Mece ce gaskiyar dalilan Abba Kabir na komawa APC?

Abba Kabir.

Asalin hoton, Abba Kabir/X

Lokacin karatu: Minti 3

Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya koma jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, amma da yawan mutane na ta tambayar, shin mene ne haƙiƙanin dalilinsa na barin tafiyar Kwankwasiyya?

Raba gari da Kwankwaso da Abba ya yi ya bai wa mutane da dama mamaki, kasancewar yana cikin wadanda ake yi wa kallon ‘yan amanar tafiyar Kwankwasiyya.

Kafin ranar Alhamis 22 ga watan nan, wasu jami'an gwamnatin Kano a wani ƙoƙarin ƙarshe na ganin an ci gaba da tafiya a dunƙule, sun yi ta yunƙurin ganin Kwankwaso ya shiga tafiyar ta komawa APC, sai dai da alama roƙon bai karɓu ba.

Sanarwar Abba Kabir Yusuf ta ce gwamnan ya bar inuwar Kwankwaso ne saboda rikicin cikin gida da ya yi wa NNPP katutu da kuma muradin ci gaban Kano.

Sai dai Jam'iyyar Kwankwaso ta ce abin da aka yi cin amana ne kawai da neman sauƙi ko ta halin ƙaƙa.

Abin da ya faru, in ji ta, ya yi kama da na siyasar Kano a jamhuriya ta biyu, lokacin da Gwamna Rimi ya raba gari da Mallam Aminu Kano.

Sai dai wasu sun ce an ga irin wannan a lokacin da Kwankwaso ya raba gari da su Rimi bayan zaɓen 1999.

Wani ƙaulin kuma na cewa kaɗa hantar da 'yan APC suka riƙa yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf cewa za su ƙwace Kano a 2027, mai yiwuwa ya yi tasiri.

Duk da ƙarfin APC a sama, shi ne ya kayar da ita daga mulkin Kano da rinjayen ƙuri'u dubun dubata, kuma Kotun Ƙoli ta tabbatar masa da nasarar.

Akwai kuma ƙaulin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da sauran hanyoyin kwaɗaitarwa.

'Yan adawa sun daɗe suna zargin jam'iyyar APC da amfani da "karnukan farauta" wajen razana abokan adawa ta hanyar bankaɗo badaƙalar kuɗi a ce za a yi musu tonon silili da kai su kotu matuƙar ba su koma ba.

APC ta sha musanta zargin amma ci gaba da sauyin sheƙar da musamman gwamnoni da 'yan majalisun dokoki na adawa ke yi zuwa cikinta ya sa za a daɗe kafin ta iya gamsar da 'yan Najeriya.

Sai dai, mece ce gaskiyar dalilan da suka sa Abba Kabir barin NNPP tare da komawa APC?

Ɓaraka a shugabanci jam'iyya

Alamar jam'iyyar NNPP

Asalin hoton, NNPP/X

Kabiru Sufi, malami a kwalejin ilimin share fagen shiga jami'a da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, ya ce akwai manyan dalilai guda uku da suka sa gwamnan ya sauya sheƙa.

"Ɓaraka a matakin shugabancin jam'iyyar na ƙasa na cikin dalilan. Wannan ya sa kowane ɓangare na iƙirarin su ne masu iko har ma ta kai jam'iyyar na da alamomi biyu, alamar kayan marmari da kuma littafi," in ji Kabiru Sufi.

Ya ce matakin ya kai jam'iyyar zuwa kotu inda aka yi ta ɗaukaka ƙara.

"Wannan ne ya sa ake ganin cewa idan aka ci gaba a haka za a iya shiga takara sannan ba a san me kotu za ta yanke ba. Kar a zo a shiga zaɓe rikici ya sa a karɓe zaɓen idan jam'iyya ta samu kamar yadda ya taɓa faruwa a jihar Zamfara," in ji Sufi.

Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da gwamnan da muƙarrabansa suka bayar na ficewa daga NNPP.

Shiga jam'iyyar da ke mulki a tarayya

Wani dalili da masanin ya ce ya sanya gwamnan ficewa daga NNPP shi ne, komawa jam'iyyar da ke mulki a ƙasa na da alfanun gaske.

"Idan suna jam'iyyar da ke juya gwamnati a matakin taraya za a samu alfanu daban-daban kamar daidaiton ayyuka saboda manufa ɗaya, da morar ƙarin yawaitar ayyuka da suke ganin ba sa samu," in ji shi.

Ya kuma ce suna ganin wannan na daga cikin ribar da za su samu da komawarsu zuwa APC.

Rage zafin adawa

Masanin ya ƙara da cewa wani ƙarin dalili na barin jam'iyyar NNPP da gwamna Abba Kabir ya yi shi ne son rage adawa a jihar tsakanin jam'iyya mai mulki da wadda ke mulkin tarayya.

"Suna ganin matakin zai rage zafin adawa da ɗumamar siyasa da ake da shi a jihar," in ji Kabiru Sufi.

Ya ce gwamnan da muƙarrabansa na ganin cewa akwai masalaha a sauya sheƙar da suka yi.

Rashin daidaito a ɓangarorin jam'iyyar biyu

Dakta Kabiru Sufi ya ƙara da cewa masu hasashe na ganin rashin daidaito a tsakanin wasu ɓangarori biyu; matakin jam'iyyar a jihar da kuma kanta a matsayin tafi ɗaya na cikin dalilan gwamnan na ficewa.

"Wasu za su yi tunanin cewa idan zaɓen fidda gwani ya zo za a iya samun sauyi watakila. Suna ganin kamar dangantaka na yin tsami duk da cewa abu ne da bai fito fili ba, wasu na ganin gudun kada wani abu yaje ya dawo gwamna ya rasa takara zai iya zama dalilin ficewa daga NNPP," in ji dakta Sufi.

Ya ƙara da cewa watakila kasancewar tsamin dangantaka na wasu ɓangarorin tafiyar Kwankwasiyya da ya sa babu wanda ya san wanda zai yi takara ko da wanda yake kai, ya ƙara ƙarfafawa gwamnan da muƙarrabansa neman mafita a wata jam'iyya.