Yadda matashi ya cinna wa masu sallah wuta a Kano

...

Kimanin mutum 15 ne aka tabbatar sun mutu yayin da wasu ke ci gaba da jinya a asibiti bayan da wani mutum ya cinna wa masallaci wuta a jihar Kano da ke arewacin Najeriya - kamar yadda ƴansanda suka tabbatar.

Wani mutum ne ake zargin ya watsa fetur a cikin masallacin sannan ya cinna wuta ya kuma rufe ƙofofin masallacin daidai lokacin da kimanin mutane 40 ke gudanar da jam'in sallar asuba.

Lamarin ya faru ne sanadiyyar rikici kan rabon gado.

Tuni ƴansanda suka kama mutumin mai shekara 38 inda suke yi masa tambayoyi.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Mazauna ƙauyen sun ce wuta ta kama gadan-gadan a masallacin yayin da aka ji mutane na ihu a lokacin da suke fafutikar buɗe ƙofofin masallacin.

Daga nan ne mutane suka isa wurin masallacin domin kai ɗauki.

Wata sanarwa da ƴansanda suka fitar ta nuna cewa an tura ƙwararrun jami'an tsaro masu warware bam da sauran abubuwan fashewa zuwa wurin da lamarin ya faru.

Sai dai daga baya ƴansandan sun tabbatar cewa ba a yi amfani da bam wajen kai harin ba.

Hukumar kashe gobara a jihar ta Kano ta ce ba a nemi ɗaukin ta ba a lokacin da wutar ta tashi.

Ƴansanda sun ce wanda ake zargin ya tabbatar musu da cewa ya ɗauki matakin ne a wani ɓangare na turka-turkar rabon gado, inda ya ce ya cinna wutar ne kasancewar akwai wasu da yake tunanin sun danne masa hakki a cikin masallacin.

Jami'in ƴansanda Umar Sanda ya ce: "Abin da ya faru ba ya da alaƙa da ta'addanci, rikici ne kawai na batun rabon gado."

Ya kara da cewa "wanda ake zargin na hannunmu inda yake amsa tambayoyi."

Yawan mutanen da suka mutu na ci gaba da ƙaruwa kasancewar wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa na cikin mummunan hali a asibitin ƙwararu na Murtala Muhammad da ke Kanon.