Bola Tinubu: Yabo da suka bayan kwana 100

...

Asalin hoton, FACEBOOK/BOLA TINUBU

'Yan magana kan ce lokaci tamkar takobi yake, idan ba ka yi amfani da shi ba ka sari damar da ke gabanka to shi zai sare ka.

Magana ce kan yadda kwanaki ke tafiya cikin gaggawa, yanzu an kwashe kwana 100 tun bayan rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya.

Babu shakka cikin waɗannan kwanaki abubuwa da dama sun faru waɗanda wasu sun yi wa mutane daɗi wasu kuma akasin haka.

Cikin waɗannan kwanaki an samu sauye-sauye masu yawa a manufofin gwamnati, da sauyi na masu rike da mukamai da ma ta rayuwar al'ummar kasar.

Bari mu yi duba kan wasu abubuwa da gwamnatin ta bullo da su waɗanda a wajen wasu matakai ne na ci gaba a wajen wasu kuma saɓanin hakan.

Cire tallafin man fetur

Shekaru masu yawa aka kwashe a Najeriya ana kai ruwa rana kan tallafin man fetur.

Su wane ne ke amfana da shi? Ta yaya yake taimakawa ko durƙusar da tattalin arziƙin Najeriya? Da dai sauran wasu tambayoyi da ke da alaƙa da hakan.

Tun gabanin zuwan gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, ake ta kukan cewa babu abin da tallafin farashin man fetur yake haifar wa Najeriya sai koma baya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An yi ta ƙorafin cewa wasu mutane ƙalilan ne ke amfana da tallafin maimakon al'ummar Najeriya baki ɗaya.

Wannan ya sa Shugaba Buhari ya yi alƙawarin cire tallafin, sai dai ya gaza yin hakan kai tsaye a tsawon shekara takwas na mulkinsa.

Sai dai a ranar da ya karɓi mulki, a cikin jawabinsa na farko, shugaba Tinubu ya fito ɓaro-ɓaro ya bayyana wa al'ummar Najeriya cewa "tallafin man fetur ya ƙare."

Masana da dama sun bayyana cewa ƙasar za ta ƙara samun kuɗaɗen da za ta gudanar da manyan ayyuka da su a gefe guda.

Suna cewa kuɗaɗen da ake bayarwa a matsayin tallafin za a iya tattalinsu domin a karkatasu zuwa wata hanyar da za ta amfani kowa a Najeriya.

Sai dai da dama daga cikin ƴan Najeriya na nuna shakku kan hakan sanadiyyar tsadar rayuwa da lamarin ya haifar.

Lamarin da sanya ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta kira zanga-zanga ta ƙasa baki ɗaya domin nuna rashin jin daɗinta da halin da lamarin ya jefa al'umma.

...

Asalin hoton, getty images

Dunƙule kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare

Kasuwar musayar kuɗi a Najeriya ta zama wata akalar sauya rayuwar al'umma, tashinta ko kuma faɗuwarta.

A duk lokacin da aka samu sauyawar farashin dalar Amurka a kasuwar bayan fage hakan kan shafar sauran kasuwanni.

Wannan na da alaƙa da yadda Najeriya ta dogara wajen shigo da kayan da take amfani da su daga ƙasashen ƙetare.

Sai dai gaza samun daidaito a kasuwar ta musayar kuɗi, kamar batun cire tallafin man fetur, shi ma ya samo asali ne daga gwamnatocin baya.

Wannan matsala ta ci gaba har zuwa lokacin da Tinubu ya karɓi jagorancin Najeriya.

Sabbin manufofinsa ya sa ya yi tunanin daidaita darajar Naira a babban banki CBN da na bankunan kasuwanci da kuma na kasuwar bayan fagge.

Sai dai lamarin ya ƙara ingiza faɗuwar darajar takardar ta naira.

Duk da dai shugaban ya ce an yi hakan ne domin kasuwa ta riƙa yi wa kanta farashi.

Masana tattalin arziƙi da dama sun yaba wa wannan ƙoƙari tare da fatan hakan zai iya dakatar da rashin tabbas a fagen musayar kuɗaɗen.

Tsadar rayuwa

Wannan matsala za a iya cewa ta samo asali ne daga matakin cire tallafin man fetur.

Farashin mai ya yi tashin gwauron zabi zuwa sama da naira 600, karon farko a tarihin ƙasar.

A sanadiyyar haka ne farashin kayan masarufi ya nunnunka.

Dalilin da ya kai ga tashin farashin kayayya musamman kayan abinci.

Wannan lamari ya tursasa wa gwamnatin tarayya da na jihohi fafutikar nemo hanyoyin da za su tallafa wa talaka.

Gwamnatin Tarayya ta ce ta ware kuɗi naira biliyan shida ga kowace jiha domin kashewa wajen samar da tallafi ga al'umma domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Haka nan an yi alƙawarin fitar da hatsi domin raba wa al'ummar.

Sai dai masana na ganin samar wa al'umma hanyar samun abin da za ci ɗauki ɗawainiyar kansu shi ne mafita kasancewar tallafin buhunan shinkafa da ake bayarwa ba lamari ne da zai dawwama ba.

Yajin aikin ma'aikata

Wata balahira mai kama da sarƙa, domin kuwa yajin aikin na da alaƙa da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki, wanda ma'aikata ke ganin hakan a matayin tarnaƙi da zai kawo tsaiko a ayyukansu.

Ma'aikata da dama sun nuna rashin jin daɗinsu saboda tsadar kuɗin mota, wanda a cewar wasu da yawa da BBC ta zanta da su, hatta albashinsu ba zai ishe su yin kuɗin mota na tsawon wata guda ba.

Wannan ya sa wasu jihohi a Najeriya suka rage wa ma'aikata ranakun aiki.

Wasu kuma suna ci gaba da duba yadda za su ɓullo da hanyoyin da za a sassauta wa ma'aikata halin da suke ciki.

Duk da cewa barazanar da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar ta yi na shiga yajin aiki bai kai ga nasara ba, bayan wata tattaunawa da ta gudana tsakanin ɓangaren gwamnati da na ƴan ƙwadago, daga baya ma'aikatan sun yi yajin aikin gargaɗi na kwana biyu a watan Satumba.

A ranar Talata 5 ga watan Satumba da kuma Laraba 6 ga watan, NLC ta gudanar da wani jayin aikin gargaɗi ga gwamnatin Najeriya, na neman a duba halin da mutanen Najeriya ke ciki.

Tare da yin gargaɗi shiga yajin aiki gama gari da zai tsayar da Najeriya cik nan da kwanaki masu zuwa idan gwamnati ba ta yi komai ba a kai.

Baya ga haka likitoci masu neman ƙwarewa na ƙasar sun gudanar da yajin aiki domin neman gwamnati ta cika musu alƙawarin da ta ɗauka a tattaunawarsu ta baya.

Wani lamari da ya jefa asibitoci da sauran mutanen gari cikin halin damuwa.