Abin da ya sa gwamnoni ke da tasiri a siyasar Najeriya

Taron ƙungiyar gwamnonin Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Governors’ Forum

Bayanan hoto, Wani taron ƙungiyar gwamnonin na baya-bayan nan
    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 4

Maslahar da gwamnonin PDP suka samar a kan rikicin da ya so raba kan jam'iyyar, na cigaba da jan hankali.

Jam’iyyar ta ɗauki hanyar darewa gida biyu ne, inda ɓangarori biyu suka dakatar da juna, tare da sanar da wani a matsayin shugaban jam’iyyar na riƙo a madadin shugabanta na yanzu, Iliya Damagun.

Sai dai bayan gwanonin sun sanya baki a lamarin, sai suka soke dakatarwar da aka yi wa dukkan ɓangarorin, sannan suka ce kowa ya koma matsayinsa, wanda hakan ke nufin Damagun ne zai cigaba da shugabantar jam’iyyar.

Tun bayan da Najeriya ta dawo mulkin dimokraɗiyya a jamhuriyya ta huɗu a shekarar 1999 ne ƙarfin gwamnoni ke ci gaba da ƙaruwa a fagen siyasar ƙasar.

Ƙungiyar gwamnoni Najeriya tana da ƙarfi matuƙa, inda har ta kai takan taka rawa wajen tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa.

Idan ana batun ƙarfin iko, yawanci an fi mayar da hankali a kan ƴan majalisa, waɗanda ake tunanin suna yadda suke so a siyasar Najeriya.

Sai dai ganin yadda gwamnonin jihohi suke iya kayar da ɗan majalisa ko sanata idan suna saɓani da shi, duk kuwa da ƙarfinsa a majalisa, sai tunani ya fara sauyawa.

Wannan ya ƙara fitowa bisa la'akari da yadda gwamnoni da dama idan sun kammala wa’adin mulkinsu, sukan zaɓi tafiya majalisar dattawa, kuma da wahala a kayar da gwamnan a zaɓen fid-da-gwani.

Ko kuma su tsayar da wasu ƴan takarar, su kayar da waɗanda ba sa so domin tsayawa takara.

Ƙarfin ikon gwamnoni illa ce ga dimokraɗiyya?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A game da yadda ake zargin cewa dole yadda gwamnonin suka dama a siyasa, haka za a sha, Farfesa Abubakar Umar Kari, malamin nazarin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja ya bayyana wa BBC cewa haka lamarin yake.

"Musamman a wannan jamhuriya ta huɗu. Gungun gwamnoni suna da matuƙar ƙarfin faɗa a ji, kusan ma za a iya cewa su ne suke da ƙarfi fiye da kowane gungun ƴan siyasa''.

''Wannan kuma ya fara fitowa fili ne ina ga tun a wuraren 2002 a lokacin da ake shirin zaɓe na biyu, inda gwamnonin PDP na lokacin suka taka rawa wurin yanke waɗanda za su yi wa jam’iyyar takara a matakai daban-daban.

Ya ce tun lokacin da suka kafa ƙungiyar gwamnoni kusan babu wani abu da za a yi, a samu nasara idan babu su a ciki.

"Wannan ya jawo abubuwa da dama yawancinsu marasa kyau, waɗanda suke da illa ga ita kanta dimokuraɗiyyar. Sun tattara iko da yawa, kuma duk lokacin da wani ya tattara iko da yawa, dole za a yi ɓarna. Kuma abin da yake faruwa ke nan."

Farfesa Kari ya ƙara da cewa akwai zarge-zarge da yawa waɗanda suna da hujjoji da ke cewa kusan gwamnoni sun mallake komai a siyasar, "inda suke yanke manyan matakan dimokuraɗiyya.

Musamman ma waɗan da za su riƙe muƙami a jam’iyya da gwamnati da sauransu."

Sai dai masanin siyasar ya ce ba haka ake yi a ƙasashen da suka ka cigaba ba, inda ya ce ko a Najeriyar ma, daga jamhuriya ta huɗu ne, "saboda a baya jam'iyya ta fi ƙarfin gwamnonin. Amma yanzu an yi sake, jam'iyyun sun koma aljihun wasu."

Wasu lokuta da gwamnoni suka nuna ƙarfin iko

A zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, wasu gwamnoni biyar sun samu saɓani da shi, inda suke fice daga jam'iyyar.

Gwamnonin su ne Rabiu Kwankwaso na Kano, da Murtala Nyako na Adamawa, da Aliyu Wamako na Sokoto, da Rotimi Amaechi na Rivers, da Abdulfattah Ahmed na Kwara, inda suka fito ƙarara suka yi adawa da jam'iyyarsu ta PDP, inda a ƙarshe suka fice, suka koma APC, wanda hakan ya taimaka wajen kayar da Jonathan a shekarar.

Haka ma a zaɓen 2023, wasu gwamnonin biyar na PDP suka ware a ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike, wanda shi ma ya yi tasiri wajen rashin nasarar PDP.

Ko a yaƙin zaɓen 2023, ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar bai je kamfe Rivers ba, wanda hakan baya rasa nasaba da takun-saƙar da ke tsakaninsa da Wike a lokacin.

Haka kuma a baya an sha sanar da ƴancin ƙananan hukumomi, amma kuma gwamnonin jihohi suka riƙa fatali da matakin.

Sannan a jihohin, akwai zargin gwamnoni sukan sanya majalisun jihohin da ƙananan hukumomi a aljihunsu, ta yadda sai yadda suke so za a yi.

Wannan na ƙara fitowa fili duk da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta tabbatar da ƴancin ƙananan hukumomin, amma kawo yanzu kusan duk jihohin da aka yi zaɓen, jam’iyyar gwamnatin jihar ko kuma wadda gwamnan yake goya wa baya ne ke samun nasara.

A zahiri yake yadda gwamnoni suke da ƙarfi a jihohinsu, inda suke zama wuƙa da nama a siyasa da mulki, har suke zaɓen waɗanda suke so su zama ƴan takara tun daga matakin majalisar dattawa da ta tarayya da majalisar jiha da ƙananan hukumomi.

Wannan ya sa kusan duk ɗan takarar da yake da matsala da gwamna, ko dai ya canja jam’iyya, ko kuma a kayar da shi a takarar ta cikin gida, sannan masu neman takarar kuma suke kamun-ƙafa da gwamnonin.

Sannan idan za a je zaɓen fid-da-gwani na shugaban ƙasa, yawanci gwamnonin ne suke zuwa da masu kaɗa ƙuri'a wato dalaget na jihohinsu, sannan su ne suke jan akalar ƙuri’un jihar.

Wannan na zuwa ne saboda su ne suke zama jagororin jam’iyyunsu a jihohi.

Bayan haka, kuma a ƙungiyance, ɗan takarar shugaban ƙasa na buƙatar goyon bayan gwamnoni, ko kuma mafi yawansu domin samun tikitin takara.

Me ya kamata a yi?

A game da matakan da ya kamata a ɗauka domin gyara siyasar ƙasar, Farfesa Kari ya bayar da wasu shawarwari kamar haka:

  • A kafa jam’iyyu na haƙika
  • Jam’iyyun su fi ƙarfin duk wani ɗan jam’iyya
  • A fito da tsare-tsare da za a rage wa gwanoni ƙarfi

Masanin ya ce idan aka yi haka to akwai yiyuwar rage tasirin gwamnonin a siyasar ƙasar.