'Abin da Trump ya aikata a Venezuela zai iya zama ɗanba ga wasu shugabannin duniya'

Shugaban Amurka Donald Trump

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Abin da Trump ya aikata a Venezuela zai iya janyo ruɗani na tsawon watanni a faɗin duniya
    • Marubuci, Jeremy Bowen
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, International editor
  • Lokacin karatu: Minti 6

Kama shugaban Venezuela Nicolás Maduro da Donald Trump ya yi a wani hari da ya kai ƙasar, ya ƙara nuna irin ƙarfin iko da shugaban na Amurka ke da shi tare da samun goyon bayan sojojin ƙasar.

Amurka ta tsare Maduro karkashin ikonsa kuma yanzu za ta kwace "ikon" Venezeula.

Shugaban Amurkar ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a wanda ke cike da ce-ce-ku-ce kan tsarin harkokin wajen Amurka a gidansa na Mar-a-Lago da ke jihar Florida. Ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da rike iko da Venezuela har "sai an kai lokacin aka tabbatar za a iya miƙa mulki cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba."

Sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio, ya ce ya tattauna da mataimakiyar shugabar Venezuela Delcy Rodriguez, wadda ta faɗa masa cewa, "za mu yi duk abin da kuke buƙata... A tunanina, ta nuna farin ciki, sai dai ba ta da wani zaɓi."

Sai dai Trump bai yi wani cikakken bayani ba. Ya ce "ba mu tsoron wani abu in ma har akwai shi".

Shin yana ganin zai iya mulkar Venezuela daga inda yake? Shin hakan na nufin cewa zai bi kalamansa ta hanyar amfani da ƙarfin soji, waɗanda ya yaba wa tare da Marco Rubio da kuma sakataren tsaron ƙasar Peter Hegseth a Mar-a-Lago, sannan ko hakan zai iya sauya Venezuela da kuma sanya shugabannin yankin Latin Amurka yin mubaya'a?

Kalamansa sun yi nuni da cewa hakan na iya faruwa.

Amma hakan ba zai kasance abu mai sauki ba.

Wata ƙungiyar taƙaita yaɗuwar rikice-rikice ta ƙasa da ƙasa ta yi gargaɗi a watan Oktoba cewa, faɗuwar gwamnatin Maduro za ta iya janyo tashin hankali da rashin zaman lafiya a Venezuela.

A wannan wata, jaridar New York Times ta ruwaito cewa jami'an diflomasiyya da na tsaro a farkon gwamnatin Trump sun bayyana irin abubuwan da za su faru idan aka tumɓuke gwamnatin Maduro. Sun ce za a iya samun tashin hankali ganin cewa ƙungiyoyi masu riƙe da makamai na neman samun iko.

Cirewa da kuma tsare Nicolas Maduro wani babban abu ne da ya ƙara nuna ƙarfin ikon sojojin Amurka.

Amurka ta jibge ɗaruruwan jiragen yaƙi kuma ta cimma burinta ba tare da rasa ran ko da ɗan Amurka ɗaya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Maduro ya yi watsi da buƙatun al'ummar Venezuela ta hanyar watsi da shan kaye a zaɓen ƙasar, ƴan Venezuela da dama za su yi maraba da abin da ya faru a yanzu.

Sai dai tasirin abin da Amurka ta aikata zai ci gaba da yin amo har gaba da iyaƙokin ƙasar.

Fuskokin mutane sun cika da farin ciki lokacin da Trump yake jawabi a Mar-a-Lago, yayin da suke murnar harin da ƙwararrun sojojin Amurka suka kai Venezuela.

Samamen sojojin yana a mataki na farko ne kaɗai.

Tarihin Amurka na samun damar sauya gwamnatoci ta ƙarfin tuwo a tsawon shekara 30 da suka wuce na cike da kura-kurai.

Rikicin siyasa da ke bin baya shi ne abin da ke janyo ruɗani a lamarin, ko dai a yi nasara ko kuma akasin haka.

Iraqi ta faɗa cikin matsala mafi muni bayan mamayar Amurka a shekara ta 2003. Ƙoƙarin sake gina Afghanistan da aka ɗauka na tsawon shekaru 20 da kuma aka kashe biliyoyin daloli, ya rushe cikin kwanaki kalilan bayan ficewar Amurka a shekara ta 2021.

Trump ya yi gargaɗin cewa kada wata ƙasa ta saka baki cikin harkokin Amurka.

A ɗaya gefe, ya gargaɗi shugaban Colombia, Gustavo Petro da ya yi a hankali.

Daga bisani ya faɗa wa gidan talabijin na Fox cewa "ya kamata a yi wani abu a Mexico".

Cuba ma na cikin jerin ƙasashen da Amurka ke saka wa ido.

Na kasance a Haiti a shekara ta 1994 lokacin da shugaba Bill Clinton ya aika sojoji 25,000 da kuma jirage masu saukar ungulu biyu domin sauya gwamnati. Sannan, gwamnatin ta Haiti ta ruguje ba tare da an yi ko da harbi ɗaya ba. Shekaru 30 bayan faruwar lamarin, ƴan Haiti sun shiga ruɗani da kuma halin rashin tabbas. A yanzu ƙungiyoyin ƴanbindiga ne suka mamaye ƙasar suna cin karensu babu babbaka.

