'Farashin kayan abinci zai ci gaba da tashi a Najeriya'

Kayan Abinci

Asalin hoton, Getty Images

An yi hasashen ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci na yau da kullum da aka saba da su, kamar shinkafa da masara da gero, a Najeriya da sauran ƙasashe da dama a yankin Afirka ta Yamma a shekarar nan.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani rahoto mai taken “Kasuwancin Yankin Afirka ta Yamma'' wanda hukumar abinci da aikin gona ta duniya FAO ta fitar.

Rahoton ya danganta lamarin da wasu abubuwa da suka haɗar da raguwar samar da kayayyaki, da takunkumin kasuwanci da rashin tsaro da karyewar darajar kuɗaɗe.

Ya kuma yi gargaɗin cewa wannan na iya haifar da ƙalubale ga samun abinci da wadatar shi a yankin, abin da ke buƙatar a dauki matakin gaggawa.

Kayan abinci

Asalin hoton, Getty Images

Bugu da ƙari, rahoton ya bayyana cewa, yadda farashin kayan yake a yanzu, ya zarce yadda aka saba gani cikin shekaru biyar a fadin yankin abun da bai rasa nasaba da matsalolin da aka lasafta a sama.

“Kazalika hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya na ci gaba da karuwa a duk shekara, sai dai lamarin ya kara ta’azzara sakamakon cire tallafin man fetur’’ in ji rahoton.

Ana hasashen cewa farashin zai ci gaba da karuwa, kasancewar babu wani mataki da aka dauka na magance wadannan matsaloli, da suka hadar da raguwar samar da kayayyaki, takunkumin kasuwanci, da tasirin yanayin kasa a duniya.

Me masana ke cewa?

Noman Rani

Asalin hoton, Getty Images

Dakta Abubakar Sulaiman, shine mataimakin shugaban hukumar abinci ta duniya a Najeriya, ya shaida wa BBC Hausa cewa baya ga matsalolin da rahoton ya ambato, akwai kuma matsin tattalin arziki, da talauci.

''Kwanakin baya a watan Oktoba na bara mun fitar da rahoton cewa mutum miliyan ashirin da biyar za su fuskanci karancin abinci a Najerya, a wannan shekara ta 2024'

Ya kara da cewa dole ne a fadada harkokin noma ta yadda manoma za su koma bakin aiki su yi noma da kayayyakin noma na zamani, ta yadda za a samu yabanya mai kyau''

''Hakan na nufin sai an samar da takin zamani, da iri, sannan a tari noman rani na wannan shekara, kuma a yi shiri na matsakaici da dogon zango don inganta noman ranin ba wai kawai na wannan shekara ba'' in ji masanin.

Matsalar tsaro dai na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da rashin noma a Najeriya musamman a arewacin kasar da aka fi yin noma, sakamakon matsalar yan bindiga da ke hana manoman zuwa gonakinsu, a wasu wuraren kuma suka tursasa biyar haraji.