Jam'iyyun adawa na kara kaimi wajen neman wanda zai kalubalanci Tinubu a 2027

Asalin hoton, Atiku Abubakar PIX
Ga dukkan alamu ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin Jagororin jam'iyyun hammaya na PDP da Labour Party don yin kama -kama wajen kawo ƙarshen gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 da ke tafe.
Bayanai na nuna cewa tattaunawar na ci gaba da karfi tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasar Atiku Abubakar na PDP da kuma Peter Obi na jam'iyyar Labour don ganin sun haɗe wuri guda don aiki tare.
A wata hira da aka yi da dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi a baya baya nan ya ce ceto Najeriya daga halin da take ciki shi ne babban abinda yake fatan za su yi aiki tare domin ganin hakan ta tabbata, ba wai batun kashin kansa na zama shugaban Najeriya ba
Mista Obi ya kuma yabawa Atiku Abubakar bisa wasu kalamai da aka ruwaito ya yi a baya baya nan da ke nuna alamun amincewarsa kan tattaunawar domin hadin kai da zimmar tunkarar shugaba Tinubu na jam'iyyar APC mai Mulki a zaben 2027 da ke tafe.
Dr Tanko Yunusa mai magana da yawun jam'iyyar ta Labour ya shaida wa BBC cewa fatansu shi ne su hada kai domin su cimma nasara
‘’Muna tunanin idan muka zauna da juna, mu ka hada karfi da karfe, watakila mu cimma nasara’’, in ji shi.
Dr Yunusa ya ce a halin yanzu jiga-jigan jam'iyyun biyu na tattaunawa wajan neman wanda ya cancanta:
''Maganar cewa wanene zai yi shugabanci ba ta taso ba amma muna tunani tsakaninmu ya kamata mu nemi wanda ya cancanta wanda ya ke da jini a jika wanda zai iya wannan aiki'', in ji shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma bangaren tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023 Atiku Abubakar ya jadada bukatar ganin cewa jam'iyyun hammaya sun hade domin tunkarar jam'iyyar APC a zaben da ke tafe.
Mai Magana da yawun tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Abdulrashid Shehu Uba Sharada ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta haifar da matsaloli ga alummar kasar kuma wannan batu na hadaka ya wuce na jita-jita:
''Duka wadanan jagorori idan ka lura za ka ga cewa suna magana ne kusan bakinsu daya. Dan har shi jagoran Labour Party Peter Obi ya zo ya tattauna da wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar kan wadannan batutuwa da kuma yadda za a samu maslaha tare da hadin kai domin fuskantar alamuran da ke gabanmu na zabe da kuma Sauron matsaloli da suka shafi alumma'', in ji shi.
Wannan ba shi ne karon farko da wasu bangarori suka yunkuro domin su yi aiki tare a siyasar Najeriya ba.
Sai dai wani batu da ke kawo mu su cikas shi ne na ajiye bukatun kashin kai domin marawa daya daga cikinsu baya a matsayin dan takara.
A baya gabanin zaben 2023 jam'iyyar Labour ta Peter Obi da kuma jam'iyyar NNPP ta tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun yi kokarin hadewa amma daga bisani maganar ta watse saboda rashin amincewa akan wanda za a marawa baya.














