Dalilin da ya sa tattalin arziƙin Najeriya ya shiga mummunan hali

...

Asalin hoton, GIFT UFUOMA/BBC

Najeriya a halin yanzu na fuskantar taɓarɓarewar tattalin arziƙi mafi muni wanda ke haifar da wahalhalu sannan yake fusata al'ummar ƙasar..

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, ta shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar a ranar Talata, inda ta buƙaci gwamnati ta ƙara ɗaukar matakai.

Adadin kuɗin litar man fetur ya karu fiye da sau uku fiye da yadda ya yi watanni tara da suka wuce, yayin da farashin kayan abinci kamar shinkafa ya rubanya fiye da ninki biyu a shekarar da ta gabata.

Waɗannan abubuwa guda biyu sun nuna irin matsalolin da ‘yan Najeriya da dama ke fuskanta ganin yadda albashi bai yi daidai da yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ba.

Kamar ƙasashe da dama, Najeriya ta fuskanci taɓarɓarewar tattalin arziki a shekarun baya-bayan nan, amma kuma akwai wasu batutuwan da suka shafi ƙasar, waɗanda wani ɓangare na sauye-sauyen da shugaba Bola Tinubu ya gabatar a lokacin da ya hau mulki a watan Mayun da ya gabata suka ƙara haddasa taɓarɓarewar tattalin arziƙin ƙasar..

Girman lalacewar tattalin arziƙin Najeriya

Gabaɗaya, hauhawar farashin kayayyaki na shekara-shekara, wanda shi ne matsakaicin adadin yadda farashi ke tashi, yanzu ya kusan kaiwa kashi 30 cikin 100 - adadi mafi girma cikin kusan shekaru 30. Farashin abinci ya karu har ma fiye da kaso 35.

Sai dai kuma, mafi ƙarancin albashin wata-wata, wanda gwamnati ta ƙayyade, wanda kuma ya kamata dukkan ma’aikata su kiyaye, bai canza ba tun shekarar 2019, inda aka sanya shi a kan Naira 30,000, wato dala 19 kacal kenan a farashin canji a halin yanzu.

Mutane da yawa suna fama da yunwa inda suke ririta abincin da suke da shi ko kuma neman mafita ta hanyar amfani da wanda ke da farashi mai rahusa.

A arewacin ƙasar, yanzu haka wasu na cin shinkafar da wanda kamfani ke zubarwa kuma ake amfani da su a matsayin abincin kifi.

Bidiyoyin da aka watsa a kafofin yaɗa labarai suna nuna yadda wasu ke rage sanwar abincin da suke ci.

Wani bidiyo ya nuna yadda wata mata ke yanka kifi zuwa gunduwa tara maimakon huɗu zuwa biyar yadda ya kamata.

An ji ta tana cewa burinta shi ne ta tabbatar da danginta za su iya cin kifi a kalla sau biyu a mako.

Me ke janyo taɓarɓarewar tattalin arziƙin Najeriya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Hauhawar farashin kayayyaki ya yi tashin gwauron zabi a kasashe da dama, yayin da farashin man fetur da sauran kuɗaɗe suka tashi sakamakon yaƙin Ukraine.

Sai dai kuma ƙoƙarin da shugaba Tinubu ya yi na gyara tattalin arzikin kasar ya kara ta'azzara lamarin.

A ranar da aka rantsar da shi watanni tara da suka gabata, shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur.

Ƙarancin farashin man fetur a tarihi a Najeriya mai arziƙin man fetur ya dade yana zama alfanu ga ‘yan ƙasar amma kuma ya haifar da tabarbarewar tattalin arzikin ƙasar.

A rabin farkon shekarar 2023, tallafin man fetur ya kai kashi 15 cikin 100 na kasafin kudin ƙasar, wanda ya zarce yawan kudaden da ake kashewa a fannin lafiya da ilimi.

Shugaba Tinubu ya ce za a iya amfani da wadannan kuɗaɗe yadda ya kamata a wasu wurare.

Sai dai kuma, hauhawar farashin man fetur da ya biyo bayan cire tallafin ya haifar da tabarbarewar tattalin arziki, lamarin da ya haifar da tashin gwauron zabi na sauran kayyayaki.

Wani masani kan harkokin kudi, Tilewa Adebajo ya danganta hauhuawar farashin kayan masarufi da cewa abu ne da Tinubu ya gada daga magabacinsa Shugaba Muhammadu Buhari.

Adebajo ya bayyana shirin BBC cewa, gwamnatin da ta shude ta nemi rancen dala biliyan 19 daga babban bankin ƙasar na gajeren lokaci, wanda banki ya buga kudin da hakan ya janyo hauhawar farashin man fetur.

Mene ne ya faru da naira?

Tinubu ya kuma kawo karshen daidaita darajar naira da dala inda ya bar ta kasuwa ta yi halinta. Babban bankin dai ya kashe kudade masu yawa don kula da matakin.

Amma kuma wannan matakin ya saka darajar Naira ta durƙushe inda a yanzu ta kai matsayin da ba a taba ganin irinsa ba a makon jiya.

A watan Mayun da ya gabata, Naira 10,000 za ta sayi dala 22, yanzu dala 6.40 ne kacal naira 10,000 za ta iya saya.

Sakamakon Naira ba ta da daraja, dukkan farashin kayayyakin da ake shigar da su kasar sun tashi.

Yaushe al'amura za su warware?

Yayin da ake ganin da wuya shugaba Tinubu ya janye matakin da ya dauka kan batun tallafin man fetur da kuma Naira, wanda a cewarsa za a samu sakamako mai dorewa ta yadda tattalin arzikin Najeriya zai kara karfi, gwamnati ta bullo da wasu matakai na rage radadin da al'ummar ƙasar ke ciki.

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya sanar da kafa hukumar da ke kula da farashin kayan abinci.

Gwamnatin ta kuma umarci rumbunan ajiyar hatsi na kasa da ya raba tan 42,000 na hatsi da suka haɗa da masara da gero.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnati ta ce tana raba tallafi ga talakawa da marasa galihu ba.

Sai dai ƙungiyoyin kwadago sun sha sukar tsarin raba abinci da gwamnatin ke yi, suna masu cewa yawancin rabon ba ya kai wa ga iyalai marasa galihu.

Gwamnatin ta kuma ce ta na haɗa kai da masu noman shinkafa don ƙara samun abincin a kasuwanni kuma an umurci jami’an kwastam da su sayar da buhunan hatsin da suka kama a farashi mai rahusa a babban birnin Legas.

To sai dai yayin sayar da kayan abincin an samu turmutsitsi har abin ya kai ga mutuwar mutane bakwai, kamar yadda kafafen yada labarai na ƙasar suka ruwaito. Yanzu dai an dakatar da sayar da kayan abincin a farashi mai rahusa.

An kama kayan abincin ne a ƙarƙashin gwamnatin da ta gabata, wadda ta haramta shigar da shinkafa daga ƙasashen waje domin ƙarfafa gwiwar manoman cikin gida amma an ɗage haramcin a shekarar da ta gabata a kokarin rage farashin shinkafar amma saboda faduwar darajar naira, hakan bai yi tasiri ba.

Kusan magidanta miliyan 15 matalauta ne ke karbar tallafin kuɗi na naira 25,000 duk wata, amma a kwanakin nan, ba a samu labarin ana biyan su ba.