Ka-ce-na-ce ya ɓarke tsakanin Gwamna Dauda da Sanata Yari

Asalin hoton, OTHER
Wani sabon cece-kuce ya barke tsakanin tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata a yanzu Abdul'aziz Yari da kuma gwamnan jihar mai ci Dauda Lawan Dare, kan batun matsalar tsaro a jihar.
Lamarin ya samo asali ne bayan bullar wata sanarwa daga ɓangaren sanata Abdul'aziz Yari, inda ya yi kira ga gwamnan jihar Dauda Lawan, kan ya mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro da ya saba cewa gadarta ya yi a wajen Bello Matawalle.
Sai dai da alama hakan bai yi wa bangaren gwamna Dauda Lawan dadi ba, inda har jam'iyyarsa ta PDP da ke Mulki a jihar ta ce Bello Matawalle ya kamata a ba wa wannan shawarar.
Cikin sanarwar, Abdul'aziz Yari, ya gargaɗi Gwamna Lawan a kan ya dakata da yin kalaman dabasu kamata kan ministan tsaron Najeriya ba, Bello Matawalle.
Sanarwar tsohon gwamnan ta ce maimaikon haka ya kamata gwamnan mai ci ya mayar da hankali wajen ci gaban jihar musamman samar da hanyoyin da za a magance matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Cikin sanarwar, sanata Yari, ya ce ita wannan matsala ta tsaro dukkan gwamnonin da suka gabace shi ciki har da Matawallen da shi kansa gwamnan na yanzu kowa ya yi fama da ita, sannan kuma dukkansu sun yi iya bakin kokarinsu wajen magance ta.
Sai dai a martanin jam'iyya mai mulkin jihar ta Zamfara PDP, ta ce sanata Yari ya bar jaki ne yana bugun taiki.

Asalin hoton, OTHER
Shugaban jam'iyyar PDP a Zamfara Dakta Jamilu Jibo Magayaki, ya shaida wa BBC cewa, ministan tsaro Bello Matawalle ya kamata a ce an bawa wannan shawara ba su ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce, "Mu abin da muka yi tsammanin daga wajen sanata Yari shi ne ya kara karfafawa gwamna mai ci gwiwa kan badakalar da ake zargin minista Matawalle ya aikata a lokacin da yake mulki shin gaskiya ce ko karya?
"Bayan haka kuma mu muna zaton su tsoffin gwamnonin Zamfara za su goya masa baya ta yadda za a hada karfi wajen magance matsalar tsaro da kuma ciyar da jihar Zamfara gaba."
To sai dai kuma jam'iyyar APC a jihar ta Zamfara ta ce gwamna Dare baya daukar shawara.
Sakataren jam'iyyar ta APC, Yusuf Idris, ya shaida wa BBC cewa, "Gwamna Lawan baya son ana bashi shawara, yanzu Abdul'aziz Yari, shawara ɗaya ya bashi amma ya sa sai zaginsa ake, sannan ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, Matawalle ya sha nemansa kan su zauna a nemo hanyar samar da tsaro a Zamfara, amma ya ki zuwa."
Sai dai duk da wannan cece-kuce da ke ci gaba da kasancewa tsakanin gwamnan jihar mai ci da kuma tsofaffin gwamnonin wato Sanata Abdul'aziz Yari da ministan tsaron Najeriya Bello Matawalle, har yanzu abin da talakawan kasar ke fata shi ne, ganin an kawar da matsalar tsaron da suke fama da shi tsawon shekaru.
Fatan 'yan jihar dai a daina wannan cece-kucen, a hada kai a ceto jihar Zamfara.














