Sabbin dabarun tsaron Trump da tasirinsu kan ƙasashen ƙetare

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
- Marubuci, James Lewis
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News World Service
- Lokacin karatu: Minti 4
Dabarar tsaron ƙasa ta gwamnatin Trump ta haifar da fargaba a tsakanin manyan ƙawayen Amurka da ke nuna suayin akala daga ƙa'idojin da suka kafa manufofin harkokin wajen Amurka tsawon shekaru da dama.
Takardar mai shafuka 33, wacce gwamnatin Amurka ta gabatar a makon da ya gabata, ta gabatar da duniya a matsayin wani fage na tattalin arziki, wanda ya daukaka yarjejeniyoyin da ke tsakanin ƙasashe biyu kan kishin ƙasa a fannin tattalin arziki sama da ɓangarori daban-daban da kuma inganta dimokraɗiyya.
Yana nuni da yawan "aƙidun na gwamnatin Trump'', wakilin BBC na Ma'aikatar Harkokin Wajen Tom Bateman ya shaidawa wa 'The Global Story podcast'.
Haka kuma abin mamaki shi ne abin da takardar ba ta ambata, inda ba ta yi wata suka kan manyan abokan adawar Amurka irin su Rasha ko China ba.
Madadin haka, ta tanadi wasu kalamai masu tsauri kan Turai, wanda ya haifar da damuwa a manyan biranen Turai a wannan makon.
'Bacewar yanayin rayuwa'
Yayin da dabarun tsaron ƙasa na baya sun kasance suna tabbatar da haɗin kan Amurka da ƙasashen Turai, wannan takarda ta ɗauki wani salo na dabam.
''Ba za a iya gane Turai nan da shekara 20 ko ƙasa da haka ba'', in ji shi, saboda yadda nahiyar ta rungumi wasu maniufofin shige da fice, waɗanda ke yin mummunar tasiri a kan "al'adun Yammacin Turai."
A wani sashe, dabarar ta bayyana a fili cewa Turai na fuskantar "ɓacewar yanayin rayuwa".
Jagororin Turai, aƙalla a bayan fage, sun shiga ruɗani kan wannan takarda, in ji wakilin Ma'aikatar Harkokin Wajenmu.
"Ba su yi mamakin cewa wannan shi ne matsayin aƙidar sassan gwamnati ba - amma ganin an bayyana shi a cikin takardar manufofin hukuma abin damuwa ne a gare su," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
An shafe watanni ana fuskantar taɓarɓarewar dangantaka tsakanin Amurka da Turai.
Ɗaya daga cikin alamun farko na halin gwamnatin Trump game da Turai ya fito fili ne a cikin watan Fabrairu, lokacin da mataimakin shugaban ƙasa JD Vance ya gabatar da wani mummunan hari kan dimokraɗiyyar Turai, a taron tsaro na Munich, inda ya caccaki shugabanninsu ya na mai cewa sun yi watsi da buƙatun masu kaɗa ƙuri'a game da batun cirani ƙaura da ƴancin faɗar albarkacin baki.
Amma a aikace, wannan sabuwar dangantaka ta rashin kwanciyar hankali nuna kanta ne wani fage na daban - yaƙin Ukraine.
Da alama takardar ta nuna cewa Turai ta yi rashin fahimtar yanayin yadda siyasar duniya ta ke kuma dole ne Amurka ta faɗaɗa makamashin diflomasiyya don daidaita yankin.
Ana zargin ƙungiyar Tarayyar Turai da daƙile yunƙurin Amurka na kawo ƙarshen yaƙin Ukraine, kuma a cewar takardar, dole ne Amurka ta "sake tabbatar da daidaito a Rasha, wanda zai daidaita tattalin arzikin Turai".
Babban saƙon shi ne ya kamata Ukraine ta ci gaba da kasancewa ƙasa mai cin gashin kanta amma hakan na buƙatar ta amince da babban matsayin Rasha.
Wakilinmu ya ce Donald Trump ya fara "gajiya" da ƙasashen Turai da Ukraine. "A bayyane ya ke... matsin lamba yana kan Turawa don su amince da matsayin da ƴan Ukraine za su gani a matsayin miƙa wuya," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Rikicin Ukraine ya riga ya kunno kai a wasu lokuta masu muhimmanci, ciki har da ganawar Trump da Vance a ofishin shugaban Amurka a watan Fabrairu tare da Shugaba Volodymyr Zelensky, inda aka soki Zelensky aka kira "mara mutunci" kuma "mara godiya".
Shugabannin Turai a yanzu suna fuskantar gaskiyar cewa Amurka na iya matsawa a samu wani sakamako da ya fi kusanci da abubuwan da Moscow ke so fiye da na Kyiv.
Rasha ta yi maraba da dabarun tsaron ƙasar na Amurka, tana mai bayyana shi a matsayin "ya yi daidai" da muradun ta.
'Abin da Trump ya gabatar
Baya ga sukar da ya yi wa Turai, sabuwar dabarar ta dauƙaƙa nahiyar Amurka, wacce ake kira "Yammacin Duniya", a matsayin babban abin da Amurka ta fi mayar da hankali a kai a cikin manufofinta na ƙasashen ƙetare.
Gwamnatin tana son ''ta tabbatar da cewa yankin ya kasance mai kwanciyar hankali wanda ya ke cikin kyakkyawan tsari don daƙile kwararra ƴan cirani zuwa Amurka, in ji takardar.
Wakilinmu ya shaida bayyana cewa, gwamnatin Trump na ganin wannan mataki a matsayin hanyar da za a bi domin dakile tasirin jda china ke da shi a Yankin Latin Amurka, duk da cewa ba a ambaci sunan China kai tsaye a cikin takardar ba.
Kasar China ta ƙara ƙarfin tattalin arziki a yankin, a cewar Trump, duk da cewa iƙirarinsa na cewa ita ke gudanar da mashigin ruwan Panama ba gaskiya ba ne.

Asalin hoton, Reuters
Yunƙurin diflomasiyyar Amurka na baya-bayan nan a yankin ciki har da ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya kai a ƙasashen Latin Amurka a farkon wannan shekara, na nuni da aniyar Washington na sake tabbatar da tasrinta a fannin tattalin arziki a yankin.
A yayin da dabarun ba su dogara kan girman tawagar sojin wannan manufar ba, kai hare-hare ta sama da ake yi kan waɗanda ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a yankin Caribbean da kasancewar jiragen yaƙin Amurka da dama da kuma dubban jami'an soji a gabar tekun Venezuela na jaddada barazanar yin amfani da ƙarfin soji.
Tuni dai sabon tsarin tsaron na Amurka ya sake fasalin muhawara a birnin Washington da ma nahiyar Turai baki ɗaya.
Tasirinsa kan Ukraine, da dangantakar Amurka da Turai da kuma duniya baki ɗaya yana ci gaba da bayyana.
Amma takardar ta bayyana abu ɗaya a sarari: gwamnatin Trump na da niyyar sake sauya fifikon manufofin Amurka na ƙasashen ƙetare - kuma tana tsammanin ƙawayenta su amince da wannan sabuwar manufar.











