Manyan al'amuran siyasa da ake sa ran faruwarsu a Najeriya cikin 2026

wasu daga cikin jiga-jigan siyasar Najeriya

Asalin hoton, Social Media handles

Bayanan hoto, A shekarar 2026 ne siyasar Najeriya za ta ɗauki zafi kasancewar ita ce jajiberin shekarar babban zaɓen ƙasar
    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 5

Shekarar 2026 shekara ce da Najeriya za ta fuskanci manyan al'amura masu ɗaukar hankali.

Kama daga na siyasa da tattalin arziki, da sauran fannonin rayuwar ƴan ƙasar da dama.

A fagen siyasar ƙasar ana ra ran ganin abubuwa da dama kama daga kaɗa kugen babban zaɓen ƙasar na baɗi zuwa tsayar da ƴan takara da sauran abubuwa.

Dokta Yakubu Haruna Ja'e shugaban Malami a jami'ar jihar Kaduna ya ce gaba-ɗayan wannan shekara za ta karkata ne kan al'amuran siyasa a Najeriya, ''ta yadda in ba a yi hankali ba duka zaɓaɓɓu za su mayar da hankali kan yaƙin neman zaɓe maimakon aiki''.

Cikin wannan muƙala mun rairayo wasu daga cikin abubuwa na siyasa da ake sa ran faruwarsu a Najeriya cikin wannan sabuwar shekara ta 2026.

Ƙarin ƙarfin ADC

Wasu jiga-jigan ADC

Asalin hoton, X/Multiple

A shekarar da ta gabata ne manyan jiga-jigan siyasar Najeriya suka rungumi jam'iyyyar ADC a matsayin jam'iyyar da za su yi haɗaka da nufin ''kawar'' da jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

Sannu a hankali jam'iyyar ta riƙa samun ƙarfi tsakanin ƴan hamayyar ƙasar waɗanda suka riƙa taruwa a cikin jam'iyyar da manufa guda.

Kawo yanzu ƴansiyasar da suke cikin jam'iyyar sun hada da Atiku Abubakar da Peter Obi da Mallam Nasir El-Rufai da Rotimi Amaechi da David Mark da sauransu.

Dokta Yakubu Haruna Ja'e ya ce ana sa ran jam'iyyar za ta ƙara samun ƙarfi a wannan shekara ta 2026, musamman idan ta yi taka tsantsan wajen zaɓen mutanen da za su yi mata takara a 2027.

''Za ta samu ƙarin ƙarfi, musamman a yanzu da jam'iyya mai mulki ta yi cikar kwari, dole za a ɓata wa wasu, kuma idan aka ɓata musu ba inda za su tafi sai ADC'', in ji shi.

Sai dai masanin siyasar ya yi gargaɗin cewa matsawar jam'iyyar ba ta yi a hankali za ta iya fuskantar ricikin cikin gida saboda yadda za ta cika da manyan jiga-jigan siyasa.

Raba garin Abba da Kwankwaso

Abba da Kwankwaso

Asalin hoton, Abba Kabir/ Rabi'u Kwankwaso/Facebook

A ƙarshen shekarar da ta gabata ne aka fara samun alamun rabuwar gari tsakanin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ubangidansa a siyasa, Sanata Rabi'u Kwankwaso.

To sai dai da alama a farkon wannan shekarar batun zai tabbata, domin kuwa daga dukkan alamu akwai zato mai ƙarfi na cewa Abba Kabir Yusuf zai fice daga jam'iyyar NNPP zuwa APC.

Jihar Kano ce dai kaɗai inda NNPP ke mulki a Najeriya, don haka wasu ke ganin ficewar Abba tamkar ruguza jam'iyyar ne.

Sai a gefe guda wasu na ganin Kwankwaso a matsayin ''kai kaɗai gayya'', kasancewar shi ya kafa jam'iyyar har ta kai ga samun nasara a Kano.

Sai dai Dokta Ja'e na ganin cewa komawar Abba APC wata sabuwar dambarwar ce APCn kasancewar akwai manyan gwasake a cikinta a Kano.

Zaɓukan fitar da gwani

A wannan shekara ta 2026 ne kuma jam'iyyun siyasar Najeriya za su fitar da gwanayensu a manyan zaɓukan ƙasar na 2027.

Daga watanni shidan ƙarshen shekarar jam'iyyun siyasar ƙasar za su karkata kan yaƙin neman zaɓe da zaƙulo mutanen da za su tsaya musu takara a 2027, kamar yadda Dokta Yakubu Ja'e ya bayyana.

Dokta Yakubu Ja'e ya ce zaɓukan fitar da gwani a wannan karo kasuwanci za a buga.

