Me ya janyo rarrabuwar kai a jam'iyyar Labour Party ta Najeriya?

...

Asalin hoton, FB/Multiple

Lokacin karatu: Minti 3

Daya daga cikin manyan jam'iyyun adawa a Najeriya wato Labour Party, ta faɗa halin ƙaƙa-ni-ka-yi duk da hukuncin kotun ƙoli na baya-bayan nan, wanda aka shigar domin warware rikicin shugabanci da ke addabar jam'iyyar.

Rikicin dai ya kaure ne tsakanin shugabancin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure da kuma ɗaya ɓangaren wanda ya ayyana Nenadi Usman a matsayin shugabar riƙo.

Kowane ɓangare na iƙirarin shi ne sahihi.

Jam'iyyar Labour ta shiga rikicin ne, bayan rasuwar shugabanta na kasa, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam a shekara ta 2020.

Inda ake ta sabata juyata tsakanin masu goyon bayan shugabancin Julius Abure da masu ganin ya zama wajibi a sake lalen shugabancin bayan karewa wa'adin shugabancin nasa.

Sai dai a hukuncin da kotun ƙolin Najeriya ta yanke, ta soke hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wadda ta amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.

Kotun ta ce babu wata kotu da take da ƴancin tsoma baki a rikicin shugabancin jam'iyya, kasancewar "lamari ne na cikin gida."

Ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen shugaban Najeriya na 2023, Peter Obi ya karkata ne ga ɓangaren da ya amince da Nenadi Usman a matsayin shugabar riƙo.

A watan Satumban 2024 ne ɓangaren nasu ya naɗa ta kan muƙamin bayan wani taro da ya gudanar.

Julius Abure ya yi fatali da taron da kuma naɗin da aka yi wa Nenadi.

Haka nan kuma bayan kimanin wata ɗaya da naɗin ne kotu ta amince da shugabancin Julius Abure.

Yanzu dai lamarin ya sake rincaɓewa tun bayan da kotun ƙoli ta yanke hukuncin cewa kotu ba za ta tsoma baki a rikicin jam'iyyar ba.

Dukkanin ɓangarorin biyu na iƙirarin cewa su ne kotu ta bai wa gaskiya.

Nenadi Usman da Abure

Asalin hoton, Nenadi Usman/X/Labour Party Nigeria

'Za mu kori Peter Obi'

Ɓangaren jam'iyyar LP ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta yi barazanar korar "duk wanda ke yi wa jam'iyyar zagon kasa a cikin gida".

Ɓangaren ya ambato mutane kamar gwamnan jihar Abia, Alex Otti da kuma dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 na jam'iyyar Peter Obi a cikin waɗanda matakin zai iya shafa.

Umar Farouk Ibrahim, wanda shi ne sakataren jam'iyyar ɓangaren Julius Abure, ya shaida wa BBC cewa suna sane da "yadda wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar ke kokarin yi wa jam'iyyar zagon kasa domin suna ganin yadda suke kai komo a wasu jam'iyyun adawa."

Ya ce, "Kowa ya riga ya sani cewa gwamnan jihar Abia Alex Otti da kuma Peter Obi, ba sa tare da shugabancin jam'iyyar domin hakan ne ya sa suka garzaya kotu suka kai kara kan cewa ba su yarda da shugabancin jam'iyya ba," in ji Farouk Ibrahim.

'Shure-shure ba ya hana mutuwa'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai kuma a nasu bangaren wadanda aka yi wa barazanar dakatar da su daga jam'iyyar ta Labour sun ce wannan abu da bangaren Julius Abure suke duk shure-shure ne.

Muhammad Ndimi Abdullahi, Daya ne daga cikin 'yan'yan jam'iyyar Labour da ke bangaren su Peter Obi, ya shaida wa BBC cewa duk abin da bangaren su Abure da jama'arsa ke faɗa "shaci fadi ne kawai."

"Mu abin da muka sani cewa shugabancin jam'iyya na karkashin gwamnan Abia da mataimakinsa da 'yan majalisunmu na tarayya da jam'iyyar Labour da mambobin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, wadannan a yanzu suke da hurumi da dama a jam'iyyarmu ta Labour.

"Shi Abure a yanzu wa'adin shugabancinsa a jam'iyya ya kare tuntuni dama an zabe shi ne a kan zai yi shekara guda, to ya gama, amma kuma ba ya son barin mukamin, shi ya sa yanzu yake kawo rudani saboda ba ya son tafiya, ita kuma jam'iyya ba harka ce ta ra'ayi ba, harka ce ta cikin gida. Muna da masu fada a ji don haka su ne ke da wuka da nama na su zabi wadanda za su ja ragamar jam'iyya." In ji Muhammad Ndimi Abdullahi.

Wasu 'yan jam'iyyar dai sun yabawa da hukuncin na kotun kolin inda suka ce an yi adalci, wasu kuma na cewa hukuncin na bukatar fassarar da ta dace daga masana.