Martanin da Harry ya mayar wa Trump kan caccakar NATO

Yarima Harry na masarautar Birtaniya ya yi kira da a mutunta tare da fadin ainihin gaskiyar sadaukarwar da sojojin kungiyar tsaro ta NATO suka yi a lokacin fagen daga a Afghanistan.
Harry ya ce shi ma ya yi aiki a wancan lokaci, kuma har ma ya kulla abota da mutane da dama.
Sau biyu dai ana tura Yarima Harry cikin tawagar sojojin Birtaniya zuwa Afghanistan
Yarima Harry ya yi kalaman ne a yayin da yake jinjina ga sojojin kungiyar tsaro ta NATO, da aka kashe a fagen daga ciki har da sojin Birtaniya 475.
Yariman na mayar da martani ne kan takaddamar da kalaman shugaba Donald Trump na Amurka ta haddasa a hirarsa da kafar yada labarai ta Fox News a ranar Alhamis.
Mr Trump ya ce sam Amurka ba ta taba bukatar dakarun tsaro na NATO ba, amma da an yi magana sai su ce sun tura dakaru Afghanistan, sun kuma zauna a can na dan lokaci, ba ma a sahun gaba suke a fagen daga ba.
Trump ya ce ba shi da tabbacin ko sojojin kawancen za su taimaka wa Amurka idan bukatar hakan ta taso.
Kalaman Mr Trump, sun janyo allawadai daga kasashen turai, inda Firaministan Birtaniya Sir Kier Stammer, ya kira su da cin mutunci da tozarci.
Birtaniya da sauran kasashe sun bi Amurka zuwa Afghanistan bayan kawancen tsaro na NATO ya dauki mataki jim kadan bayan kai harin 11 ga watan Satumba a cibiyar kasuwancin Amurka da ma'aikatar tsaro ta Pentagon, harin da kungiyar al-Qaeda ta dauki alhakin kai wa karkashin jagorancin Osama Bin Laden.
Shugaba Trump dai ya ce babu wata rawar azo a gani da dakarun kawancen NATO suka yi da suka cancanci a yaba musu.
Yarima Harry ya ce a shekarar 2001 a karon farko a tarihi NATO ta dauki matakin tsayawa kafada da kafada da Amurka ta hanyar kutsawa Afghanistan, a kokarin tabbatar ta tsaron Turai baki daya, an kira aminai kuma sun amsa kira, in ji Harry.
Dubban rayuka sun sauya, iyaye sun binne 'ya'yansu maza da mata da suka mutu,'ya'ya sun zama marayu, iyalai sun shiga mawuyacin hali.
Don haka ya kamata a mutunta sadaukarwar da suka yi, lokaci ne na zama tsintsiya madaurinki daya da nuna halacci da diflomasiyya da zaman lafiya.











