Me ya sa ƴansanda ke yin harbi a lokacin zanga-zanga?

- Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
A Najeriya zanga-zangar matsin rayuwa na ci gaba da gudana, kuma wani abu da ake nuna damuwa a kai shi ne yawaitar rasa rayuka tun bayan ɓarkewar zanga-zangar a ranar ɗaya ga watan Agusta.
Ƙungiyar Amnesty International ta ce kimanin mutum 13 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar zanga-zangar, sai dai rundunar ƴansandan ƙasar ta musanta hakan.
Amma shugaban ƙasar, Bola Tinubu, a cikin jawabin da ya yi wa al'ummar ƙasar a ranar Lahadi ya jajanta wa ƴan'uwan mutanen da aka kashe a "Borno da Kano da Kaduna Jigawa da sauran jihohi."
A cikin sanarwar da ta fitar, Amnesty International ta ce: "Wajibi ne hukumomi a Najeriya su yi bincike domin tabbatar da cewa jami'an tsaron da ake zargi da hannu a lamarin sun fuskanci sharia'a."
Haka nan a wurare da dama da zanga-zangar ta rikiɗe zuwa tarzoma, wasu daga cikin masu zanga-zangar sun bayyana cewa jami'an tsaro ne suka buɗe wuta a kan al'umma.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake zargin jami'an tsaro a Najeriya da harbi kan masu zanga-zanga ba.
Ko a shekarar ta 2020, lokacin da aka gudanara da zanga-zangar adawa da rundunar ƴansanda ta SARS, an zargi jami'an tsaro da buɗe wuta kan masu zanga-zanga a gadar Lekki da ke birnin Legas.
Wani lamari da ƙungiyoyin kare hakkin bila'adama suka yi Allah-wadai da shi.
Shin me ya sa jami'an ƴansanda ke harbi da bindiga a lokacin zanga-zanga duk kuwa da cewa ana samun asarar rayuka?

Asalin hoton, Getty Images
Tsohon kwamishinan ƴansanda a Najeriya, CP Muhammad Indabawa ya ce akwai matakan da ƴansanda ke bi wajen tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zanga.
Ya ce wadannan matakai ne ake bi har ta kai ga lokacin da za a iya yin harbi da bindiga idan bukatar hakan ta taso.
Shi kuwa tsohon kwamishinan ‘yansanda Muhammad Wakili ya ce “ba a yin harbi har sai an cika wasu sharudda na cikin doka”
Ya ce akwai ‘First order 237’ inda aka nuna lokacin da dan sanda zai iya yin harbi.
Sai dai a cewarsa idan an yi amfani da kwarewa da hakuri da hankali to akan yi zanga-zanga a gama lafiya sai dai idan an samu bata-gari.
Matakan kan fara ne daga ƙasa zuwa sama, a cewar tsohon jami'in ɗansanda.
Mataki na farko - Bayar da kariya
Matakin farko shi ne lokacin da ƴansanda ke bayar da kariya ga masu zanga-zanga.
"Idan masu zanga-zanga na yi tafiyar da ita cikin lumana, ƴsandan za su ci gaba da ba su kariya har zuwa lokacin da za su gama su watse," in ji CP Indabawa.
CP Wakili ya ce in dai zanga-zanga ce ta lumana ba ta wuce matakin farko, sai dai sau da dama zanga-zangar lumanar ce ke rikidewa tana komawa tarzoma.
Mataki na biyu - Gargaɗi

Asalin hoton, Getty Images
Mataki na biyu kuma a cewar CP Indabawa shi ne na gargaɗin masu zanga-zanga.
"Idan abu a ya fara rikicewa za a shiga matakin 'proclamation," in ji tsohon ɗansandan.
Ya ce a lokacin da ƴansanda suka ga cewa lamarin zai ƙazance ko kuma za a samu rikici a lokacin zanga-zanga, za su sanar da masu zanga-zanga cewa su watse.
Kuma a cewarsa idan har a wannan lokacin masu zanga-zanga suka watse, to shi ke nan babu wata barazana, kowa zai kama gabansa.
Amma idan masu zanga-zanga a wannan lokaci suka ƙi watsewa, ƴansanda na da damar su ɗauki mataki na gaba.
Mataki na uku - Amfani da barkono mai sa hawaye

