Lokuta bakwai da aka ɓaɓe tsakanin 'ubangida da yaronsa' a siyasar Najeriya

Kwankwaso da Ganduje da kuma Abba

Asalin hoton, BBC Collage

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Nan gaba a yau ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sanar da komawa jam'iyyar APC a hukumance bayan raba gari da ubangidansa a siyawa, Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP.

A ranar Juma'a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar NNPP da aka zaɓe shi a karkashinta a shekarar 2023.

Gwamnan ya bayyana rikicin cikin gida da fifita ci gaban al'ummar jihar Kano a matsayin dalilansa na ficewa daga NNPP.

Tuni dai jam'iyyar ta yi masa martani, cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri'ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.

Ba wannan ne karon farko da aka samu sabani, wanda ya kai ga ɓaɓewa tsakanin ubangida da yaronsa a siyasar Najeriya ba.

Saɓani tsakanin ubangida da yaro a siyasar Najeriya abu ne da ya daɗe yana faruwa, inda akasari hakan ke faruwa bayan yaron ya hau mulki kuma ya fara ƙoƙarin cin gashin kansa.

Cikin wannan muƙala mun duba wasu muhimman lokuta da aka samu ɓaɓewar ubangida da yaronsa a siyasar Najeriya tun daga 1999 lokacin da ƙasar ta koma kan mulkin dimokraɗiyya a jamhuriya ta huɗu.

Kwankwaso da Ganduje

Kwankwaso da Ganduje

Asalin hoton, RABIUMUSAKWANKWASO

Ɗaya daga cikin raba garin siyasa da ya ɗauki hankali a siyasar Najeriya shi ne tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musu Kwankwanso da babban yaronsa a siyasa Abdullahi Umar Ganduje, wanda shi ma tsohon gwamnan jihar ne a yanzu.

Ganduje ya kasance tare da Kwankwaso lokacin da ya fara yin gwamnan Kano a 1999 a matsayin mataimakinsa.

Bayan da Kwankwaso ya sake komawa gwamnan Kano a 2011 ya sake ɗaukar Ganduje a matsayin mataimakinsa, kafin daga baya ya tsayar da shi takarar gwamnan bayan kammala wa'adinsa a 2015.

Ganduje ya zama gwamnan Kano inda ya yi wa'adi biyu tsakanin 2015 zuwa 2023.

Sai dai hawansa mulki da ɗan lokaci aka soma samun saɓani tsakanin jagororin siyasar Kanon biyu, inda kowa ya kama gabansa, har ma Kwankwaso ya fice daga APC ya koma PDP.

Kwankwaso da Abba Kabir

Kwankwaso

Asalin hoton, RABI'U MUSA KWANKWASO/X

Wannan ce rabuwar siyasa ta baya-bayan nan da ta ɗauki hankali tsakanin ubangida da yaronsa a siyasar Najeriya.

Tun a ƙarshen shekarar da ta gabata ne ake ta raɗe-raɗin cewa gwamnan Kano Abba Kabir, wanda aka zaɓa ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, zai koma APC.

Sanata Kwankwaso ne ya tsayar da Abba Kabir takara har sau biyu, da fari a 2019 ƙarƙashin PDP, bai yi nasara ba, sannan a 2023 a NNPP ya kuma ya yi nasara bayan kayar da Nasiru Gawuna na APC mai mulkin jihar a lokacin.

Abba Kabir ya kasance kwamishinan ayyuka na musamman ƙarƙashin gwamnatin Kwankwaso a 2011.

El-Rufai da Uba Sani

El-Rufai da Uba Sani

Asalin hoton, facebook/Multiple

Wata rabuwar siyasa da ta bai wa masu bin al'amuran siyasa da dama mamaki ita ce tsakanin tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da gwamnan jihar mai ci Sanata Uba Sani.

Wannan rabuwa za a iya bayyana ta da ɓaɓewa tsakanin aminan siyasa biyu ganin irin rawar da Nasiru El-Rufa'i ya taka wajen lashe zaɓukan da Uba Sani ya yi takara.

Baya ga faɗi tashin da El-Rufai ya yi wajen ganin Uba Sani ya zama sanata, shi ne kuma ya yi shige da ficen tabbatar da Uba Sani a matsayin ɗan takarar gwamnan Kaduna a zaɓen 2023, inda ya lashe zaɓen, kuma El-Rufa'i ya miƙa masa mulkin jihar ta Kaduna.

Sai dai tafiyar ba ta yi nisa ba, bayan fara mulkin Uba Sani an fara samun rashin jituwa tsakaninsa da aminin nasa, lamarin da har ya kai ga El-Rufai ficewa daga jam'iyyar APC tare da komawa SDP kafin daga baya ya koma ADC.

Tinubu da Ambode

Shugaban Najeriya Bola Tinubu wanda a baya shi ne ubangidan siyasar jihar Legas da ke yankin kudu maso yammacin ƙasar, ta taɓa samun saɓanin siyasa tsakaninsa da ɗaya daga cikin manyan yaransa.

