'Yadda aka kashe rabin ƙawayena a harin bam kan makarantarmu'

Ƴan biyu Makarem da Ikram
Bayanan hoto, Tagwaye Makarem da Ikram na cikin ajujuwa daban-daban lokacin da harin ban ɗin ya fara.
    • Marubuci, Mohamed Mohamed Osman
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, El-Obeid, Sudan
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ranar ta kasance kamar kowace rana ga tagwaye Makarem da Ikram, 'yan shekara 18, a lokacin da aka kai wa makarantarsu harin bam a Sudan.

Makarem ta kasance tana cikin ajin Turanci yayin da Ikram take cikin ajin kimiyya, lokacin da suka ji wani "ƙara da ba mu saba ji ba" daga wajen makarantar.

Ashe harin bam ne ya auka wa makarantar.

Makarem ta bayyana cewa ta samu rauni a kafadarta lokacin harin, yayin da abokan karatunta da ke fikin ajin suka kwanta a ƙasa domin tsira, dukkaninsu suna ta ihu.

"Mun raɓe a gefen bango, inda wata daliba da ke tsaye a gabana ta sanya hannu a kafadarta ta ce, "Kafadarki na zubar da jini."

A cikin wannan rikici, 'yan biyun waɗanda ke a ajujuwa daban-daban, suka yi ƙoƙarin haɗuwa amma ba su yi nasara ba. Daga baya, Ikram ta fara neman Makarem ba tare da ta sani cewa an riga an kai ta asibiti ba.

Kamar sauran waɗanda suka jikkata, mazauna garin ne suka kai Makarem asibiti, waɗanda suka yi amfani da motoci da keken doki saboda babu motocin daukar marasa lafiya a birnin el-Obeid.

Daga bisani dai malamai da abokan ajin Makarem suka shawo kan Ikram da ta daina neman 'yar uwarta ta koma gida.

Sai da Makarem ta koma gida daga asibiti a ranar ne iyalanta suka gane cewa tana raye.

Ikram ta ce, "Na tsaya a wajen ƙofar gida ina jira na ga ko za ta dawo, a lokacin da na gan ta tana zuwa, kawai duka muka fashe da kuka."

Ikram dai ba ta ji rauni ba saboda tana cikin ɓangaren makarantar da harin bam ɗin bai yi wa illa ba.

"Harin bam ɗin ya bar Makarem da ƙaramin yanka da wasu tarkace a kanta.
Bayanan hoto, "Harin bam ɗin ya bar Makarem da ƙaramin yanka da wasu tarkace a kanta.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar malamin Turancin Makarem da Ikram da wasu ɗalibai 13 yayin da da dama suka jikkata a harin bam ɗin da aka kai makarantar ta Abu Sitta, da ke el-Obeid ta jihar Kordofan ta Arewa, a watan Agustan 2024.

Makarantar na da ɗalibai aƙalla kimanin 300.

Hukumomin yankin sun zargi dakarun RSF da ke yaƙi da rundunar sojin Sudan da kai harin bam ɗin.

RSF ba ta yi wani bayani kan wannan lamari ba kuma ba ta amsa buƙatar BBC ta yin tsokaci ba saboda ba a tabbatar ko harbin bam ɗin a makarantar da gangan aka kai shi ba.

Makarem ta ce an kashe rabin abokan karatunta a harin yayin da sauran rabin kuma sun jikkata sosai.

Baya ga raunata kafaɗarta, ta kuma samu rauni a kai, amma an sallame ta daga asibiti bayan samun taimakon farko.

Amma bayan 'yan kwanaki, bayan ta fara jin ciwon kai mai tsanani, aka yi mata ɗaukar hoton ƙwaƙwalwa wanda ya gano ƙaramin yanka daga bam a kan nata.

"Ina jin ciwo sosai wanda sai na sha magungunan rage zafi da dama nake jin sauƙi," in ji ta.

Taswirar Sudan, ciki har da birnin da aka kai harin bam, El-Obeid.
Bayanan hoto, Taswirar Sudan, ciki har da birnin da aka kai harin bam, El-Obeid.

Yaƙin basasa a Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 150,000 da kuma tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ƙasar na fuskantar rikicin jin-ƙai mafi muni a duniya.

Kimanin yara miliyan 13 daga cikin yara miliyan 17 waɗanda suka kai shekarun zuwa makaranta da suka rage a Sudan, ba sa zuwa makaranta, in ji MDD.

An rufe makarantar 'yan mata ta Abu Sitta na tsawon watanni uku bayan harin, yayin da ake gyara ta.

