Abubuwan da suka kamata ku sani game da rundunar Anti-Daba ta Kano

Jami'an yan sandan Kano

Asalin hoton, Getty Images

Matsalar daba babbar matsala ce a Kano arewacin Najeriya, dalilin da ya sa kenan aka kafa runduna ta musamman domin yaƙi da matsalar.

Sai dai zargin kisa, da cin zarafi da wuce gona da iri da ake yi wa ƴan sandan Anti daba a Kano ya haifar da saɓanin ra'ayi kanta a jihar.

A kwanan nan ne aka zargi ƴan Anti Daba da halaka wasu matasa a Kano, lamarin da ya haifar da ƙone-ƙonen tayoyi domin adawa da ayyukan rundunar.

Wasu Kanawa na son a rusa rundunar wasu kuma na son a yi mata garanbawul saboda amfaninta ga matsalar dabanci.

Menene Anti Daba?

Anti Daba rundunar ƴan sanda ce ta musamman da aka kafa saboda rikicin daba da ya yi yawa a Kano.

Rundunar ta ƙunshi jami'an ƴan sanda da kuma tsoffin ƴan daba da suka tuba da suka amince su yi yaƙi da ƴan daba a rundunar ƴan sandan.

Rundunar da ke da hedikwata a Unguwar Sani Mainagge, an kafa ta ne kusan shekara 10 bayan dawowar mulkin tsohon Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso karo na biyu.

Kayan jami'an rundunar Anti Daba na daban ne ya bambanta da na ƴan sanda kuma babban aikinsu shi ne yaƙi da ƴan daba a Kano.

Ana jin daɗin Anti Daba?

Ana yaba wa rundunar da jin daɗin aikinsu ta wajen yaƙi da cikakkun ƴan daba a Kano. "Idan unguwa ta gagara, sukan shiga su yi maganin ƴan daban," a cewar wani mazaunin Kano.

Ya ce an samu sauƙin daba a unguwanni irinsu Ƙoƙi da Agadasawa da Mandawari da Ƙofar Wambai da Ɗorayi inda rikicin daba ya yi ƙamari, albarkacin ayyukan Anti Daba.

Sai dai ya ce wani lokaci suna wuce gona da iri inda suke shiga unguwa su dinga kamen mutane musamman samari da ba su da alaƙa da ƴan daba. "Suna musu dukan tsiya har ya kai ga ajalin mutum."

Kasancewar wasu daga cikin jami'an Anti Daba tsoffin ƴan daba ne, masu lura da lamurra a Kano sun ce yanzu aikinsu ya koma farautar tsoffin abokan gabarsu waɗanda suka tuba.

Me mutane ke son a yi?

Ra'ayi ya sha bamban inda wasu mutanen Kano ke son a bar wa yan sanda su yi aikin rundunar da ke yaƙi da ƴan daba ta Anti Daba.

Wasu kuma sun fi so a yi mata garanbawul saboda amfaninta ga maganin ƴan daba.

Akwai kuma waɗanda ke son a rusa sashen ƴan sandan, saboda yadda suke wuce gon da iri.

Shugaban kwamitin tsaro a Majalisar Wakilan Najeriya Sha'aban Ibrahim Sharaɗa ya ce zai gabatar da kuɗirin neman rusa rundunar gaban majalisar wakilai duk da ba gwamnatin tarayya ta kafa ta ba.

Ɗan majalisar ya bayyana fargaba kan kada abin da ya faru a Legas ya faru a Kano musamman lokacin zanga-zangar EndSARS, inda aka yi fashe-fashe da ƙone-ƙone.

Me rundunar ƴan sandan Kano ta ce?

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce abun da ya faru na zargin ƴan Anti Daba da wuce gona da iri a unguwar Sharaɗa shi ne na farko da ya taɓa faruwa.

Kakakin rundunar ƴan sandan DSP Haruna Abdullahi ya ce ba kasafai ake samun ƙorafi kan ayyukan ƴan Anti Daba ba.

"Wannan abu da ya faru shi ne farko da aka ɗauki mataki game da ƴan sandan, an kama su kuma an kulle su," in ji shi.

Ya ce jami'an Anti Daba sun yi ƙoƙari sosai wajen magance matsalar daba a Kano saboda shi ne babban laifin da aka fi aikatawa kamar ƙwatar kayan mutane musamman wayar salula.

Ya kuma ce akwai hanyoyi da aka yi tanadi ga jama'a na gabatar da ƙorafi kan aikin yan sanda, kuma duk lokacin da mutum ya wuce gona da iri akwai doka a kansa.