Me ya sa wasu matasan Najeriya ke kiraye-kirayen yin zanga-zanga?

Wani ɗan ƙungiyar fararen hula lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da manufofin gwamnati a lokacin tunawa da ranar mulkin dimokuradiyya a Legas, ranar 12 ga watan Yunin 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani ɗan ƙungiyar fararen hula lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da manufofin gwamnati a lokacin tunawa da ranar mulkin dimokuradiyya a Legas, ranar 12 ga watan Yunin 2024
    • Marubuci, Haruna Ibrahim Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

A cikin makonnin da suka gabata, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suka mamaye muhawarar da ake tafkawa a shafukan sada zumunta da kuma a fili shi ne zanga-zangar da wasu matasa ke shiryawa ta nuna fushi kan 'tsananin rayuwa' a Najeriya.

An ga matasa da dama sun fito suna nuna aniyarsu ta shiga zanga-zangar duk da kiraye-kiraye daga wasu ɓangarori, waɗanda ke ganin ba ta kamata ba.

Har lamarin ya janyo takun-saƙa tsakanin malaman addini da matasa a arewacin Najeriya, bayan da wani matashi ya nemi a ɗauki mataki kan duk wani malami da ya soki lamirin zanga-zangar.

Zanga-zangar mai taken #EndBadgovernanceinNigeria wadda ake cewa za ta gudana ne a ranar ɗaya ga watan Agusta na ci gaba da jan hankalin ba ƙungiyoyi kawai ba har ma hukumomi a ƙasar ta Najeriya.

Wani abu da ya sanya ƙungiyoyi da dama ke fitowa suna bayyana ra'ayoyinsu yayin da ranar da aka tsara yin zanga-zangar ke ci gaba da matsowa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ke ci gaba da artabu da ɗalibai masu zanga-zanga a ƙasar Bangaladesh inda aka kashe masu zanga-zanga aƙalla 150.

Haka nan kuma har yanzu ƙurar zanga-zangar da matasa suka yi a Kenya ba ta lafa ba, inda a can kuma ake zargin cewa gomman mutane ne suka mutu a lokacin zanga-zangar bayan da jami'an tsaro suka yi amfani da ƙarfi a ƙoƙarin tarwatsa su.

BBC ta duba mene ne dalilin da matasan ke bayarwa na kiraye-kirayen yin zanga-zanga?

Mene ne dalilin zanga-zangar?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Matsin tattalin arziƙi: Babban abin da matasan ke dogaro da shi game da kiraye-kirayen su na yin zanga-zangar shi ne matsin tattalin arziƙi.

Al'ummar ƙasar na kokawa kan yadda tashin farashin kayan masarufi ya sanya suke gaza sayen abubuwan buƙatu na rayuwa, yayin da ake zargin cewa talauci ya yi yawa ta yadda wasu mutanen ba su da tabbacin samun cin abinci koda sau ɗaya a rana.

A sabon rahoton da hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya ce hauhawar farashi a ƙasar ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin 2024.

Kuma tsawon wata 18 ke nan a jere ana samun hauhawar farashi a Najeriyar, duk da matakan da hukumomin ƙasar ke ɗauka.

Hauhawar ta fi shafar kayan abinci inda sabbin alƙalumman na hukuma suka ce ya kai kashi 40.87 a watan Yunin 2024 idan aka kwatanta da Yunin 2023 inda aka samu ƙaruwar kaso 15.6.

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin shugaba Tinubu ta cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, farashin kayan masarufi ya ci gaba da ɗagawa.

Da farko dai farashin litar man fetur ya nunka kusan sau huɗu, lamarin da ya sanya farashin sufuri ya tashi, haka nan ma na kayan abinci da sauran kayan buƙatu.

"Yunwar da aka bari tana kashe mu, abin ya fi nan, ana so sai mun halaka."

In ji ɗaya daga cikin masu son ganin an yi zangara-zangar, kamar yadda ta bayyana a shafinta na tiktok.

Rashin tsaro: Dalili na biyu da masu kiraye-kirayen yin zanga-zangar shi ne rashin tsaro.

Rashin tsaro na addabar kusan dukkanin yankunan Najeriya.

Rahoton kamfanin Beacon consulting mai nazari kan tsaro a yammacin nahiyar Afirka ya bayyana cewa an samu ƙarin yawan mutanen da ake kashewa a wata shida na farkon shekara ta 2024 fiye da watanni shidan farko na shekaru da dama da suka gabata.

Ɗaya daga cikin masu neman ganin an gudanar da zanga-zangar ya bayyana cewa "mu nan Arewa babban abin da ya fi damun mu shi ne rashin tsaro."

Shugaban kamfanin, Kabiru Adamu ya bayyana cewa "a cikin rabin shekarar nan an samu mace-mace na mutum 5,710...rabon da a ga irin haka tun cikin shekara ta 2013 lokacin da Najeriya ta zama ƙasa mafi yawan mutane da aka kashe dangane da ta'addanci a cikin ƙasar."