Makarem da Ikram sun ce a farko ba za su iya tunanin komawa wurin da aka kashe abokansu da malaminsu ba.

"Amma kuma da sauran abokaina suka zo suka ce min komai lafiya yanzu, sai na yanke shawarar zan koma," in ji Ikram.

Duk da haka, komawa makarantar na tunatar da su abubuwan da suka faru masu muni.

"Nakan rufe idona a hanyar zuwa aji don kada na kalli wurin da aka harba bam ɗin," in ji Ikram.

An riƙa bai wa wasu ɗaliban shawarwari domin kawar musu da damuwa lokacin da suka koma, in ji shugabar makarantar Iman Ahmed.

An kuma samar da gadaje da nas-nas a makarantar don bai wa ɗaliban da suka ji rauni damar rubuta jarabawa cikin kwanciyar hankali.

Duk da cewa har yanzu ana kai hare-hare da jiragen yaƙi marasa matuka a el-Obeid, ɗaliban makarantar suna wasa da dariya a filin makaranta lokacin da BBC ta kai ziyara a watan Disamba.

Ikram zaune a kuje waje
Bayanan hoto, Ikram ta ce takan rufe idonta a hanyar zuwa aji saboda kada ta kalli wurin da aka harba bam ɗin.

Amma har yanzu yaran da ke ƙoƙarin yin karatu a el-Obeid na fuskantar ƙalubale.

Birnin ya kasance a ƙarƙashin ikon RSF fiye da shekara ɗaya da rabi, har sai da rundunar sojin Sudan ta sake karɓar iko da shi a watan Fabarairun 2025.

Ko da yake yanzu an samu natsuwa kaɗan, makarantu da dama sun koma wuraren mafakar 'yan gudun hijira. El-Obeid na bai wa kusan mutum miliyan ɗaya da suka tsere daga gidajensu mafaka a wurare daban-daban, in ji kwamishinan agajin jin kai na jihar.

Ibtisam Ali, ɗaliba a wata makarantar sakandare da aka mayar wurin mafakar 'yan gudun hijira, ta ce ba za ta iya barin aji ba har sai a tashi daga makaranta a ranar saboda filin makarantar cike yake da ƴan gudun hijira "Ko zuwa bandaki ya zama matsala a gare mu," in ji ta.

Walid Mohamed Al-Hassan, ministan ilimi na jihar Kordofan ta Arewa ya ce kasancewar iyalan 'yan gudun hijira a makarantu ya haifar da matsaloli, ciki har da tsaftar muhalli, amma halin da yakin da ake yi ne ya jefa su a cikin wannan yanayi."

An rufe makarantar Abu Sitta school na tsawon watanni uku yayin da ake gyara bayan harin bam din.
Bayanan hoto, An rufe makarantar Abu Sitta school na tsawon watanni uku yayin da ake gyara bayan harin bam din.

'Ina da buri'

Duk da yaƙin da abubuwan da suka faru, Makarem da Ikram, waɗanda yanzu suna da shekara 19, suna da fata mai kyau game da makomarsu.

Ikram ta kammala karatunta na sakandare kuma yanzu tana karatun Turanci a jami'a a el-Obeid.

Mutuwar abokanta da malamarta sun ƙara mata ƙwazo wajen kammala karatunta.

Makarem na son ta zama likita kamar waɗanda suka kula da ita bayan raunin da ta samu.

Ta ci jarabawar sakandare amma ba ta samu makin da ake buƙata domin shiga karatun likitanci ba.

Tarkacen abubuwan da suke cikin kanta, wanda ba za a iya cirewa ta tiyata ba, ya sa karatun farko ya yi mata wahala.

Ta ce, "Nakan yi karatu na awa ɗaya sai na huta na awa ɗaya. Abun akwai matuƙar wahala."

Dr Tarek Zobier, likitan kwakwalwa a Sudan, ya ce irin tarkacen da ke cikin kanta yana bambanta daga mutum zuwa mutum. Wasu ba sa jin alamomi kuma za su iya rayuwa ba tare da tiyata ba. Amma idan alamomi sun fi tsanani, ana iya buƙatar tiyata.

Ga Makarem, ciwon ba ko da yaushe yake damun ta ba, sai dai ya fi tsanani a lokacin sanyi.

Ta dogara da magungunan rage radadi idan ta fara jin ciwo.

Ta yanke shawarar maimaita shekarar karshe a makaranta domin sake jarrabawa. Ta ce, "Ina da yaƙini zan iya samun makin da nake burin samu. Ina da buri a gaba."