Me ya sa farashin man fetur ke hawa da sauka a Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Matatar man fetur ta Dangote a Najeriya ta sanar da rage farashin man da naira 100 kan kowace lita, wato daga naira 1,175 zuwa naira 1,075 kan kowace lita
Cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ranar Talata da daddare a shafinta na X ta bayyana cewa matakin na zuwa ne bayan saukar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Sanarwar ta ci gaba da cewa matatar ta yi ragin ne bisa tsarin sabon farashi da kamfanin ya fitar.
Matatar Dangoten ta kuma bayyana cewa matatar ta rage farashin man dizel zuwa naira 1,430 kan kowace lita daga tsohon farashin naira 1,620.
Matakin na zuwa ne karon farko cikin makonnin da aka ga tashin farashin man fetur a Najeriya.
Tun a makon da ya gabata ne matatar mai ta Dangoten ta sanar da ƙarin farasahin man, lamarin da ya haifar da ƙarin farashin a faɗin gidajen man ƙasar.
To ko me ya sa farashin man ke hawa da sauka a Najeriyar, wadda ta fi kowa arzikin man a nahiyar Afirka?
Dalilin tashin farashin man fetur a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Masana harkokin tattalin arziki na alaƙanta rage farashin Dangote da saukar farashin man a kasuwannin duniya, kamar dai yadda matatar ta bayyana.
A ranar Litinin farashin gangar mai ta kai kusan dala 120, saboda fargabar da ake da ita samun tsaikon jigilarsa daga yankin Gabas ta Tsakiya.
Tuni dai ƙasar Iran ta sanar da rufe mashigar Hormuz, wadda kashi 20 cikin 100 na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta wajen domin shiga kasuwannin duniya.
Ƙasar ta ɗauki matakin ne a matsayin martani kan hare-haren da Isra'ila da Amurka suke kai mata, waɗanda suka yi sanadin kisan jagoran addinin ƙasar da wasu manyan jami'an gwamnatin ƙasar.
Iran ɗin ta yi baranazar kai hari kan duk jirgin dakon mai da ya bi ta mashigar, lamarin da ya kawo tsaiko ga jigilar mai a yankin.
To sai bayan da a ranar Talata Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar cewa an kusa kawo ƙarshen yaƙin, an samu faɗuwar farashin man zuwa dala 90 a kasuwannin na duniya.
Me masana ke cewa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Ahmed Adamu ƙwararre kan makamashi da ke Abuja, Najeriya ya ce sauyawar farashin man fetur na da alaƙa da yadda kasuwar take ci da yadda take sauyawa lokaci zuwa lokaci.
Masanin harkokin makamashin ya ce duk lokacin da farashin ɗanyen mai ya tashi to litar man za ta tashi a gidajen mai, haka ma idan aka samu sauka a kasuwannin duniya, to farashin zai sauka a gidajen mai.
''Akwai alaƙa kai-tsaye, saboda idan farashi ya tashi a kasuwannin duniya, ita matata za ta yi ƙoƙarin samun kudin da za ta sayo mai tsada a kasuwa domin tacewa'', in ji shi.
Shi kuwa Dr Murtala Abdullahi Kwara, malami a tsangayar koyar da tattalin arziki na Jami'ar Usmanu Danfodiya da ke Sokoto, ya ce za a iya kasa dalilan tashi da saukar farashin man fetur a Najeriya zuwa gida biyu.
''Akwai matsaloli da suka keɓanta ga Najeriyar kaɗai, akwai kuma matsaloli na gama-gari da suka shafi kasuwannin duniya'', in ji shi.
Masanin tattalin arzikin ya kuma ce matsalar da ta haifar da tashin farashin a yanzu shi ne tashin farashin makamashin a duniya sanadiyyar yaƙin Iran.
''Ba Najeriya kaɗai matsalar ta shafa ba, har ma da sauran ƙasashen waje'', a cewar Malamin jami'ar ta UDUS.
Najeriya za ta iya hana tashin farashin?
Ƴan Najeriya na yawan kokawa cewa ya kamata gwmanatin ƙasar ta yi wani abu da zai hana tashin farashin man fetur a ƙasar, ko ma ta ƙayyade farashinsa.
To amma Farfesa Adamu ya ce babu wata rawa da gwamnatin Najeriya za ta taka domin hana tashi da saukar farashin man fetur a ƙasar.
''Saboda kasuwa ce gamammiya kuma haɗaɗɗiya a duniya, koda yaƙi ya shafe ko bai shafe ta ba , in dai ya shafi man fetur a duniya, to dole zai shafe ta'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa idan farashin ya tashi ta dalilin wani abu da ya faru a wata ƙasa guda ɗaya, to zai shafi tattalin arzikin kusa duka ƙasashen duniya.
Shi kuwa Dr Kwara cewa ya yi ragin da Dangoten ya yi ba mai ɗorewa ba ne.
''Ragin da Dangote ya yi siyasar kasuwancin gidan gida ne, ya yi hakan ne ya ga abokan huldarsa sun rage yawan man da suke saya a matatarsa, kuma yana tsoron kada ya rasa su, shi ya sa ya yi ragin'', in ji Dr Kwara.
Yaya kasuwar man fetur ke ci?
Farfesa Adamu ya ce ita kasuwa man fetur ba hajar ake kai wa kasuwar, a biya kuɗi a bayar da kayan ba.
''Wato abin da ake yi masu saye da sauyarwa ne za su haɗu galibi a shafukan yanar gizo, mai son saya zai nemi mai sayarwa, kuma akan yi cinikin ne watanni kafin haƙo man'', in ji shi.
Don haka ya ce kasuwar tana aiki ne kan tsammanin abin da zai faru a nan gaba, don haka idan aka samu ƙarancin man za a iya samun ƙari a cinikin da aka yi a baya.
Shi ma Dr Murtala Kwara ya ce ita kasuwar man fetur ba ta aiki da hasashe, tana aiki ne da haƙiƙanin halin da kasuwar ke ciki.
''A yanzu ƙididdigar da ake kai yanzu shi ne ba lallai sauka ba, saboda halin da ake ciki'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa idan ba yaƙin aka gama ba, babau wanda ya zai bayar da tabbacin saukar farashin man fetur a kasuwannin duniya.
Ya ce babban abin da ya haifar da matsalar shi ne rufe mashigar Hormuz, wanda hakan ya sanya wasu ƙasashen yankin Gulf suka sanar da dakatar da haƙo mai.












