Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Tinubu/Facebook
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa ta tabbatar da nasarar zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Shugaban kotun, Mai shari'a Haruna Tsammani ya ce matakin hukumar zaɓe na ayyana Bola Tinubu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen 25 ga watan Fabrairu, ya dace.
Matakin na zuwa ne bayan kotun ta kori ƙarar ɗan takarar shugaban ƙasa na babbar jam'iyyar adawar Najeriya, Atiku Abubakar da maryacen Laraba.
Shi, da Peter Obi na jam'iyyar Labour da kuma jam'iyyar APM, sun nemi kotun ta soke nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaɓen Fabrairu.
Sai dai, ba a ga 'yan adawa irinsu Atiku da Peter Obi a zaman kotun na ranar Laraba ba, yayin da manyan jami'an gwamnati ciki har da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka shafe tsawon wuni suna sauraron hukuncin kotun.
Da farko, kotun ta yi watsi da ƙarar Peter Obi na jam'iyyar LP da ta jam'iyyar APM.
Ta kuma ce duk ƙararrakin, waɗanda aka shigar don neman a soke cancantar zaɓen Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima, ba su da tushe.
Alƙalan kotun biyar wajen gabatar da hukuncin, wanda suka shafe tsawon wunin ranar Laraba, suna gabatarwa.
Sun riƙa karɓa-karɓa wajen yin bita da karanta hujjoji, tare da tsefe bayanai, kafin bayyana matsayarsu a kan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar.
Tinubu ya yi maraba da hukuncin
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tuni fadar shugaban Najeriya ta fitar da sanarwa, inda ta ce Shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin kotun cike da tsananin sanin nauyin da ke kansa, da kuma shirin hidimtawa dukkan al'ummar Najeriya.
Shugaban na Najeriya ya kuma bai wa al'ummar Najeriya tabbacin mayar da hankali wajen cika ƙudurinsa na samar da ƙasa mai haɗin kai da zaman lafiya da bunƙasar arziƙi.
Tinubu ya kuma ce ya yaba wa tsayin daka da jajircewar bin diddigin komai da kuma ƙwarewa daga alƙalan kotun biyar a ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Haruna Tsammani ga fashin baƙin doka.
Tinubu ya ce ya yi imani cewa 'yan takarar shugaban ƙasa da jam'iyyun siyasar da suka yi amfani da 'yancin da doka ta ba su dama wajen shiga babban zaɓen da kuma bin tafarkin zuwa kotu, sun tabbatar da matsayin bin tafarkin dimokraɗiyyar Najeriya.
Ya kuma buƙaci su zaburar da magoya bayansu wajen yin amanna da aƙidar kishin ƙasa, ta hanyar mara wa gwamnatinsa baya don bunƙasa rayuwar duk 'yan Najeriya.
Atiku bai gabatar da shaidun da suka dace ba - Kotu
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen dai ta yi watsi da ƙorafin Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP da neman a soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa a jihohin Kano da Lagos.
Ta ce masu ƙorafin ba su shigar da Peter Obi da Sanata Rabiu Kwankwaso ba a ƙararsu, duk da yake su ne suka ci mafi rinjayen ƙuri'un da aka kaɗa a jihohin biyu.
Haka kuma ta kori bahasin ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar wanda ya zargi Bola Tinubu da mallakar takardun shaidar ɗan ƙasa biyu wato Najeriya da ƙasar Guinea
Sannan ta yi watsi da iƙirarin cewa kotu ta taɓa kama Tinubu da laifin safarar ƙwaya a Amurka.
Ma shari'a Tsammani ya buga misali da shaidar da ayarin lauyoyin Tinubu ya gabatar na wata wasiƙa daga ofishin jakadancin Amurka da ke tabbatar da rashin tarihin aikata laifi na Tinubu a Amurka.

Asalin hoton, COURT OF APPEAL/X
Babu hujja kan iƙirarin aringizon ƙuri'u - Kotu
Mai shari'a Tsammani ya ce kotun ta ƙi amincewa da iƙirarin masu ƙorafi na cewa an yi aringizon ƙuri'u a jihohi irinsu Yobe da Oyo da Kano da sauransu, saboda ba su gabatar da bayani a kan tasoshin zaɓen da al'amarin ya faru ba.
"Hankali ba zai ɗauka ba cewa, mai ƙorafi ya yi zargin maguɗi a wurare masu yawa cikin tasoshin zaɓe 176,000 da mazaɓu sama da 8000 na ƙananan hukumomi 774 a cikin jiha 36 da kuma Abuja, amma ba tare da ya zayyana taƙamaimai wuraren da aka yi maguɗin da ya yi zargi ba," kotun ta ce.
Hukuncin ya kuma ce jam'iyyar LP ta gaza kafa hujja kan iƙirarin da ta yi, na samun kura-kurai a zaɓen watan Fabrairu.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa hukumar zaɓe ta INEC ta rage mata ƙuri'un da ta ci, inda ta ƙara a kan ƙuri'un jam'iyyar APC, sai dai a cewar kotun, jam'iyyar LP ta gaza gabatar da cikakken bayani a kan haƙiƙanin yawan ƙuri'un da ta ci, kafin a rage mata su, kamar yadda ta yi iƙirari, kuma ba su iya ba da bayani a kan tashoshin zaɓen da hakan ta faru ba.
