Yadda farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a Najeriya

kayan abinci

Asalin hoton, Getty Images

Kwararru a fannin tattalin arziƙi a Najeriya sun nuna damuwa fara kan sabon rahoton Bankin Duniya da ya yi gargaɗi cewa mutum miliyan bakwai sun sake faɗawa talauci a bara kawai saboda ƙaruwar hauhawar farashi a ƙasar.

Bankin ya ce a cikin watan Afrilun da ya wuce an samu hauhawar farashi mafi yawan da ba a taɓa gani ba a cikin shekara huɗu.

Rahoton na Bankin Duniyar ya yi nuni da abin da ya kira da fitattun garanbawul na gwamnati, da nufin shawon kan tasirin anobar cutar korona da kuma tallafawa wajen farfado da tattalin arziki, cikin su har da matakan rage tallafin man fetur, da daidata farashin wutar lantarki.

Dukkansu kuma in ji rahoton don bunkasa kafofin samun kudin shiga da nufin aiwatar da ayyukan da za su inganta rayuwar talaka ne.

Sai dai a tattaunawar su da BBC, wani masanin tattalin arziki a Najeriya Dakta Mohammed Shamsuddeen na Jami'ar Bayero ta Kano a arewacin kasar ya ce lamarin ba haka yake ba.

''Domin kuwa tuntuni dama hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar da bayanai cewa hauhawar farashi har ya haura kaso 18 bisa 100 a Najeriya,'' in ji Dakta Shamsuddeen.

Ya kuma kara cewa: ''Kuma ma dama ga mai bibiyar al'amura ya san cewa dole za a kai wannan matsayi saboda dokokin tattalin arziki da Najeriya ta riƙa yi daga baya-bayan nan da kowa ya san cewa ba za su amfana wa talaka ba.''

A nan in ji masanin tattalin arzikin yana nufin canza taswira ko fuskar tattalin arziki daga inda gwamnati ke da ƙarfin fada a ji da yawa a harkar tattalin arziki ya zuwa zare hannun gwamnati daga kusan komai na tattalin arziki.

BBC Hausa ta binciki yanayin farashin kayayyakin abinci da aka fi amfani da su a ƙasar, amma ta duba farashin jihar Kano ne duba da cewa ita ce cibiyar kasuwanci ta arewacin Najeriya.

Shinkafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shinkafa ce nau'in abincin da aka fi ci a Najeriya

Ga farashin wasu daga cikin kayayyakin abinci a arewacin Najeriya:

  • Shinkafa 'yar gida 23,000 kilo 50
  • Gero buhu 22,700
  • Masara buhu 22,500
  • Dawa buhu 22,700
  • Shinkafa 'yar waje 28,000 kilo 50
  • Semo buhu 4,000
  • Man gyada lita 25 22,000
  • Indomie 3,500
  • Spaghetti katan 4,300

Ga kuma farashin wasu kayayyakin abinci a shekarar 2017 da shi ma BBC Hausan ce ta yi bincike tare da yin labarin yadda Hauhawar farashi ta sa ƴan Najeriya suka ɗanɗana kuɗarsu a wancan lokacin.

Farashin wasu abubuwa a watan Janairun 2016 zuwa Janairun 2017

  • Buhun shinkafa babba N8000 - N19,500
  • Buhun Semovita N1,300 - N3000
  • Buhun fulawa N6,000 - N12,000
  • Kwanon dawa - N140 - N600
  • Kwanon wake N400 - N800
  • Kwanon sikari N400 - N900
  • Indomie N35 - N70
  • Tulun gas matsakaici (kilo 12.5) N2,500 - N5,300
  • Litar kananzir N100 - N500

Ga wani rahoto na jihohin da suka fi tsadar kayan abinci da BBC Hausa ta yi duba a kai a watan Maris ɗin 2021.

Jihohin da kayan abinci suka fi tsada a Najeriya. A watan Fabrairun 2021. .
Wannan layi ne

Mece ce mafita?

Shi dai Bankin Duniya ya bayyana cewa Najeriya za ta tabbatar da rage hauhawar farashi ne ta hanyar:

  • Aiwatar da tallafa wa manufofin tallafa wa daidaiton harkokin tattalin arziki
  • da shigar da kowa cikin harkokin bunkasa kasa
  • da samar da aikin yi
  • da kuma kare magidanta masu karamin karfi daga tasirin hauhawar farashi
  • da saukaka hanyar samar wa da rance ga kanana da matsakaitan masu kananan sana'oi.
Bayanan bidiyo, Tsadar rayuwa: Shin N30,000 za ta iya magance matsalolinku

Amma kuma Dakta Shamsuddeen bai ga mifita ba game da wannan.

''Suna nufin a cigaba da tsarin da dauko da cire tallafin man fetur da yanzu ɗanyan mai ya zama dala 70 a kasuwar duniya kan wo wace ganga daya?''.

''Yanzu idan aka ce an cire tallafin man fetur a Najeriya da aka ce yanzu zai doshi kusan naira dari uku duk lita daya, ta ina wannan zai daidaita hauhawar farashi a kasar?" in ji shi.

Ta bangaren batun da Bankin Duniyar yayi na kare talaka daga matsalar da hauhawar farashin kayayyaki za ta iya janyo masa kuwa Dakta Shamsuddeen cewa ya yi akwai sake.

''To ta ina haka zai yiwu idan dai talaka zai sayi man fetur da tsada, zai biya kudin wuta da tsada, ya biya haraji mai yawa, sannan kuma kullum ana rage darajar Naira,'' ya ce.

Amma kuma ya bayyana abin da yake ganin ita ce kawai mafita da cewa kamata ya yi a duba hanyoyin magance matsalolin da kai tsaye su suka haifar da hauhawar farashin kayyakin tukuna.

''Na farko shi ne dole a dawo wa da Naira darajarta idan ana so farashi ya daidaita, saboda ko mun ƙi ko mun so Najeriya da sayen shigo da kayayyakin masarufi fiye da yadda take fitarwa waje,'' in ji masanin.

Ya kuma kara da cewa: ''Ko wace irin lalacewar darajar Naira lallai zai janyo hauhawar farashi, kuma hauhawar farashin nan dole zai ƙare a kan talaka tun da dai ba kyauta za a raba wa talaka ba''.

Wannan layi ne

Dole a sauƙaƙa makamashi

Mafita ta biyu da kuma da masanin ya bayyana ita ce dole ne ya zamana makamashi ya yi sauki a Najeriya, wato man fetur da kuma wutar lantarki.

''Wannan shi ne kaɗai da zai farfado da kananan masana'antu a cikin ƙasa, in ba haka ba kwalliya ba za ta biya kuɗin sabulu ba,'' ya ce.

Dakta Shamsuddeen ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da tsaro a ta yadda manoma za su samu damar komawa gonaki don yin noma, abin da a cewar sa hakan zai iya kawo saukin farashin kayan abinci wanda Bankin Duniyar ya ce ya haura kasha sittin cikin dari na dukkan karuwar farashin da ake fama da shi.

Wannan layi ne