Manyan zanga-zanga biyar da aka yi a Najeriya da dalilan yin su

Wasu ƴan Najeriya masu zanga-zanga a Legas da ke Najeriya cikin shekarar 2022

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu ƴan Najeriya masu zanga-zanga a Legas da ke Najeriya a shekarar 2022
    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 7

Gwamnatin Najeriya ta buƙaci matasan ƙasar su jingine aniyarsu ta yin zanga-zanga wadda suka ce za ta gudana a farkon wata mai zuwa.

Bayan wata tattaunawa da ta gudana ranar Laraba a ofishin sakataren gwamnatin ƙasar, Ministan Yaɗa labarai Mohammed Idris ya sake nanata kiran da shugaban ƙasar ya yi na cewa matasa su yi haƙuri game da zanga-zangar.

"Gwamnati na sane da halin da ƴan ƙasa ke ciki, muna jin koken al’umma amma muna roƙo a ba wa gwamnati ƙarin lokaci da za ta magance dukkanin bukatunsu," in ji ministan.

Har yanzu dai rahotanni na cewa babu cikakkiyar masaniya kan waɗanda ke shirya zanga-zangar kuma babu tabbas kan dalilan yin ta.

Sai dai da yawa daga cikin masu kiraye-kirayen yin zanga-zangar a shafukan sada zumunta na kokawa ne kan matsin rayuwa, da kuma rashin tsaro a sassan ƙasar.

Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, da faɗuwar darajar naira tun bayan cire tallafin man fetur a watan Mayun shekara ta 2023.

Zanga-zanga a Najeriya ta samo asali, tun daga daga lokacin mulkin mallaka, zuwa bayan samun ƴancin kai.

Yawancin zanga-zangar da aka yi a ƙasar cikin shekarun baya sun faru ne domin nuna adawa da wasu manufofin gwamnati.

Ga kaɗan daga cikin zanga-zangar da aka yi a ƙasar da kuma dalilan da suka haifar da yin su.

2020 - Zanga-zangar 'EndSars'

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin watan Oktoban shekarar 2020, lokacin da ya kamata ƙasar ta yi bikin cika shekara 60 da samun ƴancin kai, wasu matasa sun fantsama kan titi domin bayyana fushi kan abin da suka kira amfani da ƙarfi 'fiye da ƙima' na wani ɓangare na ƴansandan ƙasar.

Zanga-zangar ta fara ne daga Legas, cibiyar kasuwanci na ƙasar da ke kudanci, inda ta bazu zuwa sauran sassan ƙasar.

Haka nan zanga-zangar ta samu karɓuwa har a wasu sassa na duniya.

Waɗanda suka shirya ta sun yi amfani da shafukan sada zumunta, musamman tuwita/X wajen neman gudummawa da goyon baya daga al'ummar duniya. Kuma sun samu nasarar yin hakan.

Matasan sun ce rundunar ƴansanda ta musamman da ke yaƙi da fashi da makamai mai suna SARS na wuce gona da iri a ayyukansu.

Lamarin ya ƙazance kuma ya zo ƙarshe ne a ranar 20 ga watan Oktoban shekarar ta 2020, lokacin da aka samu arangama tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro.

An zargi jami'an tsaro da 'harbi kai-tsaye' kan matasan da suka taru a gadar unguwar Lekki ta jihar Legas, lamarin da aka yi amannar cewa ya yi sanadiyyar asarar rayuka.

Lamarin da ya fara a matsayin zanga-zangar adawa da rundunar SARS ya rikiɗe zuwa wata dama ga matasa domin sauke fushinsu kan shugabanni da rashin kyakkyawan jagoranci da matasan suka ce ƙasar ta daɗe tana fama da shi.

Duk da cewa gwamnatin ƙasar ta sanar da soke rundunar ƴansandan ta SARS, matasa sun ci gaba da zanga-zanga, inda suka buƙaci gwamnati ta kawo sauyi a yanayin tafiyar da lamurran ƙasar, har sai da aka samu arangamar ta gadar Lekki.

Daga baya gwamnati ta kafa wani kwamitin bincike kan abubuwan da suka faru.

A ƙarshen shekarar 2021, rahoton kwamitin binciken da aka bankaɗo ya zargi jami'an tsaron da laifin harbi da kisan masu zanga-zanga.

Wannan zanga-zanga ce da za a daɗe ba a manta da ita ba a tarihin Najeriya.

2012 - Zanga-zangar cire tallafin man fetur ta 'OccupyNigeria'

..

A watan Janairun 2012, dubban masu zanga-zanga sun fantsama kan titunan manyan biranen Najeriya bayan shugaban ƙasar na wancan lokaci Goodluck Jonathan ya sanar da cire tallafin man fetur.

A Legas, jami'an ƴansanda sun harba hayaƙi mai sa hawaye kan masu zanga-zangar a ƙoƙarin tarwatsa su.

Al'ummar ƙasar sun koka kan cewa cire tallafin man fetur ɗin zai haifar da gagarumin tashin farashin sufuri da kayan masarufi.

Jim kaɗan bayan sanar da cire tallafin, kuɗin litar man fetur ta tashi daga naira 65 zuwa kimanin 140 a gidajen mai, yayin da su kuma ƴan bumburutu suke sayar da litar man har naira 200.

Cikin waɗanda suka shiga zanga-zangar har da jagororin ƴan'adawa kamar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

An bayyana cewa mutum ɗaya daga cikin masu zanga-zangar ya rasa ransa a garin Ilori na jihar Kwara da ke tsakiyar ƙasar.

