Kun san abin da ya sa ɗan'adam ke yin kuka?

Asalin hoton, Bogdan Malizkiy via Getty Images
Muna yin kuka lokacin da muke cikin damuwa, ɓacin-rai ko kuma har da farin ciki.
Shin kun san cewa dangin ɗan'adam shi ne kaɗai aka fi sani da yin hawayen tausayi?
Yayin dabbobi da dama ke yin kuka domin nuna damuwa da suke ciki, ba su da ƙwaƙwalen da za su yi tunani har su yi hawayen tausayi.
Masana kimiyya sun san yadda hawaye ke aiki, sai dai me ya sa ɗan'adam ke yin kuka, kuma me ya sa ake hawayen tausayi - wannan na cikin abubuwan da ba a gama sani ba har yanzu.
Mene ne hawaye?
"Hawaye yana ɗauke da abubuwa guda biyar a cikinsa - sinadarai, ruwa da kuma sindarin protein," kamar yadda Dakta Marie Bannier-Helaouet, wata malama a cibiyar nazarin rayuwar ɗan'adam a Switzerland.
Ta faɗa wa BBC cewa duka waɗannan abubuwa na da dangogi daban-daban. Alal misali, sinadarin protein, suna kamar wasu abubuwa ne da ke maganin cutuka, yayin da sauran kuma ke da muhimmanci wajen kula da jiki.

Asalin hoton, janiecbros via Getty Images
Sannan akwai na'ukan hawaye guda uku.
"Akwai hawayen da ke kasancewa a gefen ido kowane lokaci. Hawaye ne da ke wanke ido," in ji masaniyar.
A ɗaya gefe kuma, akwai hawayen da ke fita lokacin da kwaro ko kura ya shiga cikin idon mutum.
Hakan na faruwa ne bayan wasu jijiyo sun aika sako.
Sakonni daga jijiyoyin na zuwa cikin wani yanki a ƙwakwalwa wanda yake kula da hawaye, bayan nan sai fitar hawaye ya ƙaru.
Hawayen tausayi
Nau'in kuka na uku shi ne - hawayen tausayi - a nan abubuwa ke ƙara yin tsarkakiya.
Ɓangaren da ke alamta jin tausayi na ƙwakwalwa na tattaunawa da da jijiyoyin ido, sai dai hakan na yiwuwa ne ta wata hanya mai tsarkakiya.
A cewar farfesa Ad Vingerhoets a Jami'ar Tilburg da ke Netherlands, ya ce yin kuka akai akai na nuna cewa akwai tausayi sosai a wajen mutum maimakon jin wani abu iri ɗaya kawai.
Ya bayyana cewa dalilan da ke sanya mu kukan tausayi na sauyawa yayin da muke ƙara tsufa.

Asalin hoton, Gpointstudio via Getty Images
Yayin da muke ƙara tsufa, kukan da muke yi na alaƙa da irin tausayi da muke ji - "ba wai kawai ga wahala da muke ciki ba, sai dai muna kuka ne kan irin wahalhalu da kuma raɗaɗi da sauran mutane ke ciki".
Vingerhoets ya bayyana cewa tausayi mai kyau - kamar wanda yake faruwa bayan ganin abu mai kyau ko kuma halittar Allah - shi ma kan ingiza hawaye.
Me ya sa ake yin kuka?
Mutane da dama na ruwaito cewa suna wartsakewa bayan yin kuka, sai dai akwai tababa a wajen masana kimiyya kan cewa ko wannan tasiri da gaske ne.
Lauren Bylsma, masaniya kan tunanin ɗan'adam a Jami'ar Pittsburgh da ke Amurka, ta kasance tana amfani da abubuwan da ke nuna yadda zuciya take aiki, wajen gano cewa ko kuka na sa mu ji daɗi.
Ta yi amfani da wasu na'urori wajen naɗar yadda zuciya ke bugawa, wanda zai ba mu damar sanin yadda sassan jikinmu ke aiki.
Bincikenta na farko ya gano cewa daf kafin mu fara kuka, wani abu na faruwa a cikinmu.
"Kuma bayan fara kuka nan ne ake ganin jiki ya kwanta wato komai ya daidaita", in ji ta - sakamakon wani ɓangare a cikin jiki da ke taimakawa wajen kwantar da hakali.
Sai dai masani Vingerhoets ya ce kuka kaɗai baya sa mu ji daɗi a kodayaushe, musamman idan muna da cutar damuwa ko kuma wasu matsaloli.

Asalin hoton, Xavier Lorenzo via Getty Images
Me ya sa wasu mutane suka fi kuka?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Maza kan yi kuka aƙalla sau ɗaya a wata, yayin da mata kuma ke kuka sau huɗu zuwa biyar, a cewar masaniya Bylsma.
Yayin da wannan zai iya kasancewa ɗabi'a da aka koya, masaniyar tunanin ɗan'adam ɗin ta ce saboda ganinsa da muke yi a wurin al'adu da dama, hakan na nuna cewa akwai wani abu.
"Alamu na nuna cewa mata sun fi ji ko kuma nuna tausayi, kuma ina ganin kuka na ɗaya daga cikin abubuwan," in ji ta. "Akwai wasu bambance babmbance da dama kamar halayya da kuma yanayin halittar jiki."
Bylsma ta ce babu wata hujja da ke nuna cewa girman sassan jiki a lokacin al'ada na shafar yadda muke kuka, sai dai ta ce mai yiwuwa yanayin jiki na taka rawa saboda bambanci tsakanin jinsi da kuma abubuwa kamar juna biyu da kuma tsufa.
"Mun kuma gano cewa mutanen da suka fi jin tausayi, su za su fi saurin kuka, saboda suna kuka ne kan ganin irin halin ƙunci da wasu mutane ke ciki," in ji Bylsma.
Gaba-ɗaya kuka na kasancewa ne kan yanayin shakuwa da mutane.