A shekarar 2015 ne Tinubu ya tsayar da Akinwumi Ambode takarar gwamnan jihar Legas a jam'iyyar APC ya kuma yi nasara.

To sai dai bayan ɗarewarsa kujerar gwamnan jihar - wadda ta fi kowace yawan al'umma a ƙasar - sai aka fara samun saɓani a tsakani.

Lamarin da har ya kai ga Tinubu janye goyon bayan da yake bai wa gwamnan, inda zaɓen 2019 ya sauya shi a matsayin ɗan takarar APC kuma ya gaza cin zaɓen fitar da gwani.

Wike da Fubara

Fubara da Wike

Asalin hoton, OTHERS

Rikicin da ya shiga tsakanin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da ubangidansa tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike.

Da taimakon Wike ne Fubara ya samu tikitin takarar gwamnan jihar a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a jihar - mai arzikin man fetur - amma sai daga baya saɓani ya shiga tsakaninsu.

Saɓani tsakanin ƴansiyasar biyu ya jefa jihar cikin rikicin siyasa, lamarin da har ya kai ga Shugaba Tinubu ɗaukar matakin dakatar da Gwamna Fubara tare da ayyana dokar ta-ɓaci a jihar a shekarar da ta gabata.

A ƙarshen shekarar 2025 ne Fubara ya bayyana ficewarsa daga PDP zuwa APC, wani abu da ya ƙara fito da ɓarakar da ke tsakaninsa da Wike- wanda shi ne ministan Abuja.

Obasanjo da Atiku

Atiku Obasanjo

Asalin hoton, Abdurrasheeth/FB

Raba gari tsakanin Obasanjo da Atiku na daga cikin farko-farkon saɓanin siyasa da aka gani tsakanin ubangida da yaronsa a jamhuriya ta huɗu.

A shekarar 1999 Obasanjo ya ɗauki Atiku matsayin mataimakinsa, lokacin da PDP ta tsayar da shi takarar shugaban ƙasa.

Sun yi aiki tare har ƙarshen wa'adin mulkinsu na biyu a 2007.

To sai dai saɓani ya kunno kai tsakaninsu a ƙarshen wa'adin mulkinsu bayan da Obasanjo ya buƙaci yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska, domin samun damar tsayawa takara a wa'adi na uku.

Atiku Abubakar ya kasance kan gaba a yaƙi da wannan buƙata ta Obasanjo, lamarin da ya dagula dangantar da ke tsakanin mutanen biyu.

Wike da Amaechi

Jihar Rivers da ke kudancin Najeriya ta kasance tamkar jihar Kano a arewacin ƙasar, a fagen siyasa, inda rikicin siyasar jihohin ke ɗaurkar hankalin ƴanƙasar.

An samu saɓanin siyasa tsakanin Rotimi Amaechi da Nyesom Wike waɗanda duka a yanzu tsoffin gamnonin jihar ne.

A lokacin mulkin Amaechi tsakanin 2007 zuwa 2015, ya yi aiki da Nyesom Wike , wanda a lokacin ya naɗa shi shugaban ma'aikata, daga 2007 zuwa 2011, kafin a naɗa shi ƙaramin ministan ilimi.

Amaechi ya taka rawar gani don ganin Wike ya samu takarar gwamnan jihar, da kuma nasararsa a ƙarƙashin jam'iyyar PDP.

To sai dai saɓani ya shiga tsakaninsu, lamarin da har ta kai ga Amaechi ya fice daga PPD tare da komawa APC.

Wasu saɓanin siyasar da ba su fito fili ba

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Baya da waɗannan da suka fito fili kuwa akwai wasu saɓanin siyasa da aka samu tsakanin ubangida da yaronsa a siyasar jihohinsu.

Daga ciki har da na tsoffi gwamnonin jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa da Aliyu Magatakarda Wamakko, da wanda aka samu tsakanin tsoffin gwamnonin jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima da Mahmudu Aliyu Shinkafi.

Haka ma akwai wanda aka samu tsakanin tsoffion gwamnonin jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje da Sanata Ibrahim Dangwambo.

Sai wanda aka samu tsakanin tsoffin gwamnonin jihar Rivers, Peter Odoli da Nyesom Wike.

Sannan kuma da wanda aka samu tsakanin tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon ministan taro, Mohammed Badaru Abubakar da gwamnan jihar mai ci Mallam Umar Namadi, kodayake saɓaninsu bai fito fili ba, ya fi zafi tsakanin yaransu.

Ga kuma yanzu an ga Atiku ya koma jam'iyyar haɗakar ADC, yayin da babban yaronsa a jiharsa ta Adamawa, Umaru Fintiri wanda shi ne gwamnan jihar, ke jam'iyyar PDP, wani abu da ke nuna cewa a yanzu ƴansiyasar biyu ba sa tare, kodayake ɓarakar ba ta fito ba.