Gwamnatin Najeriya dai ta bayyana cewa tana bakin ƙoƙarinta wajen ganin an warware matsalar tsaron da ke addabar yankunan ƙasar.

Sai dai har yanzu ana ci gaba da samun matsalar masu garkuwa da mutane a yankin arewa maso yammacin ƙasar, yayin da a arewa maso gabas kuma cikin watan Yuni aka kai harin ƙunar bakin wake a garin Gwoza na jihar Borno, mafi girma da aka daɗe ba a ga irin sa ba.

Martanin gwamnati

Wasu matasa a lokacin zanag-zangar EndSars a birnin Legas da ke Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu matasa a lokacin zanag-zangar EndSars a birnin Legas da ke Najeriya

Babu shakka gwamnatin Najeriya kamar kowace irin gwamnati ba za ta so ganin al'umma sun fantsama kan titi suna zanga-zangar nuna ɓacin rai kan wasu manufofinta ba.

Zanga-zanga mafi girma ta baya-baya da ta faru a Najeriyar ita ce ta EndSars, wadda ta gudana a shekarar 2020.

Zanga-zangar wadda ta ɓarke a ƙoƙarin matasa na nuna fushi game da 'cin zalin' jami'an tsaro - musamman tawagar ƴansanda ta Sars, mai yaƙi da fashi da makami - ta nemi rikiɗewa zuwa tarzoma bayan da aka samu arangama tsakanin matasa da ƴansanda.

Shi ya sa a wannan karo kiraye-kirayen yin zanga-zanga ya ja hankalin hukumin gwamnati da ƙungiyoyi, lamarin da ya sa ɓangarorin suka mayar da martani kan lamarin.

A wata tattaunawa da BBC, ministan yaɗa labarun Najeriya, Muhammed Idris ya ce gwamnatin ƙasar na bakin ƙoƙarinta wajen ɗaukar matakan da suka kamata domin hana matasa fita zanga-zangar.

Sai dai a ɓangare ɗaya, Bayo Onanuga, wanda ɗaya ne daga cikin masu taimaka wa shugaban Najeriya kan yaɗa labaru ya zargi tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar LP, Peter Obi da hannu wajen shirya zanga-zangar.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci ƴan Najeriya su gudu shiga zanga-zangar.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

Karshen labarin da aka sa a X

Sai dai wannan bayani nasa ya janyo martani daga ɓangarori da dama. Inda ƙungiyar kare muradun al'ummar Ibo ta Ohanaeze Ndigbo ta yi tir da kalaman na Onanuga.

Haka nan kuma ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta yi Alla-wadai da kamen da aka yi wa ɗaya daga cikin waɗanda aka fi jin muryoyinsu a batun zanga-zangar, wanda ake kira Abu Salma a shafin TikTok.

Abu Salma ne daga cikin wadanda aka fi jin muryarsu a shafukan sada zumunta cikin a masu kiraye-kirayen yin zanga-zangar.

Ƙungiyoyi na nuna adawa da zanga-zangar

Tuni dai wasu ƙungiyoyi suka fito suka bayyana rashin amincewa da zanga-zangar, tare da bayyana cewa mamabobinsu ba za su shiga ba.

A ranar Litinin, shugabancin ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore, ƙarƙashin jagorancin Bello Bodejo sun gudanar da wani taron manema labarai a Abuja, inda suka yi kira ga mamabobinsu da su ƙaurace wa zanga-zangar.

Haka nan ma wata ƙungiya ta matasan Arewa ta bayyana cewa ba za ta shiga zanga-zangar ba.

Ita ma ƙungiyar tuntuɓa Arewacin Najeriya (ACF) ta buƙaci matasa su ƙaurace wa zanga-zangar kasancewar 'ba a shirya ta a lokacin da ya kamata ba."

A nata ɓangare, ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta buƙaci shugaban Najeriya, Bola Tinubu ne ya tattauna da masu shirya zanga-zangar domin samu mafita, kasancewar "al'umma a ƙasar na cikin mawuyacin hali" in ji shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero a cikin wata tattaunawa da kafar talabijin ta Channels.

Su wane ne ke shirya zanga-zangar?

Ya zuwa yanzu dai babu wata ƙungiya a zahiri da za a gani wadda ta ce ita ce ke shirya zanga-zangar.

Haka nan babu wani mutum da ya fito ya bayyana cewa shi ne jagora ko kuma shi ne ya assasa zanga-zangar ta nuna damuwa kan matsin rayuwa a ƙasar.

Sai dai abin da ake gani kawai shi ne matasa da ke tattauna batun a shafukan sada zumunta, suna ƙarfafa wa juna gwiwa wajen ganin sun fito domin yin zanga-zangar.