SARS: ‘Yan sanda ba abokanmu ba ne, in ji Ƴan Twitter

'Yan sandan SARS
Lokacin karatu: Minti 4

Mabiya shafukan sada zumunta na Tuwita a Najeriya sun yi wa ƴan sandan ƙasar ca, musamman ma na rundunar nan ta musamman mai yaƙi da fashi da makami da ake kira SARS.

Hakan ya biyo bayan mutuwar wani matashi ne da ake zargin ƴan sandan ne sanadi wanda suke zargin sa da kasancewa ''ɗan damfara'' da aka fi sani da ''Yahoo Boys'' a Osogbo, babban birnin Jihar Osun.

Rahotanni sun ce ƴan sanda sun bi matashin tare da wasu matasan uku a mota, inda a ƙoƙarinsu na tsere wa ƴan sandan suka yi hatsarin da ya yi sanadin mutuwar yaron a ranar Talata da yamma.

Matashin mai suna Remi a take yanke ya mutu, yayin da aka garzaya da sauran ukun da suka jikkata asibiti.

Tuni dai mazauna birnin suka ce matasa sun fara zanga-zangar nuna taƙaicinsu kan lamarin.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa mai magan da yawun ƴan sandan jihar Yemisi Opalola ta ce: ''Lamarin ya faru amma muna iya bakin ƙoƙarinmu don shawo kansa.''

A shafin Tuwita dai an ƙaddamar da wasu maudu'ai har uku da ake tattauna batun a kansu. Maudu'an sun haɗa da #EndSars da aka yi amfani da shi sau fiye da 28,000, da #Yahoo da aka yi amfani da shi sau kusan 300,000 da #EndPoliceBrutality da kuma #Flutterwave.

Wasu da dama na cewa ƴan sandan ba abokansu ba ne kamar yadda aka faɗa cewa ''Ɗan sanda abokin kowa.''

tuwita

Asalin hoton, Twitter

Ga dai abin da wasu ma'abota Tuwitta ɗin ke cewa:

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wani mai suna @whatsupblog9ja ya ce: ''SARS ta bi wasu mutane a Osgbo jiya har sai da suka jawo suka yi hatsari har da mutuwa, yayin da sauran suka ji rauni.

''Mun gaji da yadda SARS ke kashe mana matasa suna alaƙanta su da ƴan damfara na Yahoo. A kawo ƙarshe #EndSARS a yau!!''

Wasu kuwa zargin ƴan sandan suke yi da cewa babu dama su ga matasa ƴan ƙwalisa da abun hannunsu sai su ce ƴan damfara ne, kamar dai yadda wani GodFather ya rubuta:

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

''Shin babban laifi ne mutum ya mallaki IPhone?, Laifi ne mutum ya sa sutura mai kyau?, Laifi ne mutum ya sa hannun jari a harkar kuɗi ta intanet?.... Ni ɗan Najeriya ne kuma ina da ƴancina.''

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

@EroBaba ya ce: ''Ya isa haka, ya isa haka! Matasa dai ba su tsira ba a ƙasar nan kuma shugabannin na nuna ko a jikinsu. Lokaci ya yi da ya kamata a kawo sauyi a tsarin aikin ƴan sanda na Najeriya. A kawo ƙarshen SARS yanzu!

Sai dai yayin da ake tsaka da kushe ƴan sandan a Tuwita, an ce ba a rasa nono a ruga, don haka wasu kuma laifin ire-iremn matasan da ake kira Yahoo Boys suke gani.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

@Miss RUTH ta ce: ''Jinjina ga dukkan ƴan buge-buge masu neman halal ɗinsu. Su kuwa ƴan Yahoo su karɓi nasu yabon daga #EndSARS.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Aya Likita ma cewa ya yi: ''Na daina abota da wasu abokaina ƴan Yahoo na rungumi sabbin abokai masu ƙwazon neman na kansu. Ban taɓa da na sanin hakan ba. #EndSARS''

Tsakanin SARS da ƴan Najeriya

Ba wannan ne karo na farko da ake samun takun saƙa tsakanin ƴan Najeriya da rundunar SARS kan irin ayyukan da rundunar ke yi, waɗanda mutane ke zargin cewa zalunci ne zlla.

A shekarar 2017 an yi ta kiraye-kirayen a soke rundunar inda har aka yi ta zanga-zangar a wasu biranen kasar, bayan gangamin da aka rika yi a shafukan zumunta na neman a rushe ta bisa zargin taka hakkin bil'adama.

Ammam a martanin da ta mayara a watan Disamban 2017 rundunar 'yansandan Najeriya ta ce babu wani abu da zai sa ta rusa rundunar nan ta musamman mai yaki da fashi da makami da ake kira SARS duk da kiraye-kirayen da wasu a kasar ke yi na soke ta.

Karin labarai masu alaƙa