Wane tasiri gwamnoni ke yi wajen cin zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya?

Asalin hoton, Sanata Uba Sani
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan yadda wasu gwamnonin jam'iyyun hamayya ke tururuwar komawa jam'iyyar APC mai mulki.
Wasu na ganin gwamnonin na komawa ne domin kwaɗayin samun tikitin takarar kujerunsu da kuma yiwuwar sauƙin cin zaɓukansu.
To sai dai wasu na zargin cewa jam'iyya mai mulkin ce ke zawarcinsu da nufin samun sauƙin lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Zargin da APC ta sha musantawa a lokuta daban-daban.
To amma gwamnonin na da tasiri wajen nasarar shugaban ƙasa a zaɓukan Najeriya?
APC na da gwamnoni 29 cikin jihohi 36

Asalin hoton, AbdurRahman Abdurrazaq/X
Ya zuwa yanzu jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya na da gwamnoni 28 cikin jihohin ƙasar 36.
Gwamnoni bakwai ne dai suka koma APC bayan zaɓensu a jam'iyyar PDP mai hamayya.
Gwamnonin da suka sauya sheƙar zuwa APC sun haɗa da Sheriff Oborevwori na jihar Delta, da Umo Eno na Akwa Ibom da Peter Mbah na Enugu da Douye Diri na Bayelsa.
Sauran su ne Siminalayi Fubara na jihar Rivers da Agbu Kefas na Taraba sai kuma Caleb Mutfwang na jihar Filato.
Haka kuma jam'iyyar na da gagarumin rinjayen da za ta iya zartar da muhimman dokoki a majalisun dokokin ƙasar biyu, wani abu da ke ƙara nuna ƙarfin jam'iyyar a fagen siyasar Najeriya.
Tasirin gwamnoni a siyasar Najeriya

Asalin hoton, others
Gwamnonin dai na da matuƙar tasiri a siyasar Najeriya, inda suke taka rawar gani a fagen siyasa da ma ɗaukar matakai a ƙasar.
Tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimokraɗiyya a jamhuriyya ta huɗu a shekarar 1999 ne ƙarfin gwamnoni ke ci gaba da ƙaruwa a fagen siyasar ƙasar.
Ƙungiyar gwamnoni Najeriya tana da ƙarfi matuƙa, inda har ta kai takan taka rawa wajen tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa.
Idan ana batun ƙarfin iko, yawanci an fi mayar da hankali a kan ƴan majalisa, waɗanda ake tunanin suna yadda suke so a siyasar Najeriya.
Sai dai ganin yadda gwamnonin jihohi suke iya kayar da ɗan majalisa ko sanata idan suna saɓani da shi, duk kuwa da ƙarfinsa a majalisa, sai tunani ya fara sauyawa.
Wannan ya ƙara fitowa bisa la'akari da yadda gwamnoni da dama idan sun kammala wa'adin mulkinsu, sukan zaɓi tafiya majalisar dattawa, kuma da wahala a kayar da gwamnan a zaɓen fid-da-gwani.
Wace rawa gwamnoni ke takawa a zaɓen shugaban ƙasa?

Asalin hoton, Ahmad Aliyu Sokoto/X
Farfesa Yahaya Tanko Baba, malami a sashen nazarin kimiyyar siyasa na jami'an Usman Danfodiyo da ke Sokoto ya ce gwamnonin na taka muhimmiyar rawa wajen nasarar shugaban ƙasa a zaɓukan Najeriya, musamman a shekarun da suka gabata.
''Gwamnoni na da tasiri sosai idan aka yi la'akari da yadda ake gudanar da zaɓuka a Najeriya'', in ji shi.
Malamin Jami'ar ya ce idan aka duba yadda tsarin siyasar Najeriya yake na amfani da kuɗi da ƙarfin mulki a lokutan zaɓe, za a tabbatar da tasirin gwamnonin a nasarar zaɓe a jihohinsu.
''Sukan yi amfani da kuɗi ko jami'an tsaron da ke ƙarƙashin ikonsu wajen tursasa wa ƴan hamayya, da sauran al'umma'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Masanin siyasar ya ce ƴan adawa suna fuskantar barazana sosai a jihohin da ba su da mulki.
Ya ƙara da cewa hakan ce ta riƙa faruwa musamman tun bayan komawa jamhuriya ta huɗu.
'Da alama ta sauya zani'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
To sai dai Farfesa Tanko ya ce da alama yanzu an fara samun sauyi a zaɓukan 2023.
''Domin kuwa a zaɓen 2023 da ya gabata mun ga yadda Peter Obi duk da rashin gwamna da jam'iyyarsa ke da shi, sai da ya yi nasara a jihohin ƙasar fiye da 10, kuma tazarar ƙuri'un da ke tsakaninsa da na biyu bai kai ƙuri'a miliyan guda ba'', kamar yadda ya bayyana.
Ya ci gaba da cewa sakamakon zaɓen 2023 ya nuna cewa ba lallai ba ne a yanzu gwamnoni su ci gaba da yin tasiri kamar yadda suka a zaɓukan baya ba.
''Idan ka lura da ƙuri'un da Peter Obi ya samu a 2023 za ka sha mamaki domin kuwa hatta jihar Legas ta Tinubu ya fito inda kuma APC ke mulki, jam'iyyar LP ce ta yi nasara a jihar'', in ji shi.
''Ya ci jihohi masu yawa a kudu maso kudanci da kudu maso gabas da ma wasu na arewaci, wanda hakan alama ce da ke nuna cewa tasirin gwamnoni ya ragu ko ma ya daina aiki a zaɓen shugaban ƙasa'', in ji shi.
Don haka ne masanin siyasar Najeriya ya ce a yanzu yadda siyasar ƙasar ke nunawa babu wani tasiri mai ƙarfi da gwamnonin za su yi wajen cin zaɓen shugaban ƙasa.
''Ko da duka jihohin ƙasar 36 na ƙarƙashin jam'iyyar APC, a yanzu ba za mu iya cewa za ta lashe zaɓe ba'', in ji shi.
Mene ne zai yi tasiri a zaɓen 2027?
Farfesa Tanko ya ce manyan abubuwa guda biyu ne za su yi tasiri a zaɓen 2027, kuma su ne za su ja hankali a yaƙin neman zaɓe mai zuwa, kamar yadda ya yi bayani.
''Abubuwan su ne tsaro da tattalin arziki, waɗannan su ne suka fi addabar ƴan Najeriya a halin yanzu'', kamar yadda ya bayyana wa BBC.
Malamin jami'ar ya ce rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta shi ne ya fi ci wa ƴan ƙasar tuwo a ƙwarya.
''Musamman yanzu da aka samu katsalandan daga ƙasar Amurka, mafi yawan ƴan ƙasar ba su gamsu da wannan katsalanda ba, kuma wannan zai yi matuƙar tasiri a yaƙin neman zaɓen shekara mai zuwa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Haka ta fuskar tattalin arzikin masanin siyasar ya ce wasu manufofin tattalin arziki da gwamnati ta ɓullo da su ba su yi wa ƙasar daɗi ba, kuma za su ja hankali a lokacin yaƙin neman zaɓe.
''Akwai batun cire tallafin man fetur da faɗuwar darajar naira da ɓullo da sabbin dokokin harajin nan da suka fara aiki yanzu, za su tsananta rayuwar al'umma, kuma za su ja hankali sosai tare da yin tasiri a zaɓe mai zuwa'', in ji malamin jami'ar.










