Shin Saudiyya ta fara sassauta ra'ayinta ne kan Iran?

Kafofin watsa labaran Saudiyya na kallon ziyarar ministan tsaron ƙasar zuwa Iran a matsayin sabon babin ƙulla alaƙa

Asalin hoton, IRANIAN SUPREME LEADER OFFICE HANDOUT/EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Kafofin watsa labaran Saudiyya na kallon ziyarar ministan tsaron ƙasar zuwa Iran a matsayin sabon babin gyara alaƙa
    • Marubuci, BBC Monitoring
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kafofin watsa labarai na Saudiyya, waɗanda ake ganin suna aiki ne a ƙarƙashin dokoki masu tsauri na gwamnatin ƙasar sun fara sauya yadda suke rahotanni kan alaƙar ƙasar da Iran.

Nazarin rahotanni da jawabai da sharhi da maƙaloli na jaridu da gidajen talabijin kan alaƙar Saudiyya da Iran cikin kimanin wata 10 da suka gabata sun fara sauyawa daga abin da aka saba gani a shekarun baya, inda aka saba ganin rashin jituwa da rashin alaƙa mai kyau.

A baya kafofin sun fi mayar da hankali ne kan sukar matakan Iran, musamman a ɓangaren tsaro, da kuma goyon bayanta ga ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

Alaƙar ƙasashen biyu a baya

A shekarun da suka wuce, Saudiyya da Iran sun kasance masu adawa da juna da kuma yin gasa domin neman zama ja-gaba tsakanin ƙasashen yankin, lamarin da ya sa suka riƙa amfani da ƙasashen da suke da iko da su wajen faɗa da rikici ta bayan fage, kamar yadda aka gani a Syria da Lebanon da Yemen.

A watan Maris na 2023, ƙasashen biyu sun sa hannu kan yarjejeniyar sulhu, inda ƙasar China ta shiga tsakani domin rage matsalolin da ke tsakaninsu.

Amma duk da wannan yarjejeniyar, saɓanin da ke tsakanin ƙasashen biyu ya ci gaba da fitowa fili.

Kafofin sadarwa a Saudiyya suna ganin rawar da Iran ke takawa wajen ɗaukar nauyin ƙungiyoyi irin su Hezbollah a Lebanon da Houthi a Yemen da Hamas ya saɓa da muradun Saudiyya na rage rikice-rikice a yankin.

Saudiyya na ganin zaman lafiya a yankin ne zai taimaka mata wajen ciyar da tattalin arzikinta da ma cimma muradunta na Vision 2030.

Amma yadda Isra'ila ta ɗaiɗaita Hamas da Hezbollah da ma kifar da gwamnatin Bashar al-Assad sun taimaka wajen rage ƙarfin ikon Iran.

Samun sauyi

Bayan harin Isra'ila a Doha ne kafofin sadarwa na Saudiyya suka fara kawo rahotanni kan buƙatar ƙasashen yankin irin su Turkiyya da Saudiyya da Iran su haɗa kai

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Bayan harin Isra'ila a Doha ne kafofin sadarwa na Saudiyya suka fara kawo rahotanni kan buƙatar da ke akwai ta manyan ƙasashen yankin irin su Turkiyya da Saudiyya da Iran su haɗa kai

Haɗin kai

Ziyarar ministan tsaron Saudiyya Khalid bin Salman Al Saud zuwa Tehran a watan Afrilu ya ja hankali matuƙa, wanda ke nuna alamar girmama juna.

Hani Wafa, babban editan jaridar Riyadh ya ce ziyarar na da matuƙar muhimmanci, inda ya rubuta cewa, "Saudiyya da Iran ƙasashe biyu ne masu girma da daraja a wannan yankin, kuma za su ƙarfafa juna idan suka haɗa kai. Amma babbar nasarar ita ce samun zaman lafiya da kuma ɗora ɗambar ciyar da yankin gaba."

Shi ma ɗanjarida a Saudiyya, Jasser al-Jasser ya yi nasa jawabin a tashar talabijin ta Al-Sharq News TV, inda ya ce an fara samun sauyi a alaƙa da ke tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya ce ya zo ne bayan abubuwan da suka faru a Lebanon da Syria da Yemen.

Ya ƙara da cewa yunƙurin Iran na inganta tattalin arzikinta da gyara alaƙarta da ƙasashen Larabawa na buƙatar taimakon Saudiyya.

Yaƙin Iran da Isra'ila

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kafofin sadarwa a Saudiyya sun bayyana yadda ƙasar ta dage wajen bayyana matsayarta a kan yaƙin Iran da Isra'ila.

