Kotu ta ayyana Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano

Asalin hoton, Abubakar Musa DK
Kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano ta soke nasarar Abba Kabir Yusuf, a matsayin halastaccen gwamna.
Haka zalika, ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya ci zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris ɗin 2023.
Jam'iyyar APC ce ta shigar da ƙara a gaban kotun, tana ƙalubalantar nasarar Abba Kabir.
Kotun ta bayyana wannan hukunci na ranar Laraba ne, ta hanyar manhajar Zoom, cikin wani tsattsauran yanayin matakin tsaro a birnin Kano.
Mai shari'a Oluyemi Akintan-Osadebay, ita ce shugabar kotun wadda ta jagoranci alƙalan kotun guda uku.
Kotun ta ce ta yanke wannan hukunci ne bisa hujjar cewa an yi aringizon ƙuri'u har 165,633, waɗanda aka gano ba su da sitamfi da kuma kwanan wata a cikin ƙurin Abba Kabir.
Tun farko a watan Maris ɗin 2023, hukumar zaɓen ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen ne da ratar ƙuri'a 128,900.
Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri'u mafi rinjaye da suka kai 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye da shi, ya samu ƙuri'a 890,705.
Alƙalan kotun sun umarci hukumar zaɓe ta INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf, tare da gabatar da ita ga Nasiru Yusuf Gawuna.
Lauyan jam'iyyar NNPP, Bashir Muhammad Tudun Wuzirci bayan fitowa daga kotun, ya ce hukuncin ya zo musu da mamaki, wanda in ji shi bai kamata a ce an yi haka ba.
Ya ce amma akwai kotuna na gaba, kuma suna tabbatar da cewa idan sun je gaba, za su warware abin da ya kira "wannan surkullen da aka wanda bai kamata a yi ba".
A cewarsa, ko da wasa ba su yarda wannan hukunci ba, don haka za su yi shawara da mutanen da suke wakilta "kuma in Allah ya yarda za mu ɗau mataki".
Barista Bashir Tudun Wuzirci ya ce irin haka ta faru a jihar Osun, amma kotun ɗaukaka ƙara ta zo ta warware kuma Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa abin da tirabunal ta yi ba daidai ba ne.
Dalilan APC na shigar da ƙara
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin ɓangarorin da jam'iyyar APC ta kai ƙara gaban kotu, har da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ɗan takarar da aka ayyana a matsayin wanda ya ci zaɓen gwamnan Kano, da kuma jam'iyyarsa ta NNPP.
Ta ce Abba Gida-Gida, bai ci zaɓen gwamnan Kano da halastattun ƙuri'u ba.
Mashawarcin jam'iyyar a Kano kan harkokin shari'a, Barista Abdullahi Adamu Fagge, kuma ɗaya daga cikin lauyoyin da ke wakiltar jam'iyyar, cikin wata hira da BBC ya ce sun nemi kotu ta ayyana ɗan takarar jam'iyyarsu na APC, matsayin wanda yake da rinjayen halastattun ƙuri'u.
Haka kuma wani ƙarin ƙorafin da APC ke da shi, kamar yadda lauytan ya ce, shi ne wanda aka ayyana cewa ya ci zaɓe na NNPP, sunansa ba ya cikin rijistar jam'iyyar NNPP.
Sannan Jam'iyyar NNPP ba ta gudanar da zaɓen fitar da gwani ga masu neman takara, kafin zaɓen gwamnan Kano ba.
Lauyan ya ce "waɗannan suna cikin dalilai da suka sa muka shigar da ƙara gaban kotu, muna ƙalubalantar zaɓen gwamnan Kano", kamar yadda lauyan ya bayyana.
Gargaɗin 'Yan sanda

Asalin hoton, Abdullahi haruna Kiyawa/Facebook
Tun a ranar Talata, kwana daya gananin yanke hukuncin ne rundunar 'yan sanda reshen jihar Kano ta gargaɗi al'ummar jihar kan tayar da zaune-tsaye gabanin hukuncin na ranar Alhamis.
Haka nan rundunar tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun gudanar da wani sintiri a sassan birnin jihar don nuna ƙarfin da suke da shi wajen tunkarar abin da rundunar 'yan sanda ta kira "kowacce irin barazana".
An ga kwambar motocin haɗin gwiwar jami'an tsaro da suka haɗa da 'yan sanda da sojoji da kuma sauran jami'ai masu kayan sarki yayin wannan sintiri da suka zagaya sassan birnin.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Hussain Muhammad Gumel ya shaida wa BBC cewa sun yi tsare-tsare don tabbatar da ganin ba a samu asarar rai ko dukiya ko kuma cin zarafin wani mutum ba, bayan sanar da hukuncin kotun.
Rundunar ta ce ta jibge isassun jami'an tsaro da kayan aiki zuwa wuraren da ta kira 'muhimmai a Kano' don tabbatar da tsaron rayuka da na dukiya.
Hukuncin dai ka iya zama zakaran gwajin-dafi ga duka jam’iyyun biyu waɗanda suka shafe makonni suna addu’o’in fatan samun nasara a hukuncin.