Donald Trump ya bayyana cewa zai sake gina Venezuela, sai dai ba kan dimokraɗiyya ba. Ya yi watsi da batun cewa shugabar adawar ƙasar Maria Corina Machado, wadda ta lashe kyautar zaman lafiya ta nobel ta jagoranci ƙasar.

"Ina ganin akwai matukar wahala gareta ta iya zama shugabar ƙasar, ba ta da goyon bayan hakan... ba ta mutuncin yin haka."

Bai ambaci Edmundo Gonzalez ba, wanda ƴan ƙasar da dama suka yi imanin cewa shi ne ya lashe zaɓen ƙasar a 2024.

Maimakon haka, a yanzu Amurka na goyon bayan mataimakiyar Maduro, Delcy Rodriguez.

Yayin da ake hasashen cewa akwai wasu da suka bai wa Amurka bayanai har ta kai ga kama Maduro, gwamnatin da magajinsa Hugo Chavez ya kafa, na cike da haɗin kai.

Mamayar da Amurka ta kai Venezuela ya sake janyo hankali kan yadda Trump ke kallon duniya.

Bai ɓoye aniyarsa ta son mallakar albarkatun wasu ƙasashe ba.

Tuni ya fara ƙoƙarin samun riba daga albarkatun ƙasar Ukraine, inda shi kuma zai bai wa ƙasar tallafin soji.

Har ila yau, shugaban Amurkar bai ɓoye aniyarsa ta son iko da ɗimbin albarkatun Venezuela ba, kuma ya yi imanin cewa an cuci kamfanonin man Amurka lokacin da aka mayar da ɓangaren man ƙasar na ƙasa baki ɗaya.

"Za mu riƙa ɗiba ɗimbin albarkatu, kuma tarin albarkatun zai tafi ga al'ummar Venezuela da kuma mutanen da ke wajen ƙasar da suka saba zama a cikinta, kuma har ga jama'ar Amurka a matsayin alfanu gare su."

Harin da aka kai da kama Maduro, wani babban ci-baya ne ga batun hanyar da ta dace na tafiyar da harkokin duniya, kamar yadda yake a cikin dokokin ƙasa da ƙasa.

Batun ya wargaje tun kafin zuwan Donald Trump kan mulki, sai dai ya sha nuna cewa zai iya watsi da duk wata doka da ba ya so a cikin Amurka da kuma matakin ƙasa da ƙasa.

Ƙawayensa na Turai waɗanda ba sa son ganin ɓacin ransa, ciki har da Firaminista Keir Starmer, suna neman hanyoyi na cewa suna goyon bayan dokokin ƙasa da ƙasa ba tare da sun yi Alla-wadai da batun kama Maduro ba da kuma cewa hakan ya saɓa wa dokar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Kare matakin sojojinta da Amurka ta yi kan kama mai safarar ƙwayoyi da ake nema ruwa a-jallo a matsayin shugaban Venezuela ya janyo ruɗani, musamman ganin cewa Trump ya ce ƙasar za ta yi iko da Venezuela da kuma ɓangaren man ƙasar.

Maduro ya gana da jami'an diflomasiyyar China a fadarsa a Caracas, sa'o'i kaɗan kafin kama shi.

China ta yi Alla-wadai da matakin Amurka. Inda ta ce "Mamayar Amurka ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa da kuma ƴancin Venezuela kuma yana barazana ga zaman lafiya da tsaron Latin Amurka da yankin Caribbean".

Amurka ta daina "saɓa wa ƴancin ƙasashe da kuma tsaronsu".

Duk da haka, China za ta iya ganin hakan a matsayin wata dama.

Tana ɗaukar Taiwan a matsayin wani yankinta kuma ta ayyana cewa komawa iko da ƴankin shi ne abin da ta saka a gaba.

Wannan ita ce fargabar da mataimakin shugaban kwamitin tattara bayanan sirri na majalisar dokokin Amurka, Sanata Mark Warner ya nuna. Ya fitar da sanarwar da ke cewa shugabannin China da kuma saura na sa ido cikin tsanaki kan abin da Trump ya aikata.

"Idan Amurka ta fara amfani da ƙarfin soji wajen afka wa ƙasashe da kama shugabanninsu da take zargi da aikata laifuka, me zai hana China nuna irin wannan ƙarfi kan Taiwan? Me zai hana (Shugaban Rasha) Vladimir Putin yin irin haka wajen garkuwa da shugaban Ukraine? Idan aka shata wannan layi, dokoki da suka hana tashin hankali a duniya za su fara rugujewa, kuma shugabanni masu mulkin kama karya su ne na farko wajen fara amfani da damar."

Donald Trump na ganin cewa shi yake tsara dokoki, kuma abin da yake aiki a Amurka karkashin ikonsa ba ya nufin cewa wasu ƙasashe za su ga irin haka.

Sai dai ba haka ƙarfin mulki ke aiki ba.

Take-takensa a farkon shekara ta 2026 na nuni kan wani sabon ruɗani na tsawon watanni 12 da duniya za ta fuskanta.