Ko rikicin Ganduje da Abba ka iya mayar da Kano kan siyasar santsi da taɓo?

    • Marubuci, Usman Minjibir
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 5
Abba Kabir da Ganduje

Asalin hoton, Kano state govt

Zaman tankiya da faɗi-in-fada da gorantawa juna ne ke yin amo a makon nan tsakanin gwamnatin jihar Kano karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf da tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Da ma dai rikicin ya dade yana faruwa tsakanin bangarorin biyu duk da cewa sai a wannan makon ne ya fito fili, bayan da gwamnatin jihar Kano ta sanar da kafa wasu kwamitoci na binciken tsohon gwamnan da mukarrabansa.

A ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu ne gwamnatin ta Kano ta kafa kwamiti guda biyu domin binciken zarge-zargen rashawa da cin hanci da kuma rikicin siyasa tare da ɓatan jama'a da suka faru a karkashin gwamnatin Ganduje.

Da yake kaddamar da kwamitocin, gwamna Abba Kabiru Yusuf ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu a laifukan a tsawon shekaru takwas da su gabata.

Bayanai dai na nuna cewa gwamnatin Kano na zargin gwamna Umar Ganduje da gararumar kudi har dalar Amurka dubu 413 da kuma naira biliyan 1.38.

Rahotanni sun nuna cewa tuni kwamitocin suka fara tattara bayanai daga wurin shaidu da mutanen da zarge-zargen suka shafa kai tsaye.

Martanin Ganduje kan kwamitoci

..

Asalin hoton, Ganduje media aide

A ranar Juma'a 5 ga watan Afrilu, kwana daya bayan kafa kwamitocin guda biyu da gwamnatin Kano ta yi domin binciken gwamnatin Ganduje, sai shugaban jam'iyyar APC din, a wata sanarwa ya soki gwamnatin Kano.

"Maimakon ku mayar da hankali kan ayyukan raya kasa amma kun zauna kuna ta daukar matakan kawar da hankalin al'ummar jihar Kano daga irin gazawar gwamnatinku.

Hakan alamu ne da ke nuna ba ku yi wani abun a zo a gani ba da irin makudan kudin da ake antayowa jihar tun bayan hawan mulkin shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga watan Mayun 2023." In ji Ganduje.

Ya kara da cewa " saboda tsabar jahilci sun manta da shari'ar da wata babbar kotu ta yanke cewa zarge-zargen da suke tuhuma ta da su ba huruminsu ba ne. Ministan shari'a ne da hukumar EFCC kawai za su iya bincike kan wannan."

Daga karshe, tsohon gwamnan jihar ta Kano ya shawarci gwamnatin Abba Kabir Yusuf da " har yanzu ba ku makara ba wajen dorawa daga inda na tsaya domin na bar ayyukan alkairin da ya kamata ku koya."

Martanin Abba Yusuf ga Ganduje

..

Asalin hoton, KNSG

To sai kalaman na Ganduje ba su yi wa gwamna Abba Kabir dadi ba inda a ranar Lahadi ya yi kakkausan martani ga Abdullahi Umar Ganduje.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakain gwamnatin ta Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, gwamna Abba Kabir ya ce shekaru takwas da Ganduje ya yi yana mulki ba su tsinana wa jihar komai ba.

"Akwai badakala a zamaninka kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa mun hukunta ka tare da mukarrabanka bisa dangane da irin rashawa da cin hanci da suka zama alama a gwamnatinka." In ji gwamna Abba.

Daga karshe Abba Gida-Gida ya kara da cewa "watanni takwas da muka yi a mulki ya fi shekaru takwas na gwamnatinka mai cike da shiririta da rashawa."

Me hakan yake nufi?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masana kimiyyar siyasa irin su farfesa Kamilu Sani Fagge sun ce wannan sa-toka-sa-katsi da ke faruwa bai zo musu da mamaki ba kasancewar 'yan siyasa kan bi abokan hamayyarsu da kulli.

