Dalilan da suka jefa PDP da LP rikicin cikin gida

Atiku Abubakar da Peter Obi

Asalin hoton, PDP/LP

Bayanan hoto, Atiku Abubakar na PDP (hagu) da Peter Obi na LP na fama da rikicin cikin gida a jam'iyyun adawa nmafiya girma a Najeriya
    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Duk da cewa rikici a jam'iyyun siyasa na adawa a Najeriya ba sabon abu ba ne, ba a saba ganin manyan jam'iyyun adawar a rikicin ba lokaci guda kamar yadda LP da PDP ke ciki a yanzu.

Lamarin ya yi ƙamarin da a yanzu PDP - wadda ita ce babbar mai adawa - ta kasu gida-gida, inda manyan jiga-jigan jam'iyyar ke da ɓangarori.

Jam'iyyar Labour ma, naɗa Sanata Nenadi Usman da aka yi a matsayin sabuwar shugabar jam'iyyar ranar Laraba ya bar baya da gagarumar ƙura, inda har sakataren yaɗa labaran jam'iyyar ya ce taron nadin nata ya saɓa wa dokar jam'iyyar.

Rikicin baya-bayan nan a PDP ya fara ne tun kafin babban zaɓe na 2023 lokacin da tsohon Gwamnan Rivers Nyesom Wike ya ja daga da Atiku Abubakar, yayin da Labour ta shiga nata kan rikicin shugabanci.

Da ma rikici a jam'iyya maras mulki a Najeriya ya zama al'ada, yayin da masu sharhi ke cewa ɗaya daga cikin dalilan faruwar hakan har da rashin mulki a hannu.

Masharhanta na ganin rikicin cikin gida da ya dabaibaye manyan jam'iyyun adawar, wata riba ce ga jam'iyyar APC mai mulki, kuma jam'iyyun ba su shirya ƙwatar mulki ba.

PDP ce ta zo ta biyu a zaɓen shugaban ƙasa da Atiku Abubakar ya yi mata takara, sai kuma Peter Obi da ya zo na uku a jam'iyyar Labour, inda aka bayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya yi nasara.

Gidajen PDP uku

Taron PDP

Asalin hoton, PDP

Bayanan hoto, Ministan Abuja Nyesom Wike (hagu) kenan tare da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Namadi Sambo (tsakiya) da kuma Atiku Abubakar yayin wani taron PDP a Abuja a watan Afrilun 2024

Tun watan Maris na 2023 - lokacin da kwamatin zartarwa na PDP ya naɗa Iliya Umar Damagun a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa a matakin riƙo - rikicin PDP ya sake sauya salo.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kwamatin ya ɗauki matakin ne bayan wata babbar kotu ta bai wa Iyorchia Ayu umarnin daina bayyana kansa a matsayin zaɓaɓɓen shugaban jam'iyyar, abin da bai yi wa ɓangaren Atiku Abubakar daɗi ba.

Wasu 'yan jam'iyyar na zargin Damagun da yi wa tsohon gwamna kuma ministan Abuja, Nyesom Wike, biyayya, zargin da ya sha musantawa. Sai dai har yanzu suna ci gaba da kiran ya sauka daga muƙaminsa.

A gefe guda kuma, sauran gwamnonin PDP irinsu Bala Mohammed na Bauchi na ganin ba rikcinsu ba ne, kuma ba su mara wa kowane ɓangare baya.

"Ɓangaren Atiku ba su son ya ci gaba da mulki saboda ba shi tare da su, ɓangaren gwamnan Bauchi kuma 'yan ba-ruwanmu ne, su kuma ɓangaren Wike sun fi son a bar Damagun domin ya yi musu yadda suke so," a cewar Kwamared Imrana Nas, wani shahararren ɗan jam'iyyar.

Sai dai ɗaya daga cikin masu magana da yawun jam'iyyar, Ibrahim Abdullahi, ya musanta zargin cewa Damagun na biyayya ne ga Wike.

"Tsakani da Allah ba haka ba ne. Yanzu an kafa kwamati biyu na horarwa da na sulhu, kuma idan aka samu wani da laifi - ciki har da Wike - za a hukunta shi," in ji shi.

