Abin da Trump ya ce zai yi wa Iran idan ta ƙara kashe masu zanga-zanga

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump
Lokacin karatu: Minti 2

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi Iran da cewa za ta dandana kudarta da gasken-gaske idan aka kara kashe masu zanga-zanga.

Wakiliyar BBC ta ce yayin da Amurka ta dauki mataki a kan Venezuela, haka kuma ta ce tana mayar da hankali kan Tehran, to amma babu wata alama karara.

Trump ya yi barazanar ne yayin da ake ta zanga-zangar tsadar rayuwa a Iran din sama da mako daya.

Da farko dai gwamnatin Iran din ta ce za ta fara bai wa 'yan kasar wani sabon alawus na wata-wata, na kusan dala bakwai, yayin da take neman yayyafa wa wutar mummunar tarzomar da matsalar durkushewar tattalin arziki ta haifar, ruwa.

An kashe akalla mutum 16 tun bayan da zanga-zangar ta barke a kasar ta Iran.

An shiga mako na biyu na zanga-zangar nuna rashin amincewa da tsadar rayuwa sakamakon yajin aikin da masu shaguna suka yi kan faduwar darajar kudin kasar wato Riyal, lamarin da ya sa yan kasar da dama ke kiraye-kirayen neman sauyi a siyasance.

Yayin da aka shiga kwana na tara da barkewar tarzomar, an bayar da rahoton cewa an yi zanga-zanga a mafi yawan larduna 31 na Iran din galibi a kananan garuruwa da kuma yankunan da ba su da ababen more rayuwa.

Duk da cewa kawo yanzu zanga zangar ba ta yi girman wadanda aka yi a baya ba amma kuma ta kasance mafi muhimanci a cikin shekaru uku.

Haka kuma ana ci gaba da fito-na-fito tsakanin jami'an tsaron kasar da kuma masu zanga-zangar

Sannan kuma ana ganin abu ne mai wuya sabon alawus na samar da dala 7 a kowane wata ga 'yan kasar domin rage radadin tsadar rayuwa ya yi tasiri wajen shawo kan fushin jama'a.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Shugaba Trump ya yi gargadin yiwuwar kai hare-hare na soji idan Iran ta ci gaba da kai hari tare da kashe masu zanga-zangar.

Matakin da Amurka ta dauka kan Venezuela na jan hankalin mutane a birnin Tehran - amma har yanzu babu wata bayyananniyar hanyar fita daga wannan rikicin da ke ci gaba da tabarbarewa a titunan kasar da kuma karuwar barazanar wani rikici tsakanin Iran din da Amurka da Isra'ila.