Haka nan an kama gomman masu zanga-zanga.

Daga baya, Shugaba Goodluck Jonathan ya miƙa wuya ta hanyar mayar da tallafin man fetur din tare da kawo sauye-sauye a yadda gwamnati ke kashe kudaɗe.

1993 - Zanga-zangar soke zaɓen 'June 12'

Daga baya gwamnatin Najeriya ta amince da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyya

An gudanar da zaɓen shugaban Najeriya a ranar 12 ga watan Yunin 1993 karo na farko tun bayan da sojoji suka tuntsurar da gwamnatin farar hula ta Jamhuriya ta Biyu a 1983.

An shirya zaɓen ne a ƙoƙarin mayar da ƙasar zuwa ga tafarkin dimokuraɗiyya daga mulkin soja a ƙarƙashin Janar Ibrahim Babangida.

Sakamakon da aka fara tattarawa ya nuna cewa ɗantakarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) Moshood Abiola shi ne ke kan gaba, kuma zai iya samun nasara kan Bashir Tofa na jam'iyyar NRC.

To sai dai Janar Babangida ya soke zaɓen bisa hujjar cewa "an gudanar da maguɗin zaɓe".

A cikin watan na Yuni, an samu tashe-tashen hankali musamman a yankin kudu maso yammacin ƙasar. Lamarin ya sanya mutane da dama sun tsere daga yankin, musamman Legas cibiyar kasuwanci ta ƙasar.

Haka nan ƙasashen duniya sun yi tir da lamarin, wanda a ƙarshe ya kai ga saukar Ibrahim Babagida daga muƙamin shugaban ƙasa tare da samar da gwamnatin riƙon ƙwarya ƙarƙashin Ernest Shonekan.

Daga ƙarshe Janar Sani Abacha ya karɓi mulkin ƙasar a watan Nuwamban 1993.

Sai dai a ranar 11 ga watan Yunin 1994, Abiola ya ayyana kansa a matsayin shugaban ƙasa, lamarin da ya sanya gwamnati ta fara neman sa.

Shugaban ƙasa na wancan lokaci, Janar Sani Abacha, ya zargi Abiola da cin amanar ƙasa, kuma an samu nasarar kama shi a ranar 23 ga watan Yunin 1994.

1978 - Zanga-zangar ɗalibai ta ƙarin kuɗin makaranta

...

Asalin hoton, Getty Images

A shekarar 1978 an samu ɓarkewar wata zanga-zanga da aka yi wa laƙabi da 'Ali Must Go', wadda ɗaya ce daga cikin bare mafi muni da ɗalibai suka gudanar a tarihin ƙasar.

Zanga-zangar ta ɓarke ne sanadiyyar ƙarin kuɗin makaranta a lokacin mulkin soji na tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

A wannan lokaci shugaban Hukumar kula da jami'o'i ta ƙasar ta sanar da ƙarin kuɗin makaranta sanadiyyar matsin tattalin arziƙi.

Duk da cewa ba a yi ƙari a gundarin kuɗin makaranta ba, amma ƙarin da aka yi ya nuna cewa ɗalibai za su riƙa biyan naira 90 a matsayin kuɗin ɗaki.

Haka nan an ƙara yawan kuɗin abinci, inda kwano ɗaya na abinci ya tashi daga naira ɗaya da kwabo hamsin zuwa naira biyu.

Bayan ganawa, ɗaliban ƙarƙashin lemar Ƙungiyar Dalibai ta Najeriya (NUNS) bisa jagorancin shugabanta Segun Okeowo, sun yanke shawarar ɗaukar mataki a kan gwamnati ta hanyar yin bore.

Da farko ɗaliban sun fara ne da ƙaurace wa ajujuwa, amma sai suka ga kamar matakin ba zai tursasa wa gwamnati ta sauya ra'ayinta ba.

Daga nan ne ɗaliban suka fara gudanar da zanga-zanga a Jamia'r Legas, lamarin da ya kai ga harbin wani ɗalibi.

Wannan ya sanya zanga-zangar ta yaɗu zuwa jami'o'in ƙasar, kamar Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda aka yi zargin cewa an kashe wasu ɗalibai sanadiyyar arangama da jami'an tsaro.

Bayan mako ɗaya ana zanga-zanga gwamnatin ƙasar ta rufe jami'o'i a fadin ƙasar.

Haka nan an kafa kwamiti domin yin bincike kan abubuwan da suka faru.

1929 - Zanga-zangar take hakkin mata ta 'Aba Women Riot'

Jami'an tsaron Najeriya a yankin gabashin ƙasar domin tabbatar da tsaro

Asalin hoton, Getty Images

Wannan wata zanga-zanga ce da mata ƴan ƙabilar Ibo a yankin gabashin Najeriya suka gudanar a watan Nuwamban 1929 domin nuna adawa da turawan mulkin mallaka, waɗanda suka zarga da danniya da take hakkin mata.

Zanga-zangar ta fara ne a lokacin da matan suka yi takanas zuwa garin Oloko domin tuhumar baturen yankin.

Zanga-zanga ce wadda turawan mulkin mallaka ba su taɓa ganin irin ta ba a yankin Afirka.

Zanga-zangar ta karaɗe garuruwan lardin Owerri da Calabar, wadanda suka ƙunshi kimanin mutum miliyan biyu.

Ya zuwa ƙarshen zanga-zangar a ƙarshen watan Disamban 1929 an lalata kotunan lardi guda 10 tare da far wa ma'aikatan kotunan, an kuma kai hari kan kamfanonin turawa a Aba, Mbawsi da Amata.