Wane tasiri sace takardun kotu zai iya yi ga shari'a?

Gudumar kotu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da aka gudanar a Najeriya ta tafi ta bar baya da ƙura.

A lokacin da wasu ke jimamin rashin ƴan'uwansu da suka mutu, wasu kuma na jimamin irin asarar da suka tafka ne sanadiyyar sace-sacen da wasu ɓata-gari suka yi da sunan zanga-zangar.

Wani abin da ba a zata ba - a jihar Kano inda zanga-zangar ta ƙazance - shi ne batun sace takardun shari'a a kotu.

A ziyarar da ya kai zuwa Babbar kotun jihar Kano, gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya nuna takaici kan yadda wasu matasa suka fasa kotun tare da sace takardun shari'o'i.

Takardar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba ta ce cikin takardun da aka kwashe har da na shari'ar tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje.

Tsohon Gwamnan dai shi ne Shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa a yanzu.

Gwamnatin Kano ƙarƙashin Jam'iyyar NNPP na tuhumar Ganduje, da matarsa Hafsat, da ɗansa Umar, da wasu mutum biyu bisa zargin karkatar da biliyoyin kuɗaɗe a lokacin mulkinsa.

Tuhumar da Ganduje da iyalin nasa suka musa, kuma suka bayyana a matsayin tuggu na siyasa.

To amma wane tasiri sace takardun kotu ke yi ga shari'a?

...

Asalin hoton, KANO STATE GOVERNMENT

Akwai fargaba?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barista Mohammad Mansur Aliyu, malami a Jami’ar Usman Danfodio da ke Sokoto ya ce: "Lallai zai iya shafar yadda za a gudanar da shari’a, amma akasari takardun kotu ba kwafi ɗaya ake yi ba.

"Misali, lokacin da gwmnati za ta shigar da ƙara, za ta buga kwafi da yawa. Akwai na alƙali, akwai na wanda ake ƙara, akwai na mai ƙara, sannan ana ajiye wasu. Babban abin da zai iya shafar shari’ar shi ne idan an riga an fara shari’a."

Saboda haka a cewar masanin shari'ar abin da ya faru a Kano da alama ba zai yi wani tasirin a zo a gani ba kasancewar ba a yi nisa ba a shari'ar.

"Har yanzu ba a fara shari’ar (gadan-gadan) ba, wanda ake zargi bai halarci zaman kotun ba tukuna. Don haka yawancin abubuwan da suka wakana watakila rubuce-rubuce ne na alkali, wadanda nake tunani ba zai yi wani tasiri," in ji Dokta Mansur.

Sai dai a cewar sa wannan abu ne da za a iya kauce mawa inda tun da farko an ɗauki matakan da suka dace.

Zanga-zangar da aka gudanar a Kano ta rikiɗe inda ta zama tarzoma, wani abu da ya kai ga cewa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga ta sa'a 24.

Gwamnatin jihar ta ce ta ayyana dokar ce domin kauce wa ƙarin asarar dukiya da ta rayuka.

Sai dai Barista Mansur ya ce an yi sakaci da ba a samar wa kotuna tsaron da ya dace ba gabanin zanga-zangar.

Ya ce "Kamata ya yi a ce su ma kotuna an tanadar musu da tsaro ta yadda babu yadda za a iya zuwa a taɓa su. Inda an tabbatar da tsaro a kotunan, da watakila hakan bai faru ba.’’

Dama dai tun kafin zanga-zangar, hukumomi sun nuna damuwa kan yiwuwar ɓarkewar rikici da ka iya haifar da tashe-tashen hankula.

Sai dai wataƙila hankalin hukumomin ba su kai ga tsaron kotunan ba, kasancewar ba kasafai ake samun irin waɗannan hare-hare a kan kotuna ba.

A mafi yawan lokuta, masu tayar da rikici a lokacin zanga-zanga sun fi mayar da hankali ne kan kantuna ko wauraren ajiye kayan abinci da na amfani, sai kuma ofisoshin jam'iyyu da gidajen ƴan siyasa.

Sai dai duk da cewa hari kan kotuna ba abu ne da zamo ruwan dare ba a Najeriya, akan samu irin haka lokaci zuwa lokaci.

A watan Satumban 2014 an kai wani hari a kan alƙalai da lauyoyi a Babbar Kotun Jihar Ekiti, inda ake zaman sauraron ƙarar da aka shigar ana ƙalubalantar tsayawa takarar zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar, a lokacin Mista Ayodele Fayose.

Barista Mansur ya ce domin kauce wa lalata takardu masu muhimmanci na kotu, ya kamata kotuna a Najeriya su rungumi tsarin fasahar zamani wajen adana takardun shari'o'i.