Da Isra'ila ta kai hari a Iran, Saudiyya ta yi Allah-wadai, amma bayan wasu kwanaki sai Riyadh ta sake yin Allah-wadai da martanin Iran a sansanin sojin Amurka na Udeid da ke Qatar.

Jaridar Al Arabiya ta ruwaito a ranar 14 ga watan Yuni cewa Yarima Mohammed bin Salman ya bayyana a wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Iran cewa, "hare-haren Isra'ila sun kawo tsaiko kan yunƙurin tabbatar da zaman lafiya."

A ranar 23 ga watan Yunin, kafofin yada labarai a Saudiyya, ciki har da Al Arabiyya sun ruwaito tsakuren jawabin ministan harkokin wajen ƙasar cewa, "Saudiyya na Allah-wadai da harin Iran a Qatar."

A ranar 24 ga watan Yuni, mai sharhi a jaridu a ƙasar Mishary al-Zaidi ya ce "jawabin ma'aikatar harkokin wajen Saudiyya na nuna cewa mutanen yankin Larabawa ba su da wata buƙata a yaƙin da ke faruwa tsakanin Iran da Isra'ila da Amurka face nemo hanyoyin kashe wutar rikicin da neman zaman lafiya a yankinsu."

Kafofin watsa labaran Saudiyya na ganin rawar da Iran ke takawa wajen taimakon ƙungiyoyi masu amfani da bindiga irin su Hezbollah a Lebanon da Houthis a Yemen, da Hamas ya saɓa da muradun ƙasar na rage rikice-rikice a yankin

Asalin hoton, ABEDIN TAHERKENAREH/EPA/Shutterstock

Bayanan hoto, Kafofin watsa labaran Saudiyya na ganin rawar da Iran ke takawa wajen taimakon ƙungiyoyi masu amfani da bindiga irin su Hezbollah a Lebanon da Houthi a Yemen, da Hamas ya saɓa da muradun ƙasar na rage rikice-rikice a yankin

Saƙonni bayan harin Doha

Harin Isra'ila a Doha a ranar 9 ga watan Satumba ya zo da ba-zata a yankin, sannan ya ƙara ɗaga hankalin Saudiyya, wadda take ganin za a mayar da hannun agogo baya kan yunƙurin samar da zaman lafiya a yankin.

A daidai lokacin da abubuwa suka fara jan hankali, sai Saudiyya ta sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro da Pakistan a ranar 17 ga watan Satumba duk da cewa kwana ɗaya kafin shiga yarjejeniyar, sakataren majalisar ƙoli ta tsaron Iran, Ali Larijani ya ziyarci ƙasar.

Bayan ziyarar ne kafofin watsa labaran Saudiyya suka riƙa yin rahotanni kan buƙatar gyara alaƙa tsakanin Riyadh da Tehran, musamman a ɓangaren tsaro.

Masoud Al-Fak mai sharhi ne game da harkokin Iran a jaridar Al-Arabiya ya bayyana a game da ziyarar Larijani zuwa Riyadh cewa "wakilan Iran da suka ziyarci Saudiyya na ganin Riyadh a matsayin ƙasa mai muhimmanci ta kowane ɓangare."

Jaridar Asharq Al-Awsat ta ruwaito cewa ziyarar na da alaƙa "da ƙarfafa alaƙar tsaro da tattalin arziki da alaƙar siyasa a tsakanin ƙasashen biyu."

Ita ma jaridar Arab Independent ta nanata buƙatar da ke akwai ta gyara alaƙa tsakanin manyan ƙasashen yankin, musamman Turkiyya da Saudiyya da Iran bayan harin Doha.

Shi ma Abdulaziz bin Saqr, shugaban cibiyar bincike na Persian Gulf Research Center ya ce akwai fahimtar juna a tsakanin shugabannin ƙasashen biyu kan barazanar da yankin ke fuskanta.

Abin da ya faru a Gaza

An ga canji a rahotannin da kafofin sadarwa na Saudiyya suka yi game da harin Hamas a Isra'ila na ranar 7 ga watan Oktoba bayan cika shekara biyu da harin.

Jaridar Asharq Al-Awsat ta wallafa labarai da suka soki dukkan ɓangarori, ciki har da Iran ɗin da ƙungiyoyin da take ɗaukar nauyi.

Fitaccen ɗanjarida a Saudiyya Tariq Al-Hamid ya yi rubuta a ranar 8 ga watan Oktoba, inda ya bayyana harin na Hamas da "harin da ya ci mutanensa."

Da yake jawabi kan shekara biyu na harin ya rubuta cewa harin ya canja yanayin abubuwan da ke faruwa a yankin baki ɗaya.