hotonsa da na Abdulmumimin Jibrin yana ƙoƙarin sanya masa jar hula, inda ya ce, "Jama’an jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, yau zan faɗa muku, wane ne Abdulmumini Jibrin, wane ne Aliyu Sani Madaki. Tunda ba shi da kunya to yau zan faɗi waye shi da kuma me ya yi mun da Kwankwaso da abun da da ya faɗa mun a kan Ƙwankwaso."

Sai dai Abdulmumini ya mayar da martani, inda ya ce dama asali akwai wasa tsakaninsu, amma kuma a shirye yake idan Madakin Gini ya yi maganar da ya ce zai yi, shi ma a shirye yake ya mayar da martani.

An daɗe ana hasashen su wane ne suka kafa ƙungiyar ta "Abba tsaya da ƙafarka," ba a gane ba, amma a karon farko, ƴan majalisun biyu sun fito sun yaba wa gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, inda suka ce shi mutumin kirki ne tare da shawartarsa da ya yi duk yadda zai yi, ya ''tsaya da ƙafarsa."

Me rikicin yake nufi ga NNPP a Kano?

..

Asalin hoton, Others

A game da wannan, Farfesa Kamilu Sani Fagge, na Jami'ar Bayero ta Kano ya ce rashin bin tsarin dimokuraɗiyya ce matsalar.

"Rikicin da ke faruwa a jam’iyyar NNPP a Kano samuwarsa ba abin mamaki ba ne saboda batun dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyar, ba shi da tasiri sosai. Shi jagoran jam’iyyar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana ganin yana da ƙarfin da shi zai ɗora, shi zai sauke. Kuma duk inda aka samu wannan, za ka ga an fara samun bambanci musamman waɗanda suke ganin ba a musu adalci ba," in ji Farfesa Fage.

Duk rikice-rikicen irin wannan ba sa rasa nasaba da lissafe-lissafen siyasa, wanda hakan ya sa aka fara tunanin ko wannan sabon rikicin zai iya yi wa jam'iyyar barazana.

Farfesa Fage ya ƙara da cewa, "Ai ba ma ita ba, duk jam’iyyar da ta shiga zaɓe tana rigima, yana mata illa. Abin da ya gurgunta PDP ke nan. Kuma Hausawa na cewa abin da ya ci doma, ba zai bar awe ba. Don haka NNPP muddin ba ta warware wannan matsalar ba, za ta samu matsala, ba ma a Kano ba, har da ƙasar baki ɗaya. Yanzu ga masu cewa Abba ya tsaya da ƙafarsa, ga wasu rigingimun kuma, yanzu haka wasu na cewa Kwankwaso ya bar wa wanda ya kafa jam’iyyar jagorancinta."

A game da masu cewa Kwankwaso yana taimakon Abba ne, Fagge ya ce ba haka ba ne, "ai gwamna aka zaɓa, duk da ƙarƙashin jam’iyya aka zaɓe shi, amma kamata ya yi Kwankwaso ya bar shi ya yi aikinsa. Zai iya ba shi shawara, amma a fito a ce za a mayar da shi sai yadda aka juya shi, wannan ne zai haifar da rigima. Sannan duk da wannan rigima ce ta cikin gida."

Ko Abba zai iya rabuwa da Kwankwaso?

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabir/Facebook

Abin da ke jawo muhawara a game da wannan rikicin shi ne shin gwamna Abba zai iya rabuwa da Kwankwaso domin ya 'tsaya da ƙafarsa'?

A game da wannan ne Farfesa Fagge ya ce a yanzu zai yi wahala a raba tsakanin Abba da Kwankwanso.

"Amma idan tafiya ta yi tafiya, idan kuma ba a canja salon tafiyar aka yi ba, za a iya samun farraƙa tsakanin su kamar yadda aka samu tsakanin Kwankwaso da Ganduje.

Duk inda ka samu samu ubangida da yaronsa, idan shi ubangidan ya dage sai ya juya akalar yaron, da zarar yaron ya ɗare kujerar mulki, to giyar mulki za ta sa shi ya fara ƙin yarda, sannan wannan zai bayar da wata kafa a samu wasu su su shiga tsakani su riƙa assasa rigimar."

Da aka tambayi farfesan me ya kamata gwamna ya yi idan an samu irin wannan saɓanin, sai ya ce zama ya kamata a yi, sannan a sa hidimtawa al'umma a gaba da komai ba wani ya ce dole sai an bi abin da yake so ba.