'Abubuwan da ya kamata majalisa ta mayar da hankali bayan komawa hutu'

Asalin hoton, NATIONAL ASSEMBLY
A ranar Talata 27 ga watan Janairu majalisun dokokin Najeriya za su koma bakin aiki bayan dogo hutu na Kirsimeti da sabuwar shekara.
Akwai wasu kudirori da ke gaban majalisar kafin tafiya hutu da ke da muhimmanci ga dimokuradiyya da tsaro da kuma tattalin arziki.
Cibiyar Rajin Kyautata Ayyukan Majalisun Dokoki da Yaƙi da Rashawa a kasar ta CISLAC ta nemi da su mayar da hankali kan gyara dokar zabe da matsalar tsaro.
Kungiyar ta ce ganin an shiga sabuwar shekara ta 2026, ya sa ta yi wannan Kiran don kada hankalin yanmajalisar ya koma kan siyasa su bar batutuwan da ke da muhimmanci wajen ci gaban al' umma.
Awwal Musa Rafsanjani, shugaban kungiyar ta CISLAC, ya shaida wa BBC cewa, kungiyarsu na kira ga majalisun da su fifita aikace-aikacen majalisa maimakon mayar da hankali a kan abubuwan da suka shafi siyasa.
"Ya kamata Majalisun su mayar da hankali wajen ayyukan da za su kawo ci gaba a kasa da kuma dokokin da ya kamata a ce an yi su ko an zartar da su a ba su fifiko."
"Yana da kyau kuma 'yanmajalisar su tabbatar da bayar da muhimmanci ga dokokin da ya kamata a ce an yi gyara a kansu," in ji Rafsanjani.
Ya kuma yi kira ga 'yanmajalisa da su ƙara jaddada wa 'yan Najeriya cewa za su tsaya tsayin daka domin yin abin da ya kai su majalisar, ba wai su tsaya a matsayin 'yan amshin Shata ba.
Kungiyar ta CISLAC, ta kuma ja hankalin 'yanmajalisar a kan su rika zama a majalisar domin yin abin da ya kai su ba wai a neme su a rasa ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shugaban CISLAC, ya ce, sun yi wannan kira ga majalisun ne bisa la'akari da yadda yanzu hankalin 'yanmajalisar ya koma kan siyasa tun kafin lokaci ma ya yi.
"Yanzu akwai 'yanmajalisar da yawa da hankalinsu ya koma kan batun sauya jam'iyya da kuma batun zaben 2027, shi ya sa muke rokonsu a kan su tabbatar da cewa sun yi aikin da ya kamata a ce sun yi," in ji shi.
Rafsanjani, ya ƙara da cewa akwai abubuwa da ya kamata majalisun su mayar da hankali a kansu kamar kashe-kashen da ya addabi al'ummar kasar saboda matsalar tsaro da ma sace-sacen jama'a da ake don neman kudin fansa, yana mai cewa "dole ne majalisa ta lalubo hanyoyin magance su."
Ya ce," Radadin talauci da rashin aikin yi da kuma tabarbarewar tattalin arziki, majalisa na da damar kawo tsare-tsaren da za su rage wanna radadi.
Ya kuma ce akwai buƙatar majalisar ta gyara a cikin tsarin zabe domin idan ba a yi gyara ba da yawan 'yan Najeriya ba za su yi imani da zaben ba. Sannan kuma akwai wadanda ma za su kauracewa zaben.
"Batun cin hanci da rashawa da ake wajen yin doka ko amincewa da doka, misali kamar dokar haraji, ya kamata majalisu dokokin su tashi tsaye su tabbatar da cewa ba a ci gaba da dakile aikace-aikacen da suke ba." in ji shi.