"Kamar yadda shi kansa tsohon gwamna Ganduje ya rinka yi wa abokan hamayyarsa a baya, to haka shi ma yanzu za a yi masa tunda dai 'yan siyasa suna da halayyar rukon wanda ya yi musu rashin kyautawa." In ji farfesa.

Dangane kuma da bincike da gwamnatin Kanon ta ce za ta yi wa tsohuwar gwamnatin da gwamna to farfesa ya ce:

"Yanayin dokokinmu da suka bai wa gwamnoni rigar sulke ta kariya daga tuhuma da hukuntawa. Domin idan dai har da za a hukunta gwamna idan ya yi laifi to ka ga babu wani gwamna kuma da zai zo nan gaba ya binciki wanda ya gada."

Abu na biyu kuma akwai shi ne shi wannan bincike idan dai za a yi shi ne domin ramuwar gayya to daga karshe za ka ga cewa ba al'umma ba za ta samu ci gaban da take nema kasancewar shugabanninsu sun karkata ne ga bincike don keta." In ji farfesa Kamilu Sani Fagge.

Siyasar santsi da taɓo

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce gaskiya idan dai aka tafi a haka ba na jin za a "haifa wa jihar Kano ɗa mai ido ta bangaren ayyukan ci gaban kasa sannan kuma zai rura wutar rikici tsakanin magoya bayan bangarorin biyu wanda hakan kan iya lalata yanayin zaman lafiyar jihar.

Mun ga rikicin siyasa da ya faru a baya a lokacin jam'iyyar PRP a nan Kano. Mun ga tashe-tashen hankula da kone-kone kuma tun wancan lokacin har kawo yanzu siyasar Kano na bin salon rigingimun wancan lokacin, inda aka rabu gida biyu wato santsi da tabo."

Tasirin Kwankwaso da Ganduje

..

Ku san za a iya cewa akwai hamayya mai zafi tsakanin gwamnatin Kano mai ci da wadda ta shude kasancewar sun kwashe shekaru da dama suna hamayya.

Abba Kabir Yusuf wanda tsohon ubangidan Ganduje, Rabi'u Musa kwankwaso ya mara wa baya ya yi takarar gwamna da Abdullahi Umar Ganduje mai zafi a 2019, inda hukumar zabe ta bayyana zaben da wanda bai kammala ba kuma ta shirya sabon zabe a wasu mazabu ciki har da mazabar Gama da ke karamar hukumar Nassarawa.

Kuma daga karshe Abdullahi Umar Ganduje ne ya samu nasarar lashe zaben kamar yadda hukumar zaben jihar ta sanar duk kuwa da cewa masu sa ido kan zaben na ciki da wajen Najeriya sun ayyana zaben da mai cike da rikici.

A 2023 kuma Abba Gida-Gida bisa goyon bayan Rabi'u Kwankwaso ya yi takara da Nasir Yusuf Gawuna wanda Ganduje ke mara wa baya, kuma daga karshe Abba Kabir ya samu nasara duk da cewa an kai ruwa rana a kotuna daban-daban kafin kotun koli ta ayyana Abba a matsayin wanda ya lashe zaben.

Masana kimiyyar siyasa irin su Farfesa Kamilu Fagge suna ganin irin yadda bangarorin biyu suka kwashe lokaci mai tsawo suna hamayya mai zafi ka iya yin tasiri wajen mayar da jihar Kano siyasar santsi da taɓo.

A yanzu haka dai za a iya cewa gida biyu ne da 'yan siyasa a Kano ke alfahari da su wato ko dai bangaren Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ko kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje ko kuma gida na uku na Sanata Ibrahim Shekarau.

Mece ce mafita?

Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce mafita daga wannan dambawar guda daya ce kacal wato 'yan siyasa su koma ga abun da ya sa suke mulki. Ma'ana talakawa.

"Talakawa sun zabe su ne domin su yi jagorancin da zai sama musu mafita ba wai ayi ta musayar yawu ba wanda babu inda zai kai gwamnatin da al'umma illa jefa su cikin rikici wanda daga karshe..." za a yi fargar jaji. In ji farfesa Fagge.