Masanin siyasar ya ce wasu ƴansiyasar za su yi amfani da kuɗi domin cimma muradunsu na samun takara a zaɓukan ƙasar da ke tafe a shekarar 2027.

''Dama an saba ganin ƴansiyasa na amfani da kudi wajen sayen wakilan da ke zaɓen fitar da gwani, to hakan za ta faru a wannan shekara ma, saboda yawaitar ƴansiyasar da ke neman tsayawa takara'', in ji shi.

'Fashewar APC'

Shugaba Tinubu

Asalin hoton, Bayo Onanuga

Dokta Yakubu Haruna Ja'e ya ce akwai yiwuwar jam'iyyar APC mai mulku za ta fashe a wannan shekara ta 2026.

''APC ta haɗiyi abubuwa masu yawa, kuma da wuya su iya narkewa a cikinta, don haka akwai yiwuwar cikin jam'iyyar zai fashe ta yadda wasu daga cikin ƴaƴanta za ta koma wata jam'iyyar'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa akwai mutane da dama da ke cikin jam'iyyar da ma wadanda daga baya suka koma cikinta domin fatan cikar muradunsu.

''To idan suka fuskanci cewa muradun nasu ba za su cika a jam'iyyar ba, ko aka ɓata musu za su fita daga ciki, su koma wata jam'iyyar'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Haka kuma ya ci gaba da cewa ko da wasu da aka ɓata wa sun ƙi fita a jam'iyyar, to za su riƙa yi mata zagon-ƙasa.

Ina makomar Kashim Shettima?

Kashim Shettima

Asalin hoton, Kashim Shettima/X

Bayanan hoto, Wasu ƴan hamayya sun jima suna kiraye-kirayen ajiye Kashim a 2027

Wani abu da zai ƙara ɗaukar hankali a siyasar Najeriya a 2026 shi ne batun ci gaba ko ajiye Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban ƙasa.

Ƴan'adawa da dama musamman Kiristoci sun jima suna sukar gwamnatin Tinubu da ɗaukar Musulmai matsayin shugaban ƙasa da mataimaki.

Don haka a wannan karon ma za su yunƙuro da wannan suka tasu, lamarin da zai sa Tinubun da APC sauya tunani.

Sai dai Dokta Ja'e na ganin cewa Shettima ya zamar wa Tinubu da APC ƙarfen ƙafa ne, domin kuwa ajiye tamkar ajiye arewa ne gaba ɗaya, wani abu da ya ce APC ba za ta yi ba.

''A gefe guda kuma sake tafiya da shi a matsayin mataimaki ba zai yi wa wasu Kiristoci ɗaɗi ba, don haka za su iya yi wa jam'iyyar zagon ƙasa'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

'Ungulu da kan zaɓo'

Dokta Yakubu Ja'e ya ce wani abu da ake hasashen zai faru a siyasar ƙasar a 2026 shi ne ungulu da kan zabo.

Masanin siyasar ya ce akwai gwamnoni da dama da za su nuna suna tare da APC a sama domin makomarsu ko ba su takara, amma kuma ba za su iya tallata shugaban ƙasa ko kawo masa ƙuri'un jiharsu ba.

''Za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun yi nasara su da masu riƙe da muƙamai na jihohinsu kama daga ƴan majalisar jihohi da na tarayya da sanatoci, amma kuma da wahala su iya kawo wa shugaban ƙasa ƙuri'in jihohin nasu'', in ji Dokta Ja'e.

Makomar PDP da LP

Dakta Yakubu Ja'e ya ce da alama jam'iyyun PDP ta LP sun tasamma mutuwa a fagen siyasar Najeriya.

A lokacin da aka yi zaɓen 2023 jam'iyyar PDP ta samu gwamnoni 12 cikin jihohin ƙasar 36, sai dai kawo yanzu huɗu ne kawai suka rage mata, yayain da duka sauran suka fice tare da komawa APC in ban da guda ɗaya da ya koma AP.

Baya ga gwamnoni, jam'iyyar PDP da LP mai gwamna ɗaya na da ƴan majalisar tarayya ta sanatoci masu yawa, amma da dama daga cikinsu a 2025 sun fice daga jam'iyyar.

Dokta Ja'e ya ce jam'iyyun ba za su yi wani tasiri a siyasar tarayya ba, sai dai a ɗaiɗaikun jihohin da suke da iko.

''Don haka su ma za su shige babbar jam'iyyar adawa da ADC ne in dai da gaske suke adawar tasu, ko su shiga APC idan ta yi musu tayi'', in ji shi.