Hujjojin kotun ƙoli na yin watsi da ƙarar Atiku da Obi kan nasarar Tinubu

..

Asalin hoton, facebook/Atiku Abubakar, Peter Obi

Kotun ƙolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Hukuncin na alƙalai bakwai ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Inyang Okoro, ya ce “A ƙashe, bayan warware duk wasu lamurra game da ɗaukaka ƙarar, zan iya cewa babu hujjoji masu ƙwari game da ɗaukaka ƙarar, saboda haka an yi watsi da ita,”

“Hukuncin kotu ta baya da aka zartar ranar 6 ga watan Satumba, da ya tabbatar da nasarar wanda ake ƙara na biyu a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Najeriya, an tabbatar da shi.”

Wannan dai ya kawo ƙarshen duk wata turka-turka game da batun nasarar da shugaban na Najeriya ya samu, a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Kotun ta bayyana haka ne a hukuncinta na ranar Alhamis, bayan ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyun adawa suka ɗaukaka kan hukuncin kotun ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, FADAR SHUGABAN NAJERIYA

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu

Dalilan da kotu ta bayar

- Tun daga farko kotun ta fara ne da yin watsi da buƙatar Atiku Abubakar ta gabatar da sabbin hujjoji gaban kotun kan ƙalubalantar Tinubu.

Mai shari’a Okoro ya ce kotun ba ta da hurumin karɓar sabuwar hujja kuma buƙatar ta saɓa wa dokar zaɓe.

Ya ce “Babu wani gyara a doka da aka samu wanda zai halasta wa kotun karɓar sabbin hujjoji kamar yadda yake a sashe na 132(7) na dokar zaɓe.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuma ya ce kotun ba za ta iya yin amfani da damar sashe na 22 na kotun ƙoli ba kan batun karɓar sabbin hujjoji ba domin kuwa babu wata shaɗara da ta ambaci batun amfani da takardar bogi a ainihin ƙorafin da aka shigar tun farko.

- Game da batun rashin sanya sakamakon zaɓe a shafin intanet na IreV, kotun ƙoli ta ce wannan ba hujja ce da za ta sanya a soke zaɓen na ranar 25 ga watan Fabarairu ba.

Alƙalin kotun ya ce dokar zaɓe ta bai wa hukumar INEC damar hanyar da za ta yi amfani da ita wajen fitar da sakamakon zaɓe.

Ya ƙara da cewa rashin sanya sakamakon a shafin intanet na IreV bai shafi sakamakon zaɓen ba.

- Dangane da batun wajibcin samun kashi 25% na ƙuri’un da aka kaɗa a Yankin Babban Birnin Tarayya kuwa, nan ma kutun ta amince da hukuncin kotun sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa, wadda ta ce ba dole ne sai ɗan takarar shugaban ƙasa ya samu kashi 25% na ƙuri’un da aka kaɗa a yankin Abuja ba kafin a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara.

Mai shari’a Iyang Okoro ya ce Yankin birnin tarayya ba ya da banbancin matsayi idan aka kwatanta da sauran jihohin ƙasar.

Tun farko alƙalan kotun sun yi watsi da buƙatar Atiku, ta neman gabatar da ƙarin hujjoji kan cewa Tinubu ya gabatar wa hukumar zaɓe ta INEC takardar kammala karatu ta bogi gabanin zaɓen shugaban ƙasa.

Atiku ya yi iƙirarin cewa takardun da Tinubu ya gabatar daga Jami’ar Jihar Chicago ta Amurka ba sahihai ba ne, sai dai bai samu gabatar da sabbin hujjojin nasa ba.

A ranar 6 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa da ta yi zamanta a birnin Abuja, ta yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar suna ƙalubalantar zaɓen Shugaba Tinubu.

Sai dai rashin gamsuwa da hukuncin ya sa manyan jam’iyyun adawan da ƴan takaransu suka ɗaukaka ƙara zuwa kotun ƙoli.

A lokacin ɗaukaka ƙarar, Atiku ya bijiro da sabbin tuhume-tuhume guda 35, da ke sukar hukuncin da kotun farko ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani ta yanke.

Alƙalan da suka yanke hukuncin

  • Mai shari'a John Inyang Okoro
  • Mai shari'a Uwani Musa Abba-Aji
  • Mai shari'a Mohammed Lawal Garba
  • Mai shari'a Ibrahim Saulawa
  • Mai shari'a Adamu Jauro
  • Mai shari'a Tijjani Abubakar
  • Mai shari'a Emmanuel Agim

Masharhanta na cewa matakin ƙalubalantar zaɓen shugaban ƙasa bai taɓa samun nasara a kotun Najeriya ba, ƙasar da ta koma tafarkin dimokraɗiyya a 1999, da kuma tarihin maguɗin zaɓe.