Muhawara ta ɓarke tsakani ƴan jam'iyyar Labour kan hukuncin kotu

.

Asalin hoton, Labour Party

Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya, 'ya'yan jam'iyyar hamayyar ta Labour na ci gaba da bayyana mabambanta ra'ayoyi, dangane da hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke, da ta yi watsi da wani hukuncin kotun daukaka kara da ya amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar ta Labour na kasa.

Inda wasu ke yabawa da hukuncin na kotun kolin da cewa ya yi adalci, wasu kuma na cewa hukuncin na bukatar fassarar da ta dace daga masana.

Hukuncin kotun kolin Najeriyar dai ya soke hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke ne, wanda ya yi la'akari da Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar Leba na kasa.

Kotun kolin ta ce, batun shugabancin jam'iyya al'amari ne na cikin gida, ba wata kotu da ke da hurumin yanke hukunci kansa. Kotun ta kuma ta yi nuni, cewa wa'adin shugabancin jam'iyyar Lebar na Julius Abure tuni ya kare.

Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar ta Labour bangaren Peter Obi, sun yi maraba da hukuncin suna masu cewar, wannan hukunci ya yi dai-dai.

Muhammed Indimi Abdullahi, daya daga cikin makusantan Peter Obi, ya ce 'mu na gani cewar kotu ta yi adalci, kuma ta yi abun da ya kamata, tun da mastala ce da tashafi cikin gida. Tunda kotu ta tabbatar masa da makomarsa yanzu ya rage mana mu kira taron majalsiar zartarwa na jam'iyya a dauki mataki na gaba', in ji shi.

"Yanzu abun da ya rage mana shi ne a zauna a yi taron zartarwa na jam'iyyar don a fara shirye shirye na yadda za a tafi da jam'iyyar bisa tsari, tunda dama waadin sa ya kare amma yaki sauka" a cewar Muhammed Indimi Abdullahi,

Sai dai wasu 'yan jam'iyyar ta Labour, irin su Honarabul Muhammed Abdullahi Raji, shugaban reshen jam'iyyar na jihar Kano, suna ganin wannan hukunci da kotun koli ta yanke a jiya Jumma'a, tamkar baki ne aka ja, don haka abin yana bukatar ingantacciyar fassarar da ta dace.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Gaba daya wannan hukuncin kotun dole ne fa sai an yi fassara akai, don kowa fassarar da ya gadama ya ke bayarwa. Tun farko me yasa kotun ma ta ke saurara wane shugaba wanenen ba shugaba ba, babu wata kotu da aka baiwa hurumin, yin wannan, tun da INEC ta yi wa jam'iyya rajista, kundin tsarin mulin jam'iyyar ya ce yan jam'iyyar ne ke da damar da za su zabi wanda zai shugabance su", in ji Honarabul Muhammed Abdullahi Raji.

Shugaban jam'iyyar Labour din na Kano, ya kara da cewar, 'abu ne da ya ke karara, kasancewar basu kori aburen ba, wasu ne dai kawai ke son a ce ana rikicin ko an sami rabuwar kawuna a tsakanin 'yan Najeriya, abun tambaya anan shi ne a wane babban taron jam'iyyar daga ciki, anyi a Benin sannan an yi a Inyewi,' in ji Honarabul Muhammed Abdullahi Raji.

Jam'iyyar Labour ta shiga rikicin shugabanci ne, bayan rasuwar shugabanta na kasa, Alhaji Abdulkadir Abdulsalam a shekara ta dubu biyu da ashirin.

Inda ake ta sabata juyata tsakanin masu goyon bayan shugabancin Julius Abure da masu ganin ya zama wajibi a sake lalen shugabancin bayan karewa wa'adin shugabancin nasa.

Al'amarin da ya dangana har ga wata kotun daukaka kara, wadda ta amince da Julius Abure a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa. Amma kuma a jiya kotun kolin Najeriyar ta soke wancan hukunci.