Kamar wata huɗu da suka wuce aka yi taro kuma aka sake jaddada wa Damagun muƙaminsa bayan taron jam'iyyar na ƙasa ya gaza yanke shawarar bai wa wani muƙamin.

A farkon makon nan ma ministan na Abuja, wanda ya karɓi muƙamin minista duk da yana jam'iyyar adawa, ya yi barazanar yaƙar gwamnonin jam'iyyar bayan sun zarge shi da kankane al'amura.

Wike ya fara adawa ne tun lokacin da Atiku Abubakar ya kayar da shi a zaɓen neman tikitin takarar shugaban ƙasa, bayan was 'yantakara sun janye wa abokin takararsa waɗanda ya zarga cewa ba su tsinana wa jam'iyyar komai ba.

Ya zuwa yanzu, rikicin nasu ya raba jam'iyyar uku zuwa ɓangaren Atiku, da gwamnoni, da kuma Wike.

Rikcin shugabanci a LP ya ɗauki sabon salo

Peter Obi

Asalin hoton, LP

Bayanan hoto, Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a zaɓen 2023 Peter Obi kenan yake jawabi yayin wani taro a watan Yunin 2024

A ranar Laraba ne kwamatin zartarwa na ƙasa na Labour Party (LP) ya sanar tsohuwar ministar kuɗi, Sanata Nenadi Usman, a matsayin shugabar kwamatin riƙo da zai jagoranci jam'iyyar.

Matakin ya biyo bayan taron da jagororin jam'iyyar suka yi a jihar Abia, abin da ke nufin sun ƙwace shugabancin daga hannun Julius Abure.

Sai dai ƙasa da kwana ɗaya sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Obiora Ifoh, ya fitar da sanarwa cewa taron da ya zaɓi Nenadi haramtacce ne a ƙarƙashin dokokin jam'iyyar tasu.

"Taron na da aka yi a Umuahia wasa ne kawai da ɓata lokaci," in ji shi. "Da ma akwai shugabanci a jam'iyyarmu. Saboda haka kwamatin riƙo da aka ce an kafa ya saɓa wa kundin mulkin jam'iyya."

Ya haƙiƙance cewa har yanzu Abure ne shugaban jam'iyyar "saboda shi ne aka zaɓa a babban taron jam'iyya na ƙasa da aka yi a jihar Anambra a watan Maris da ya gabata".

Kwamatin zartarwar ya bai wa kwamatin riƙon kwana 90 domin ya gudanar da zaɓuka a duka mazaɓu da ƙananan hukumomi da ke fadin jihohi 36 na ƙasa, waɗanda za su share fagen gudanar da babban taro na ƙasa kuma a zaɓi sababbin shugabanni.

Rahotonni na cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da ke da faɗa a ji a jam'iyyar ce ta nua rashin amincewa da shugabancin Abure, abin da ya kai ga rushe shugabancinsa.

Sai dai babu tabbas ko ɓangaren da ke jayayyar zai amince da zaɓukan.

'Rigima ce ta neman iko'

Husuma da rikici a jam'iyyun adawar Najeriya sun zama kamar ɗabi'a ko kuma al'ada, a cewar Farfesa Abubakar Kari, masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Abuja.

Misali, an shekara sama da 20 ana rikici a jam'iyyar APGA, wadda ba ta taɓa cin zaɓen shugaban ƙasa ba kuma ta fi ƙarfi a kudu maso gabashin ƙasar.

Farfesa ya ce duka dalilan da ke jawo rikicin ba su wuce kokawar neman iko.

"Saboda hakan ne zai ba su damar yin takara, ya ba su damar ɗora irin mutanen da suke so, su dai juya jam'iyyar yadda suka ga dama," a cewarsa.

Shi ma Farfesa Kamilu Fagge na Jami'ar Bayero ta Kano ya amince da wannan ra'ayi, yana mai cewa ba a gina jam'iyyun a kan aƙida ba.

"Ba a gina jam'iyyun a kan wata aƙida ba, kawai mutane ne suka zo da buƙatunsu daban-daban. Saboda haka, idan buƙatar wani ba ta biya ba sai ya ja daga a cikin tafiyar," kamar yadda ya shaida wa BBC.