Jami'ar Chicago ta fitar da takardun karatun Tinubu

fg

Jami'ar Jihar Chicago da ke Amurka ta fitar da takardun karatun Shugaba Bola Tinubu, bayan da ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubukar ya buƙaci hakan.

A ƙarshen makon da ya gabata ne, wata kotun gunduma da ke arewacin Illinois a Amurka ta bayar da umarnin a saki takardun karatun Tinubu ga Atiku.

A wani martani na buƙatar da Atiku ya miƙa a karo na uku, wanda ya nemi a saki kwafin sakamakon digirin 1977, Jami'ar ta ce takardun sun yi daidai da na Tinubu da ke ɗauke da kwanan watan 27 ga watan Yunin 1977.

"Bayan bincike mai zurfi, Jami'ar CSU ta gano kuma ta gabatar da takardun da aka nema, sannan ta gabatar da su don amsa wannan buƙata. Lambobin takardun su ne CSUO008 zuwa CSU0010.

"An shafe sunayen ɗaliban da ke kan takardun, saboda a sakaya sunayensu.

"CSU za kuma ta saki sakamakon ɗaliban da ke kusa da shi, masu lamba CSU0011 da lamba 0017 na wasu ɗaliban, bayan an shafe sunayen (saboda sakayawa)”.

"Waɗannan takardun sun yi daidai da yadda na Tinubu, dalibin da aka yi wa sauyin makaranta yake," kamar yadda jami'ar ta rubuta.

A baya Tinubu ya yi iƙirarin ɓatan ainihin takardunsa na jami'ar, abin da ya sa ya gabatarwa da hukumar zaɓe INEC wata takardar a matsayin madadin takardun na ainihi domin takarar shugabancin Najeriya a 2023.

Takardu da dama na waɗari a kafafen sada zumunta a matsayin shaidar kammala karatun na Tinubu a Jami'ar Jihar Chicago.

Tambari da kuma bajon da jami'ar CSU ta saki na takardun digirin a 1977 sun yi daidai da irin waɗanda Shugaba Tinubu ya gabatar wa INEC, sai dai an samu bambanci a kwanan wata.

Amma cikin bayanin da jami'ar ta yi, ta ɗauki alhakin kuskuren da aka samu a kwanan watan, tana cewa kuskure aka samu wajen rubutawa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar 19 ga watan Satumba ne, Jeffrey Gilbert na kotun majitare da ke Amurka ya amince da buƙatar da aka shigar gaban kotun tare da ba da umarnin sakin takardun karatun Bola Tinubu cikin sa'a 24.

A wani ƙoƙari na ganin haka bai faru ba, Tinubu ya ɗaukaka ƙara kan wannan umarni.

Nancy Maldonado ta kotun tarayya ta sake tabbatar da wannan hukunci da Tinubu ya so ƙalubalanta, inda ita ma ta ce a saki takardun.

Domin bin umarnin kotun da biyan buƙatar Atiku Abubakar, CSU ta ce ba za ta iya nemo ainihin kwafin takardun da ta bai wa Tinubu ba a 1979.

"A tsarin CSU ba ta ajiye kwafin takardun ɗaliban da suka yi digiri, kuma bayan dogon bincike ta gaza samo kwafin irin wanda ta bai wa Tinubu a 1979, don haka ba a samu takardun da aka buƙata ba," in ji jami'ar.

Sai dai jami'ar ta saki takardun wasu ɗaliban da ta rufe sunayensu, waɗanda suka yi daidai da na Tinubu domin tabbatar da cewa ya kammala makarantar a baya.

Atiku Abubakar dai na son amfani da takardun ne a matsayin shaida a kotun ƙolin Najeriya kan ƙorafin da ya shigar game da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na watan Fabrairun 2023.