Me ya sa rikici ya yi ƙamari a jam'iyyun siyasar Najeriya tun ba a je ko ina ba?

Asalin hoton, Google
A wani sabon salon a fagen siyasar Najeriya, duk da cewar akwai sauran lokaci kafin a kada gangar siyasar zaɓuka mussamman ma na babban zaben ƙasar 2027, tuni harkokin siyasa sun fara daukar ɗumi inda galibin manyan jam’iyyun hamayya a ƙasar ke cikin ruɗani da rikce-rikicen cikin gida.
Manyan jam’iyyun adawa irinsu PDP da Labour Party yanzu haka an samu ɓagarorin da ba sa ga-maci-ji da juna.
A iya cewa a tsari na siyasar Najeriya baraka na fitowa fili ne a jam’iyyun siyasa ana daf da zabe musamman babban zabe, to amma a wannan karon sabani ya fara tasiri a jam'iyyun siyasar Najeriyar tun ba a je ko ina ba.
A yanzu haka akwai bangarori biyu da ke kokawa a jam’iyyar Labour Party tsakanin Senator Nenadi Usman da Dr Julius Abure wanda yanzu haka ana gaban kuliya ana faman shari’a.
A jam’iyyar PDP ma an ja layi, tsakanin Ministan Abuja Nyson Wike wanda yake cikin gwamnatin APC da kuma bangaren wanda ya yi musu takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, inda lokaci zuwa lokaci ake caccakar juna da kuma yiwa juna habaici.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, na Jami'ar Bayero ta Kano, mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya ya ce rashin akida da kyakkyawar manufa na taka rawa wajen rashin samun jituwa a jam’iyyun Najeriyar.
"Dama kazo na zo ne suka shiga cikin jam'iyyar, kuma kowa ya zo da bukatar sa, wanda idan ya ga cewar baza ta biya ba, ko dai ya tattara kayansa ya tafi ko ya zauna ya yi ta yi wa jam'iyyar ƙafar ungulu, annan shi ya sa PDP da Labour da NNPP din suka tsinci kansu kace-kace a cikin rigingimu" a cewarsa.
Hari Ila yau Farfesa Kamilu Faggen ya ce 'akwai batun zafin gaba ko ruƙo, da yan siyasar ke dashi wanda idan mutum ya ga bukatarsa ba zata biya ba, sai ya ce bari kawai da a bai wa yaro riga, gwara a yaga kowa ya rasa' in ji shi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi kuwa masanin siyasar nan a Najeriya Dakta Kabiru Sufi, ya ce "dalilan da suka janyo aka sami wanan sauyin a salon siyasar da wuri haka shi ne abun da ya faru a zaben da ya gabata, musamman zarge-zargen da ake yi wa wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyu na taimakawa wani ɗan takara ko jam'iyyar da ta yi nasara a matakin tarayya, wanda hakan ya sa wasu ke ta ƙoƙari wajen ganin sun ƙwace jam'iyyar"
Haka kuma ya ce "ƙaratowar zaɓen ƙanan hukumomi a wasu daga cikin jihohin ƙasar, musamman bayan da kotun ƙoli ta bai wa kanan hukumomin ƙasar cin gashin kai, na daga cikin dalilan da suka sa aka sami sauyin siyasar, kuma hakan ya sa hamayya ta sake tasowa a cikin jam'iyyun ko a tsakaninsu, duk kuwa da cewar basu ne ke mulki a jihar ba. a cewar Dakta Kabiru Sufin.
A bangare guda kuwa, akwai wata jikakkiya a jam’iyyar NNPP mai mulkin Kano, inda ake samun rashin jituwa tsakanin manbobin jam’iyyar da wasu ‘yan majalisar tarayya, to sai dai, al’amarin bai fito fili ba, amma ana cewa gwamna Abba Gida-Gida ya shiga maganar, har ma ya gana da wadanda suke fushin.
Haka kuma wasu daga cikin ‘yan majalisar sun shaida wa BBC cewa idan abubuwa ba su sauya ba, to za su daki juji gwazarma ta yi kuka don kowa ya san halin da ake ciki.
Ita ma jam'iyyar APC na fama da na ta rikicin na cikin gida a wasu jihohi.











