Zanga-zanga - Ana musayar yawu tsakanin Ganduje da Abba kan tarzoma a Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje

Asalin hoton, FB/Multiple

Lokacin karatu: Minti 4

Wata sabuwar taƙaddama ta kunno kai a jihar Kano tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya da kuma gwamnan Kano na yanzu na jam’iyyar NNPP.

Tsohon gwamnan Abdullahi Umar Ganduje a cikin wata sanarwa ya buƙaci gwamnatin kasar ta gudanar da bincike kan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf.

Ganduje ya zargi gwamna Abba Kabir Yusuf da furta kalaman tunzura jama’a a gabanin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar kwanakin da suka gabata a duk fadin kasar.

Sai dai ɓangaren gwamnan na Kano ya yi watsi zargin wanda ya kira “soki burutsu”.

Tun hawa kan mulki, gwamnatin Kano ta NNPP ke takun saƙa da tsohon gwamnan jihar na jam’iyyar APC da ta gada.

Tsohon gwamnan, Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da martani ne ga zargin da gwamnatin Kano ta yi cewa shi ya yi hayar ƴan daba domin haifar da rikici a jihar a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar.

A cikin sanarwar da Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fitar ranar Alhamis, ya zargi gwamnan Abba Kabir Yusuf da yin kalaman da suka ingiza jama'a ga yin tarzoma da nufin baƙanta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta binciki gwamnatin jihar Kano domin kowa ya san cewa kafin zanga-zangar, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kalamai na tunzura jama’a, saɓani matakan da sauran gwamnonin jihohi suka ɗauka,” in ji Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai tun da farko gwamnatin jihar Kano ta zargi tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin wasu matasa da suka fasa kotu tare da sace takardun shari’oi.

“Kowa ya ga yadda mutanen Ganduje suka shigo Kano suka raba wa matasa makamai da kuɗaɗe da kayan shaye-shaye waɗanda suka far wa ɓangarori da dama na al’umma, lamarin da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi,” in ji Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano.

Sanarwar da gwamnatin Kano ta fitar ranar Laraba ta ce cikin takardun da aka kwashe har da na shari'ar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da gwamnatin jihar ke tuhumarsa da matarsa Hafsat da ɗansa Umar, da wasu mutum biyu bisa zargin karkatar da biliyoyin kuɗaɗe a lokacin mulkinsa.

Kuma a cikin martaninsa a ranar Alhamis, tsohon gwamnan ya yi watsi da zargin wanda ya danganta da yunƙuri na “ci gaba da yi masa bi-ta da ƙullin siyasa.”

“Wannan kawai wani yunƙuri ne gwamnatin Yusuf na ƙoƙarin karkatar da hankalin jama’a daga rikicin da ya faru a jihar,”

“Maganar cewa za a iya kwashe irin waɗannan muhimman takardu yayin zanga-zanga, ya ƙara nuna fito da gazawar wajen tafiyar da harkokin tsaro da na shari’a,” in ji Ganduje.

Wannan sabuwar sa’insa dai wata alama ce da ke nuna yadda takun saka ke daɗa munana tsakanin tsohon gwamnan jihar ta Kano da wanda ya gaje shi.

Masu zanga-zanga a birnin Kano ranar Alhamis 1 ga watan Agusta, 2024
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun a ranar farko ta zanga-zangar halin matsin rayuwa a Najeriya ne lamarin ya rikiɗe zuwa tarzoma a jihar ta Kano.

An samu arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro a lokacin da wasu daga cikin masu zanga-zangar suka yi yunƙurin kutsawa cikin gidan gwamnati.

Gabanin zanga-zangar dai, gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alƙawarin cewa sai tarbi masu zanga-zangar matuƙar za a yi ta cikin lumana, akasin matakin da sauran gwamnoni suka ɗauka na kira ga masu shirya zanga-zangar su jingine ta.

A wata ganawa da ya yi da masu ruwa da tsaki, kwana ɗaya gabanin ranar zanga-zangar, an ambato Abba Kabir na cewa: "A wurinmu, zanga-zanga hakkin kowane ɗan ƙasa ne bisa tsari na dimokuraɗiyya. Idan kuka yi zanga-zangar cikin lumana, zan tarbe ku, idan ma kuna so zan iya shiga cikin ku."

Sai dai jim kaɗan bayan fara zanga-zangar a ranar Alhamis an ga yadda wasu matasa suka riƙa farfasa wuraren ajiye kayan abinci a birnin na Kano suna kwasa.

Haka nan wasu sun riƙa lalata kadarorin gwamnati, inda har wasu suka ƙona wata sabuwar cibiyar harkokin sadarwa ta jihar.

Lamarin da ya kai ga cewa gwamnatin jihar ta ayyana dokar hana zirga-zirga ta ba-dare ba-rana.

Gwamnan ya yi zargin cewa wasu ƴan siyasa ne suka haddasa tarzomar da aka samu a jihar ta Kano a lokacin zanga-zangar.

Tun daga lokacin ne aka fara musayar kalamai tsakanin ɓangarori biyu na siyasar jihar waɗanda ba su ga-maciji da juna.

Siyasar Kano na daga cikin mafiya zafi a faɗin Najeriya - jihamafi yawan al'umma a arewacin ƙasar.