Asalin hoton, Getty Images
Idan har matakan farko da na biyu suka gaza zai zama wajibi ga ƴansanda su ɗauki mataki na uku domin kauce wa taɓarɓarewar doka.
A wannan mataki ne jami'an za su yi amfani da barkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zangza.
Indabawa ya ce akan ɗauki wannan mataki ne domin gudun kada rikici ya kaure har a samu jin rauni ko kuma rasa rai.
Ana sa ran idan aka harba hayaƙin mai sa hawaye dukkanin masu zanga-zanga za su watse saboda tasirin da yake da shi a jikin ɗan'adam.
A wannan lokaci zanga-zangar ta zama abin da ake kira 'unlawaful assembly' (taron da ya saɓa wa ƙa'ida," in ji CP Indabawa.
"Saboda a wannan lokaci za ka ga an fara ɗauke-ɗauke a doki wasu a kwashi kayan wasu a kuma kashe wasu idan ba a yi hankali ba."
Wannan shi ne mataki na farko da jami'an na ƴansanda ke ɗauka na yin amfani da wani abu domin korar masu zanga-zanga baya ga gargaɗi na baka.
Mataki na huɗu - Harbi

Mataki na gaba shi ne harbi, wanda shi ne matakin ƙarshe da ƴansanda kan ɗauka a lokacin da sauran matakan da suka gabata suka ci tura.
CP Muhammad Wakil ya ce “amfani da harsashi akwai tsanani sosai, domin sai an cika sharudda kafin a kai ga haka.
“Misali idan wani zai kashe wani, ya zama wajibi a yi amfani da harsashi domin a hana shi.”
CP Indabawa ya ce "a lokacin da za ka ga mutane sun ɗauko duwatsu ko wuƙa ko wasu makamai, to a lokacin ne za a bai wa ƴansanda damar su yi harbi."
A cewarsa, ƴansanda kan ɗauki wannan mataki ne domin kare kansu da kuma na al'ummar da ba su ji ba ba su gani ba.
Wane irin harbi aka amince ƴansanda su yi lokacin zanga-zanga

CP Muhammad Indabawa mai ritaya ya ce ba kawai ana bai wa jami'an ƴansanda umarnin yin harbi a kawai ba ne ko ta wane irin hali.
A cewarsa akwai ƙa'idar yin harbi ga ƴansanda waɗanda ke ƙoƙarin shawo kan masu zanga-zanga.
"Harbin da aka amincewa ƴansanda su yi shi ne wanda muke kira 'below the knee' (ƙasan gwiwa)," a cewar Indabawa.
Shi kuwa CP Wakili cewa ya yi ”a kodayaushe ba a harbi don a kashe, ana harbi ne don a samu gwiwa.”
Ba a amince jami'in dansanda ya yi harbi a ƙirji ko wani wuri na jiki ba.
Sai dai Indabawa ya ce akwai lokutan da akan samu kuskure saboda abubuwa sun rincaɓe a samu wani a saman jiki "wannan kuma wani abu ne daban," in ji shi.
Me kundin tsarin mulki ya ce kan harbin masu zanga-zanga?
Wani masanin shari’a kuma malamin jami’a a Najeriya, dakta Sulaiman Santuraki, ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa al’umma damar yin zanga-zanga da kuma ‘yancin yin rayuwa ba tare da an kashe su ba da wani kwakkwaran dalili ba.
To amma akwai lokutan da kuma kundin tsarin mulkin ya bai wa jami’an tsaro damar daukan mataki kan masu zanga-zanga wadanda ke kokarin tayar da fitina.
A cewarsa “sashe na 33 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya bai wa kowa yancin rayuwa, ya kuma yi bayani kan inda akan samu togiya.
Daya daga cikin togiyar ita ce “yancin dakile bore ko tayar da kayar baya.”
Ya ce “a duk lokacin da wani mutum ya zama barazana ga rayuwar wani mutumin na daban to babu yadda za a yi a ce a kare tasa rayuwar.
“Haka nan ma idan mutum ya zama barazana ga dukiyar wasu mutane, saboda rayuwa da dukiya duk ana ba su kariya iri daya ne.”











