Yadda farashin kaya ya riƙa tashi a wata shidan farko na 2024 a Najeriya

Hauhawar farashi kayayyaki a Najeriya

Asalin hoton, AFP

Farashin kayayyaki a Najeriya na ci gaba da hauhawa a watanni shida a jere na 2024.

A sabon rahoton da hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta fitar ya ce hauhawar farashi a ƙasar ta ƙaru zuwa kashi 34.19 cikin 100 a watan Yunin da ya gabata.

Kuma tsawon wata 18 a jere ke nan da ake samun hauhawar farashi a Najeriya, duk da matakan da hukumomin ƙasar ke ɗauka.

Hauhawar ta fi shafar kayan abinci inda sabbin alƙalumman na hukuma suka ce ya kai kashi 40.87 a watan Yunin 2024 idan aka kwatanta da Yunin 2023 inda aka samu ƙaruwar kaso 15.6.

Tun a Janairun 2024, hukumar samar da abinci ta duniya FAO ta yi gargaɗin cewa za a fuskanci hauhawar farashin kayan abinci a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka ta yamma a shekarar 2024.

Kodayake, a wani hasashe na Asusun Lamuni na Duniya IMF a watan Mayu ya ce za a samu raguwar hauhawar farashin kaya a ƙasar a ƙarshen shekara, duk da cewa wasu na ganin matakan da ake ɗauka ba su nuna alamun samun rangwamen ba.

Alƙalumman hauhawar farashi wata shida a jere

  • A watan Janairun 2024, alƙalumman hukumar ƙididdiga ta Najeriya sun nuna cewa hauhawar ta kai kashi 29.90 inda aka samu ƙaruwar hauhawar farashin kayayyaki da kashi 0.98 idan aka kwatanta da watan Disamban 2023 da ya kai 28.92. Alƙalumman kuma sun nuna hauhawar kayan abinci ta kai kashi 3.21 inda aka samu ƙaruwar kusan rabin kashi wato 0.49 a Janairun 2024 idan aka kwatanta da watan Disamban 2023.
  • A watan Fabrairun 2024, alƙalumman hukumar ƙididdgiga sun nuna cewa hauhawar farashin ta kai kashi 31.70 idan aka kwatanta da Janairu da aka samu 29.90. Hakan na nufin an samu ƙaruwar kashi 1.80 idan aka kwatanta da Janairu. Alƙalumman kuma sun nuna hauhawar kayan abinci ta kai kashi 3.79 a Fabrairun 2024 inda aka samu ƙaruwar 0.58 idan aka kwatanta da Janairun 2024.
  • A watan Maris na 2024, alƙalumman hukumar NBS sun nuna cewa hauhawar farashin ta kai kashi 33.20 idan aka kwatanta da Fabrairun 2024 inda aka samu 31.70. Hakan na nufin an samu ƙarin kashi 1.50 idan aka kwatanta da watan Fabrairu. Alƙalumman kuma sun nuna hauhawar farashin kayan abinci ta kai kashi 3.62 a watan Maris na 2024 inda aka samu ƙaruwar kashi 0.17 idan aka kwatanta da Fabrairun 2024 da hauhawar ta kai kashi 3.79.
  • A watan Afrilun 2024, alƙalumman hukumar NBS sun nuna cewa hauhawar farashin ta kai kashi 33.69 idan aka kwatanta da Maris na 2024 da aka samu 33.20. Hakan na nufin an samu ƙarin kashi 0.49 idan aka kwatanta da Maris. Sai dai rahoton na NBS ya nuna raguwa aka samu a ɓangaren kayan abinci a watan Afrilun 2024 da aka samu kashi 2.50 inda hakan ke nufin an samu raguwar kashi 1.11 idan aka kwatanta da watan Maris na 2024.
  • A watan Mayun 2024, alƙalumman hukumar ƙiddiddigar sun nuna cewa hauhawar farashin ta kai kashi 33.95 idan aka kwatanta da Afrilun 2024. Hakan na nufin an samu ƙarin kashi 0.26 a Mayu idan aka kwatanta da Afrilun 2024. A ɓangaren kayan abinci rahoton watan Mayu da hukumomi suka fitar ya nuna samu raguwa da aka samu kashi 2.28 wanda hakan ke nufin an samu raguwar kashi 0.22 idan aka kwatanta da Afrilun 2024.
  • A watan Yunin 2024, hauhawar farashin ta ci gaba da ƙaruwa inda ta kai kashi 34.19 kamar yadda sabbin alƙalumman hukumar ƙididdiga ta Najeriya suna nuna. Hakan na nufin an samu ƙaruwar kashi 0.24 idan aka kwatanta da watan Mayu. A ɓangaren kayan abinci kuma an samu ƙari ne inda alƙalumman suka nuna ya kai kashi 2.55 wanda hakan nufin ƙarin kaso 0.26 idan aka kwatanta da watan Mayun 2024.
Farashi ya riƙa hauhuwa tun kafin shigowar shekara ta 2024
Bayanan hoto, Farashi ya riƙa hauhuwa a Najeriya tun kafin shigowar shekara ta 2024

Me ya haifar da hauhawar?

Ana alaƙanta hauhawar farashin kayayyaki da faɗuwar darajar naira a Najeriya, ƙasar da tattalin arzikinta ke dogaro da man fetur.

Janye tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi har yanzu yana ci gaba da yin tasiri ga tsadar kayayyaki, da kuma barin kasuwar kuɗin ƙasashen waje ta daidaita farashin.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana na ganin hauhawar ta kai ƙololuwa a watan Yuni amma suna hasashen za a iya fara ganin sauƙi a watan Yuli amma sai idan har darajar naira ta farfaɗo.

Ana hasashen Babban Bankin ƙasar zai yanke hukunci kan farashin kuɗin waje nan da mako mai zuwa, amma masana na bayyana shakku kan yadda matakan za su yi tasiri ga saukar tsadar kayayyaki.

Masana irinsu Dr Muhammad Shamsudden, malamin tattalin arziki a Jami’ar Bayero Kano, na ganin a zahiri hauhawar farashin kayayyakin ta zarta alƙalumman hukumomi.

A cewar masanin, duk lokacin da canjin kudi na kasashen waje ya sauya dole kayan da ake shigo da su daga waje farashinsu dole ya tashi, haka ma na gida saboda yadda buƙatarsu za ta ƙaru.

Dr Muhammad Shamsudden, ya ce wani daliin da ke sa farashin kaya ya rinka hawa shi ne kara kudaden haraji da ake yawan yi dama kirkiro sabbin haraji.

Sai dai matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na cire harajin shigo da kayan abinci zai iya yin tasiri wajen haifar da rahusar kayayyaki musamman ma na abinci.

Amma masana na ganin sai gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don magance yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa.