Me ya sa daba ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a Kano?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
Daba wata matsala ce da aka daɗe ana fama da ita a jihar Kano da ke arewacin Najeriya inda tsawon shekaru ake ganin mummunan tasirinta.
Sai dai a kwanakin baya-bayan nan matsalar ta sake kunno kai inda a unguwar Ɗorayi faɗa tsakanin wasu ƴan daba ta kai ga kisan wani matashi.
Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da kama matashin tare da miƙa shi sashen da ke binciken manyan laifuka.
Rundunar, a cewar kakakinta ta gano wasu riƙaƙƙun ƴan daba 30 da suka addabi unguwar kuma a cikin adadin ta kama 22.
Matsalar ta daba dai ta sa jama'a a Kano na rayuwa cikin firgici tare da ƙauracewa fitar dare da kuma yin taka tsan-tsan da rana kasancewar harin daba na iya ritsawa da mutum a kowane lokaci.
Duk da ƙoƙarin hukumomin tsaro wajen kawar da matsalar, al'umma na ci gaba da fuskantar ɗaurin kai ganin yadda matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa tsawon shekaru.
Girman matsalar daba a Kano
BBC ta tuntuɓi wani tubabben ɗan daba, Sagir Usman Yarima wanda ya bayyana cewa daba matsala ce gagaruma ganin yadda take ƙara muni da kuma kai wa ga kisan bil adama.
Ya ce a baya, akwai unguwannin da suka fi shahara da dabanci sai dai a yanzu, akwai wasu unguwannin da ke wajen tsakiyar birni da suka tsunduma cikin matsalar.
A cewarsa, matsalar ta fi yawo a tsakanin matasa waɗanda ake ganin sune jagororin gobe. Hakan na ƙara raunata irin gudummawar da matasan ya kamata a ce sun bayar wajen haɓaka jihar Kano ta ɓangarori da dama.
Sagir ya bayyana cewa harkar daba kamar makaranta ce inda ake da manyan malamai da ke da ɗalibai waɗanda sune suka aikata miyagun laifuka bisa goyon bayan da suke samu.
Ya ce akwai manyan koma-baya da ke tattare da daba inda ya lissafo illolin da take yi kamar haka:
- Lalata zamantakewa
- Karya tattalin arziki
- Zubar da ƙimar Kano
- Ɓata tarbiyya
Unguwannin da daba ta fi ƙamari a Kano
A cewar tubabben ɗan dabar, a yanzu matsalar ta daba ta fi shafar unguwannin da ke wajen gari saɓanin baya da matsalar ta fi ƙamari a ƙwaryar birnin Kano.
Ya ce unguwannin da a yanzu suke fama da wannan matsala sun haɗa da:
- Ɗorayi
- Chiranchi
- Gama
- Rimin Kebe
- Yankaba
- Fanshekara
- Sabon Titi
- Hotoro
Sai kuma cikin ƙwaryar Kano da a yanzu ya ce matsalar ta ɗan ragu:
- Madigawa
- Adakawa
- Ƙoƙi
- Dogon Nama
- Yakasai
- Fagge
- Zage
- Yalwa
- Dan Agundi
Dalilin da ya sa aka kasa shawo kan daba
Sagir Yarima ya ce abin da ya sa matsalar take neman gagarar masu ruwa da tsaki shi ne rashin maganin ta tun daga tushe.
"Lokacin da aka zo za a yi aikin, hali irin na ɗan Najeriya tun daga hukumomin tsaro, akwai wasu ƴan siyasa musamman jami'an gwamnati da ke amfani da ƴaƴan al'umma, su ba su ƙwaya, su yi masu aiki, daga baya kuma su watsar da su." in ji shi.
Ya ce irin waɗannan abubuwan na ƙara ƙangarar da matasan da suka tsinci kansu a irin wannan matsala lamarin da ke warware ƙoƙarin magance matsalar.
"Akwai yaron da suke alfahari cewa idan an kama su suna da iyayen gidan da suke karɓo su, sau da dama idan an kama yaran, ai zuwa ake a karɓe su." kamar yadda ya ce.
Tubabben ya ce akwai wasu da suke hana ruwa gudu a wajen kawo sauyi a kan wannan matsala saboda "akwai masu amfana da jahilci da talaucin yaran suna ƙara ta'azzara matsalar daba a Kano."
Mece ce mafita?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sagir Yarima ya ce idan har ana son a daƙile matsalar daba to dole ne a yi amfani da shugabannin unguwanni wajen yin kira ga su matasan da suke wannan aika-aika ta dabanci.
Ya kuma ce dole ne sai gwamnati ta shigo domin tallafawa matasan da ko dai suka tuba ko kuma aka kama su da sana'oi da kuma sake wayar masu da kai game da illolin matsalar.
Matakin da gwamnati take ɗauka
Daga cikin dabarun da gwamnatin jihar Kano ke ɗauka na yaƙi da wannan matsala shi ne a shekarar da ta gabata, ta rundunar ƴan sandan jihar ta dauki tubabbun ’yan daba 50 aikin ɗan sanda a Jihar.
Ana ganin matakin zai ƙara janyo waɗanda ba su tuba ba suma su miƙa makamansu domin zama ƴan ƙasa na gari da kuma yin aiki tare da su domin kawo sauƙin fitinar.
Ko a Satumbar bara, an samu ƴan daba 43 da suka ajiye makamansu inda kuma suka yi alƙawarin tuba da neman afuwar al'umma da hukuma.
Akwai kuma runduna ta musamman da aka kafa domin yaƙi da ayyukan ƴan daba da kuma matakin baya-bayan nan na kafa ofishin ƴan sanda a unguwar Ɗorayi inda matsalar a yanzu ta fi ƙamari.