Sai dai, kotun ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ba ta da hurumin ƙalubalantar matsayin Peter Obi na kasancewarsa, ɗan jam'iyyar LP.
APC da Bola Tinubu a cikin ƙorafe-ƙorafensu sun ce babu sunan Obi a rijistar jam'iyyar LP, da aka gabatar wa hukumar zaɓe ranar 25 ga watan Afrilun 2022, abin da suka ce ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.
Kotun ta ce ba ta amince da ƙorafin da jam'iyyar LP ta yi na cewa an taɓa tuhumar Bola Tinubu a kan safarar ƙwaya a Amurka ba.
Kuma Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima sun cancanci tsaya wa takara a zaɓen watan Fabrairu.
Mai shari'a Haruna Tsammani ya ce kotun ta kori ƙorafin da Peter Obi da jam'iyyar LP na cewa sai ɗan takara ya samu kashi 25 cikin 100, kafin a ayyana cewa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa. Kotun ta ce mazaunan Abuja, ba su da wata alfarma ta musamman kamar yadda masu ƙorafin suka yi iƙirari.
Kotun ta kori ƙarar jam'iyyar APM
Tun faro, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya, ta yi watsi da ƙarar da ke neman a soke cancantar Kashim Shettima, a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.
Mai shari'a Haruna Tsammani ne ya tabbatar da haka lokacin da yake karanto hukunci a kan ƙorafe-ƙorafen jam'iyyar APM, da ke ƙalubalantar zaɓen Bola Ahmed Tinubu na APC.
Kotun dai ta ce ta kori matakin ƙalubalantar cewa an ba da sunan Kashim Shettima, don zama ɗan takara har sau biyu ba.
Jam'iyyar APM ta ƙalubalanci matakin ba da sunan Shettima ne a matsayin ɗan takarar sanata a jihar Borno, kafin a sake bayar da sunansa a matsayin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar APC.
Tun farko, kotun ta kori ƙorafin APM da ke neman soke cancantar tsayawa takara ga Bola Tinubu da Kashim Shettima.
Hukumomi sun ce sun ɗauki matakai don tabbatar da doka da oda a lokacin sanar da hukuncin da kuma bayan hakan. 'Yan sanda sun ce sun ƙara tura jami'ansu sassan Najeriya don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Cikin amo mai ƙarfi, rundunar 'yan sanda ta ja hankalin waɗanda ta kira 'yan jamhuru da jiga-jigan siyasa, a kan su yi hattara wajen furta kalamai da ayyukansu, don kuwa ba za ta lamunci iza wutar tarzoma ko abin da zai jefa ƙasar cikin zaman kara zube ba.
Masharhanta na cewa ba a taɓa soke zaɓen shugaban ƙasa a tarihin Najeriya ba, tun bayan komawar ƙasar tafarkin dimokraɗiyya a 1999.
Sai dai, ga alama hakan ba shi da wani tasiri a dimokraɗiyya da ke ƙara ƙarfi da haɓaka kamar ta Najeriya. A 2015, Muhammadu Buhari ya kafa tarihi irinsa na farko a ƙasar, inda ya kayar da shugaban ƙasa mai ci, Goodluck Jonathan.

Asalin hoton, Nigeria Police/Facebook
Alƙalan kotun na gabatar da hukunce-hukuncen ne bayan kwashe tsawon fiye da wata huɗu suna sauraron bahasi da muhawara.
Hukunce-hukuncen da kotun ta ce za ta bayyana kai tsaye ta kafar talbijin "don yin komai cikin gaskiya, ba tare da rufa-rufa ba," na da matuƙar muhimmanci ga makomar siyasar Najeriya.
A baya dai, kotun ta ƙi amincewa da buƙatar nuna zaman kotun kai tsaye ta talbijin.
Har yanzu, zaɓen, ɗaya daga cikin mafiya zafi da Najeriya ta gani, kuma da aka fi fafatawa tsakanin manyan 'yan takarar uku, bai daina tayar da ƙura ba, da janyo muhawara musamman tsakanin magoya baya a shafukan sada zumunta.
Hukuncin kotun na zuwa ne daidai lokacin da Bola Tinubu yake cika kwana 100 da hawa mulki. Hukumar zaɓe ta Najeriya (INEC) ta ce ya ci zaɓen watan Fabrairu, da yawan ƙuri'a 8,794,726.
Manyan abokan takararsa sun ce ba su yarda ba, kowannensu na cewa shi ne ya yi nasara, don haka shi ya fi cancanta da halarcin zama shugaban Najeriya.
Akwai damar ɗaukaka ƙara
Masana shari'a a ƙasar kamar fitaccen lauyan Najeriyar nan, Femi Falana mai lambar SAN na cewa yankan baya da razanarwar da ake yi wa ɓangaren shari'a irin wanda ba a taɓa gani ba game da hukuncin kotu, abu ne da ba shi da wata ma'ana.
Ya ce duk ɓangaren da bai gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, to yana da damar ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙolin Najeriya.
Yayin hira da gidan talbijin na Channels TV, Femi Falana ya ce ya damu a kan yadda mutane suke nuna cewa komai ya ƙare a sauraron ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa.
A cewarsa, hakan ba gaskiya ba ne.
Duk ɓangaren da bai yi nasara ba, kuma ya ji bai gamsu da hukuncin ba, to yana da damar garzaya wa gaban Kotun Ƙoli.







